CHAPTER 45 LOADING.....
Kowa da kowa zaune a parlour an hallara su miss untichlobanty glass dinnan kamar kar ta cire fans ma an baje sai hira ake yayinda ake ta taruwa.
Shigowan su mando yasa umaima lawan abba fadin Allah mai iko ga ido na ga na mando su mando an waye. Wani murmushi ya aiko Mata irin fresh guy dinnan kamin ya nufi sama.
Rashida Ismail ne tace kai kuma ina zuwa haka? Wasu daga cikin fan suka ce tambaya mana shi dai. Ba tare da ya juyo ba yace wajen lud zanje ko da magana ne?
Ganin hankali ma ba a kansa yake ba kallo ya koma kan jummalo yasa yayi hayewar sa sama. Aisha isma'il tace toh ke jummalo menene kike ta hade rai ko wani abin aka miki.
Jummalo tace yo menene ma ba'ajin ba? Ni daga shigowa na labari duk da matsala na shigo. Gani marainiya, ga no yar kauye, ga na rasa Bello na, ga nayi wani aure da ni kaina ban gane me ke wakana ba.
Sis beauty ne tace toh nide jummalo kar kiji haushi na amma wai menene muhimmancin ki a labarin nan? Tabe baki jummalo tayi tace in na fada miki zaki yarda?
Beauty tace sosai ma kuwa me zai hana zan yarda mana, gwaliyo jummalo ta Mata tace ta kurunkus untichlobanty zata zaku tambaya ba ni ba.
Kallon untichlobanty beauty tayi amma me a gaban enlargement suka kalle ta tana kalle kalle, kamin suyi wani zance m. Salis ya kutso kai. SISTER tace ga m. Salis yazo tsaya muna da tambayoyin da zamu yi maka fa.
Yace toh dama me ya kawo ni idan ba amsa tambayoyin ba? Sis hauwa jiya tace m. Salis ni wai lafiyar ka kalau ko kuwa? Yace eh toh zaki iya cewa lafiya nake amma ba lau ba.
Tace AI wannan ba amsa bace, yace saide kice baki fahimta ba. Maman sajida tace nifa m. Salis kaga ina yin m. Ahmad karfa kaje la sa ku shiga wani yanayi ka cutar mana da shi.
Ajiyan zuciya ya sauke yace atleast ku daga min kafa mana ni fa a yaya na dauki m. Ahmad ba komai ba kuma na yarda dashi dari bisa dari.
Shima nasan ya yarda da ni kuma bazai bari wani Abu ya same ni ba. Kamshin turaren m. Ahmad ne ya karade parlourn a yayinda yake zura mukullin sa a aljihu yace wannan haka yake brother maganar ka ba tantama.
Sis billiy tambari tace m. Salis Dan Allah toh in tambayeka mana. Yace aunty Billy ai kya bari na Dan zauna ko? Tace bismillah zama yayi a Kan carpet tace zan iya tambayan? Tace bismillah.
Yace toh yanzu kai ina kudin gadon ku yake? Kuma in an tashi karbo maka hakkin ka wa za'a nufa? Murmushi ya yi yace kina tunanin mutum mara imani irin kawuna zai bar kudin ba tare da ya hallaka su ba?
Toh duk a caca ya banzatar mana da dukiya sannan batun wa zan kama Dan karban hakki na, munafukan matansa da suna gani aka cuce mu Allah ne zai raba ni da su bari kiga na warke ba gara ba zago sai na tozarta su a idon duniya.
M. Ahmad ne ya rike hannun sa yace brother kwantar da hankalin ka. Kar ka bata ranka mu bar wannan zancen kawai. mrs_tantiri tace yanzu idan da ace marakisiyya zata fito daga gidan auren ta zaka aure ta?
Murmushi yayi yace toh menene anfanin da ace tunda bazata fita ba. Kallona fans sukayi suka ce wai da gaske bazata rabu da lud ba? Gyara zama nayi 😎 nace idan na fada AI na bata zancen amma dai.......
Sis nafeesa tace karde zata fito ta shiga gidan m. Ahmad? Nace karku damu ko ma menene ya faru komai zai dawo normal kude ayi karatu kawai.
laeylerh tace hmm nikam gaskiya kar a raba mana su. Gyara glasses Dina nayi nace toh sai ayi azama wajen yin comment tare da SHARING din wattpad link Dina kuma ayi following.
Fans suka ce an gama miss karki damu. Rufe bakin su ke da wuya sai ga oga ya shigo da sassarfa da ka gani kasan daga wani Abu yake gudun.
Murmushin dake fuskarsa ne zai tabbatar maka da cewa tare da uwar house suke AI kuwa sai gata ta shigo a shagwabe tana fadin ya lud ka bani warin takalmi na.
Yace ni kinga alamun na dauki takalmin ki ne? Ban dauki takalmin ki ba ke kika cire abun ki a bakin kofa. Hararar sa tayi tace zamu hadu tare da yin sallama.
Nace daga baya kenan zauna kawai an gode.
Maman Ahmad tace nikam marakis muna da tambaya ko ince ina sa in tambaye ki. Ni a farkon labarin nan ke yar gayu ce wayaiyiya toh ya akayi kika fara fits....Da sauri nayi gyaran murya yayinda marakis tace tun farin labarin AI haka nake ko kinyi tsallake ne?sis zata rufa'I tace ni dama haka na Santa.
Umma be tace sannun ku fa mun gode sosai da kauna. Nan aka gaggaisa ta zauna. Hauwa baba tace umma wai ina abba ne.
Umma tace ya tafi wajen aiki wai yana da meeting ba zai samu zuwa ba. Fans ne suka Dan marmayso gefen umma kasa kasa suka ce umma wai ya batun auren su lud ne zai rushe ko kuwa?
Umma tace ya danganta daga abinda marakisiyyan ke so ni bani da abin cewa in taga zata zauna dashi toh sake rage murya tayi tace amma zanso su jone.
Marakisiyya tace me ake kullawa babu ni ne? Baki a hade fans suka ce kije kiji da mijin ki mu karki dame mu tare da darawa hakan yasa ta Mike ta haura sama tana turo baki ita a dole an gwale ta.
Ganin m. Ahmad ya tashi ya fita cikin bacin rai yasa kowa ya juya ya kalli inda ya Mike. Umaima lawan ABBA muka gani tayi tsamo tsamo tana zaro ido kamar beran da ya fada cikin koko.
Kallon da ake aika Mata yasa tace ni fa ba wani Abu nace masa ba kawai tamabaya nayi ko yana da uba shikenan sai naga ya Mike ya fice.
M. Salis ne yace dalla rufewa mutane baki kamin ya Mike ya fice. Nan kowa ya fara shirin watsewa tunda abin yazo da bacin rai.
Sailuba ne tace toh wai ni ba'a lura ina parlourn bane ko kuwa baza'a tambaye ni bane? Riko hannun Aisha tayi tace please no kam inason na koma wajen sweetheart ko aure na ne yayi nayi nadama yanzu ko sakani a labarin ba'a yi.
Fincike hannun ta sis aysha tayi tace ke ni sake ni kar ki shafa min bakin jini ko ace ke nake yi bar gefe na. Allah yayi miki shiriya.
Bayan an firfito an fara duruwa a bus din da aka zo sai ga mansura da beeba an kashe daurin Dan kwali. Takun nan daidai ake yi. Beeba tace la kode an canja venue ne na dauka a gidan su umma za'ayi.
Kallon da aka tsaya ana binsu yasa su tsarguwa lode wankan nasu nayi bane dukda ba wani kwalliya suka dambara ba. Haka suka bi motan da ta banka musu hayaki har ta fita suna masu kallon juna ba tare da gane me ya wakana ba. Wani zubin AFRICAN time bai yi ba.
Miss untichlobanty 💕
22nd September,2020.
YOU ARE READING
YA JI TA MATA
Mystery / ThrillerWannan labari me suna YA JI TA MATA shine littafina na uku.... Labarin wani saurayi ne Wanda bashida aiki sai zina, a cewar sa ba laifinsa bane Allah ne yayi sa hariji. Toh hakan ne yasa iyayen sa suka rufe ido sai yayi aure amma fa an gudu ba'a tsi...