IDAN KUNA KARUWA DA LABARINNAN AYI FOLLOWING DINA SANNAN AYI VOTING
Lud kuwa yana kaiwa nan ya kama hannunta suka shige daki ya rufe kofa harda lock KYAM! Cikin huci ya wullata kan gado ya bude fridge ya dauko Zuma ya zuba ruwa a Kofi yasa zuman cokali 2 ya garwaya ya shanye.
(Wannan hadin sunan shi honey water kuma yana rage karfin giya a jikin mutum sannan yakan hana yin ciwon kai da mashaya ke yi)
Zama yayi a bakin gadon yarufe ido. Bayan kamar minti uku ya bude ya taso ya cacimi wuyan Rigan marakisiyya ya dangana ta da gini yace ke Dan uw......ki shine daga fita na kika fita naki karuwancin ko?
Yar.....uba ba cewa nayi ki koma gida ba ? Falla Mata Mari yayi sanda jini ya tsiyayo ta gefen bakin ta.
Yace wow ya sake ta yana tafawa yace wato Dan kinga an mana aure shine kika rainani ko?Toh AI tunda abinda kike nema kenan kin zo gidan ta. Amma kinsan inda aka Sami matsala ? Kinyi min karama sosai rashin imani na bai kai na tabaki ba. Ke bama wannan bace matsalar, ke har maita ma kina da shi babu tsiyar da zanyi dake yana kaiwa nan ya rufe kofar ban daki Wanda sai luba ke ciki.
Wakar da ta kunna da karan ruwa ya hanata jin hayaniyar da yake yi. Shi kuwa bed ya dauka ya daure a window ya dauko hannunta yace toh maza kama wannan ki sauka ki tafi gida.
Girgiza kai ta soma tana fadin ya lud kar kamin haka Wanda baya ma fita me kyau. Janyota take tana cijewa shi a dole sai ta kama bed sheet din ta sauka Allah yaso suna hawan farko.
Ganin zata bata masa lokaci yasa ya bude drower dinsa ya dauko safe defense bindigar sa Wanda ya nemi license. Daga shi sai boxers yace kina da zabi uku.
Ko ki fita salin alin, ko ki hau gado na kashe ki ko kuma na miki kisa mai sauki da bindiga zabi daya kamin na irga biyar ko kuma na miki duka ukun.
Tsayawa yayi bata motsa ba yace daya, biyu,uku,hudu.... tasan yadda yasha giya ba abinda bazai yi ba dukda ya rage karfinta. AI yadda kasan yar China batasan sanda ta tsallake window ba.
Bubbuga kogan bandakin sai luba ta fara tana fadin baby kofar nan tayi jamin fa ko kai ka rufe? Ciro bed sheet din yayi ya wulla a gado ya bude kofa bandakin bayan ya rufe ragan net din.
Lekawa yayi Dan ya tabbatar ta tafi yaga ta zauna ta dukun kune a kasan saitin window dinsa. Tabe baki yayi yaje ya bude sailuban yace ta gyara gado bacci yake ji. A ranta race bakada kai naje nayi shaye shayen maganin Mata na kace min bacci kake ji?
Gyara gadon dai tayi kamar yadda yace ya kwanta yana miko Mata hannu alamun tazo jikinsa a ranta tace yauwa yanzu naji batu. Hawa gadon tayi ta kwanta a jikin sa tana tsammanin taji labari sai taji shiru.
Pecking bakinsu tayi tace wai me ya sameka ne? Ajiyan zuciya yayi ya matsa daga gefenta ya bata baya yace bazaki gane ba kiyi bacci.
Matsowa ta sake yi tace haba mine haba nifa na lura cikin kwana ukun nan gudu na kakeyi kasan fa kai ka janyo matsalar nan ya za'ayi......
hannu ya daga Mata yace kiyi bacci kawai babe. Tashi yayi ta zauna tace wallahi baka isa ba yo in ba abinda zakamin wa yace ka kawoni ka ajiye ka hanani kula kowa? Ko ance ma ni yar tsana ce da zaka saka a gaba kana kallo?
Shima tashi yayi ya zauna yace ki iya bakinki ki, dalewa cinyarsa tayi ita dole zata masa karfa karfa. Ya kankade ta ya janyo belt dinsa dake ajiye gaban madubi ya fara lafta Mata yana masifa.
Ni sa'anki ne? Nace ni sa'anki ne? Ina cewa ah ah kina dagewa shegiya yanzu ma AI bakiyi latti ba sai ki tashi kije ki kula duk uban da kikeso.
Zama yayi akan kujera ya Dade kai yana tuno bakin cikin daya gaji a idon umma sanda ta fita. Shi dama tun sanda aka daura masa aure jikin sa ma yayi sanyi.
YOU ARE READING
YA JI TA MATA
Mystery / ThrillerWannan labari me suna YA JI TA MATA shine littafina na uku.... Labarin wani saurayi ne Wanda bashida aiki sai zina, a cewar sa ba laifinsa bane Allah ne yayi sa hariji. Toh hakan ne yasa iyayen sa suka rufe ido sai yayi aure amma fa an gudu ba'a tsi...