CHAPTER 58

774 110 23
                                    

Abu daya da ya sani shine yana shan gaban motocin da ke gaban sa ne yadda ake shan gaban napep marasa yin sauri dukda ko babu Wanda yakai yan Abuja bawa titi wuta. KOMIN RINTSI SAI YA HANA M. AHMAD TAFIYA DOMIN SHI YA TAIMAKA MASA YA ZAMA MUTUM.

Jummalo kam mikewa tayi Dan bata da tsoron mota ta fara washe baki wani nishadi na sauka Mata a rai ganin yanda suke ta wuce motoci abin yana Mata sugar ta mirror m. Salis ya hango ta ya murmusa tare da dauke tunanin daga kansa ya mayar da hankalin sa ga tukin da yake yi.

Idan su air port m. Salis ya bude kofan bangare da jummalo take da sauri, da yaga ta tsaya kalle kalle zata bata masa lokaci kawai ya riko hannunta ya janyo ta da gudu suka tafi wajen clearance tun daga ne sa suka hango m. Ahmad na kokarin wucewa kamin su iso ya wuce.

Kokarin tare su security yayi Wanda m. Salis yasan za ayi haka Dan haka ya shirya kawai hankada jummalo yayi bayan ya ture security, suna gudu ana biyo su har security 6.

Jummalo sai lokacin ta hango m. Ahmad Dan haka cikin jin dadi ta bude murya tana danna masa Kira YA AHMAD! YA AHMAD! MUNZO MU TAFI DA KAI GIDA!
Bata ma San sanda ta cire hannun ta da ke cikin na m. Salis ta kara gudu ba.

M. Ahmad kuwa bayan anyi clearing dinsa ya wuce yana tunanin gara da ya tafi hakan shine zai gi zaman lafiya ma kowa, hara shi daya ya wahala saura su Sami natsuwa Dan yaga alamu zuciyar sa na kokarin kawo tashin hankali  a cikin gidan su ya raba sa da kanin sa.

Kamar daga sama ya jiyo muryanta tana danna masa Kira murmushi yayi Dan a tunanin sa kawai imagination ne.  Jin talun takalmin ta da kuma sautin takalma dayawa da alamu ana kokarin tsayar da wasu yasa ya tsaya cak.

Sautin ne ke kara matsowa kusa da shi Dan haka ya juyo domin ya tabbatar da abin da yake tunani AI kuwa itace dauke da wannan murmushin nata Wanda ke sa ta zama kamar wata shashasha tana ta dago musu hannu yayinda m. Salis ke tsaye yana kallon su wani security na masagana kuma bai ma San me yake cewa ba.

Sauran biyar din kuma suka ci gaba da bin jummalo Wanda ita ma bata San suna yi ba. Cire takalma tayi duk Dan ta kara sauri tana isowa gaban sa ya daka tsalle zata dale jikin sa tana me fadin ni da ya salis ne muka zo zamu tafi da kai.

Baya ya ja tare da yi Mata murmushn me boys damuwa yace bakyajin magana ko? Ba nace miki ki dena taba maza ba? Sosa kai tayi tace au mancewa nayi tsabar jin dadin ganin ka. Kasan wahalar neman ka da mukayi kuwa?

Tana mai nuna wa da hannu ta ce ga can ya salisu yana kiranka zo mu tafi gida. M. Ahmad yace ai ni bazan koma gida ba kasan zan bari karatu zanje nayi.

Ta dafe kirji tace barin kasar kuma? Yaya Ahmad me muka maka? M. Salis ne ya karaso inda suke ganin securities na kokarin su taba jummalo da ke ta yi wa m. Ahmad karadi.

Rike hannun security din yayi tare da bashi hakuri sannan yayi masa tuni cewa musulmai ba kowani namiji ke taba mace ba. Da yake security din mai fahimta ne yace ba damuwa amma sun karya doka su koma daga baya.

M. Salis yace ya basu minti biyu yanzu zasu fita hakan yasa security din ya sanar da sauran securities cewa su koma zai fito da su.

M. Salis bai ce wa m. Ahmad komai ba kawai ya fanki hannun sa ya fara Jan sa . Kafewa m. Ahamd din yayi yace brother ku koma gida kawai ba za  biku ba. M.salis bai kulasa ba yaci gaba da Jan sa. M. Ahamd yace ka dai na dagewa brother ka San bazan biku ba na Riga da na yanke shawara.

Ganin dai m. Salis yayi kunnan uwar shegu yasa yace brother ka San dai dalilin da yasa zan bar kasarnan in ina zaune son matar ka zai cigaba da nanaye min zuciya ne ni da kai mu dinga jiwa zuciyoyin hunan mu ciwo ka barni na tafi.

Ya karasa zancen yana fincike hannun sa. Cikin tsawa m. Salis yace IDAN KUMA NACE NA SAKETA FA? Shiru wajen yayi security dake kokarin ce musu minti biyun su ya cika shima tsayawa yayi da maganan sa makale a bakin sa.

Dai dai kun mutane da akayi clearing suma tsayawa kallon ikon Allah sukayi. Abun dai kamar a da wasa. Tsaki m. Ahmad yayi tare da juyawa zai koma m salis ya riko hannun sa yace brother wallahi Allah da gaske nake na saketa kuma ni kai nake so ka AURETA bayan ta kammala iddan ta.

M. Ahamd yace kai salis kana da hankali kuwa? Kai wai yaushe zaka girma ne ka dauka komai abin wasa ne? Kawai zaka saki matar ka kace na aura? Yaushe ma ka sanni? Daga wajen aiki muka hadu har muka kulla zumunci shine....

M salis ne ya datse ta hanyar cewa toh AI shine abin da nake fada mun kulla zumunci mun zama yan uwan juna mun zama daya. Matsowa tayi daf da fuskan m Ahmad din tare da rike wuyan track suit dinsa amma ba shake sa ba yace tun ranan da na fara aiki ka shiga raina.

Kai ka sani a da ba soyaiyar Dan uwa nake maka ba soyaiyar abokin rayuwa nake ma kuma ka fahimta shiyasa kaki la bari na shiga jikin ka ashe kaima kana dauke da lalura, daga baya da ka ga matsalar mu daya ce muka hada karfi da karfe muka samu lafiya a sanadin ka ne yau na zama mutum cikakke da zan bigi kirji nayi alfahari da badan haka ba da yanzu haka ina tare da wani katon banza muna....

Hannu m. Ahmad yasa ya rufe masa baki yayinda girard sa ta hade suna kallon juna ido cikin ido kowa ya kafe yana nuna taurin kansa. M. Ahamd yace na San da wannan salis, look brother na San son da kake min ka juya ka mayar da shi na yan uwan taka amma me mutane zasu ce dukda ni abinda zasu ce bai dame ni ba.

Haka zamu ci gaba da rayuwa kenan? Duk abin da kake sa shi idan ina so sai ka bani? Tunda ka iya bani Mata na San ba abinda bazaka bani ba, nagode da soyaiyar ka gareni amma inajin nauyin na karbi kyautar ka domin a kowani lokaci idan na kalle ta sai naga kamar banyi maka adalci ma.

Yana kaiwa nan ya dauke hannun sa daga.bakin m. Salis din ya juya domin ganin idanun dukan su biyu na kokarin bada maza. Ba jikin sa kadai ba har zuciyan sa sanda ya tsaya lokacin da yaji m. Salis ya rungume sa ta baya tare da fadin bro karka tafi ka barni.

Wallahi in ak tafi Jima barin garin zanyi domin ban San inda zan sa kaina ba. Ni duk in da kake nan nake son kasancewa, kwanaki kadan dinnan da na daina ganin ka baka ga yadda nake ji ba kawai jarumta nake yi Dan akr mama jikin ta yayi sanyi.

Wannan kalaman yasa m. Ahmad juyowa yana kallon m. Salis da ya makale shi. Tabbas ya Dan fada ba karya yayi ba. Ajiyan zuciya m. Ahmad ya sauke tare da share ma m. Salis hawaye yace shikenan toh Dan kani na  na yarda.

SHIN KUNA GANIN YA DACE DA M. AHAMD YA YARDA? SHIN DA GASKE YA YARDA KO DAI WAYO YAYI MA M. SALIS

DON'T FORGET TO FOLLOW ME, VOTE BY CLICKING THE STAR BELOW AND COMMENTING YOUR THOUGHTS !

Miss untichlobanty 💕

YA JI TA MATAWhere stories live. Discover now