CHAPTER 32

1.2K 158 11
                                    

Cikin jin dadi ta Mike ta dauki camera zata haura sama kawai taji ance KE ZO NAN DAN UB....KI!

Wani sauti cikin ta ya bada yayin da lokaci daya wani gumi ya karyo Mata domin wannan karan tasan ba kanta kawai sai yadda Allah ya yi da ita.

Ganin tana bata masa lokaci yasa yace ba da ke nake magana ba? Shegiya siririya sai kace masakacin hakori.

A hankali ta juyo saboda wani mugun fitsari da ta soma ji. Yace zo nan kan inci uw....ki. kamar an ma ta duka haka ta janyo tsinken kafafun ta ta karaso inda ya ke.

Tashi ya yi ya zauna kamar uban mutane ya sa hannu ya danna kafadar ta sanda ta Russian Alan guiwowin ta ya ce fara bayani me ke faruwa?

Hmm AI anan akeyin ta nan baki ya fara rawa ta hau inda inda hannu yasa ya warto ta tare da ajiye Mata wani zazzafan tafi a kumatu ya ce ki fara bayani nace k?

Fitsarin da ta rike ne ya sauko ya gangaro hat kasan kafar lud din wani murmushi ya ajiye Wanda bai taba yin irin sa a kan idanun ta ba.

Kasa kasa tace wow this girl is really turning into something else. Shako wuyan ta yayi ya ce ke Dan....nayi kama da sa'an ubanki? Shegiya tsinanniya toh ko kisa baki ki lashe min kafa na ko kuma uwar ki ta haifi wata.

Toh a ranan ne fa marakisiyya ta fara yiwa lud rashin kunya sannan a ranan ne ya fara saka ta kasan fitsarin ta. Gyara zama yayi ya miko kafan sa ya wani lumshe ido jin shiru bata fara lashewa ba yasa yace uban me kike jira?

Ga matukar mamakin sa sai ji ya yi ta ce wallahi Allah ya isa na kuma uwata bazata haifi wata ba Dan ba abinda ka isa kayi min ta Allah ba taka ba. Kuma karka kara ce min shegiya domin kuwa ubana shine uban ka saide in kaine....

Sai kuma tayi shiru. Lud Wanda mamaki yasa shi kasa yin komai bai ma San yadda aka yi ba kawai tsintan kan sa ya yi yana mai jibgan marakisiyya da duk abinda ya samu.

Kamar ya Sami Kato haka yake harba Mata naushi. Umma na sama take jiyo hayaniya kamar wata me aljanu haka ta fito da mugun gudu Dan yadda taji sautin marakisiyya ya karkade gidan ta ko ina.

Da sauri ta janye diyar ta tana fadin kaide wallahi anyi banza mugun yaro wato Dan bace kar ka sha min sigari a tsakiyar parlour na shine zaka huce akan diya ta ko?

Kallon marakisiyya da ta makale a jikin umma tana fadin hannuna waiyo Allah hannuna ya yi yace kinci....ki AI baki ga komai ba ma. Umma ji abin da wannan me wuya kamar Marikan leman tayi min a fuska na fa amma wai yarinyar nan bai isheta a hakan ba shine harda yi min Allah ya isa?

Umma tace au dalilin da yasa kayi Mata dukan kawo wuka kenan ? Kai bakasan wasan ya da kanwa bane? Kallon marakisiyya tayi tace ke! Ce masa Allah ya isa. A hankali marakisiyya tace Allah ya isa saboda yadda take jin hannunta kamar ba ajikin ta ba Dan kuka ma yaci karfin ta.

Umma tace da karfi zaki ce masa Allah ya idan ki kuka ki Dena yi masa kuka domin kin zama budurwa kema yanzu shekaran ki 14 fa kema kin fara girma abin ki bai isa ya mayar min da ke baiwa ba.

Maza fadi naji, marakisiyya tace ALLAH YA ISA NA MUGU KAWAI! YACE AKAN UWAR KI. UMMA TACE NICE UWAR TA AI DA KA FITO KARARA KAYI MIN ALLAH YA ISAN KAJI KO HAMSHAKI ? YACE KARYAR BANZA KAWAI.

Yana kaiwa nan ya fice daga gidan Dan ba karamin haushin umma yake ji ba yadda ta fifita yar kanwar ta a kan sa amma ba hali ta fada wa duniya.

Da yamma ne bayan umma ta dawo da marakisiyya daga gidan guaran targade ta ce Mata take ta bawa yayan ta hakuri nan fa ido ya raina fata ta shiga tashin hankali take idon ta ya ciko da ruwan hawaye umma tace kar ki damu tare zamu in jira ki a bakin kofa.

Toh a lokacin da ta shiga dakin ne ta samu yana bacci abinsa kamar ba shi ya jibge ta ba ya wani bata rai kamar yadda yayi a yanzu da sukayi aure.

Bata ankare da cewa tana zubda hawaye ba sai bayan ta gama tuno labarin da sauri ta goge hawayen daidai lokacin oga shima ya bude idanun sa. Yace my tsolon rake ya dai? Me yasa kike kuka?

Murmushi tayi tace ba komai rashi muyi sallah lokaci yana shigewa. Kara tura kanshi cikin rigan ta yayi yace no ah ah akwai abin da nake nema tukun na. Ture kansa tayi tace matsa ni AI ko zan baka ka bari ayi sallah balle ma bazaka samu ba yace ni mijin ki ne fa?

Tace ina sane sarai ka yi Abu kamar mijin nawa toh nima zan zama matar ka. Yace ya kamar mijin naki yake? Tace bayan mun yi sallah zan fada maka.

Bayan sun idar da sallan magrib tayi masa tambayoyi da gyare gyare akan yadda ake limanci sabosa tana so ya dinga Jan su sallah yace bari na Nemo mana abinci ko? Tunda yanzu de kin dirki bacci yau sai hira kawai ko ya kika ce yar tsimburbura?

Kallon sa tayi ta ma rasa me zatayi dariya ko kuka ko ta tabe baki ne ko tayi tsaki tace wai ni kam wai me nayi maka ne ?

Yace me kika gani? Tace duk sunan da zaka saka min babu na arziki daga tsililiya sai tsolo sai tsumburbura? Janyota jikin shi yayi cike da tsokana yace da ki fadi kanki tsaye AI kice kina son sabon sunan ki ko tsumburbura?

Bude kofan dakin tayi ta turo shi yana dariya yana tsunburbura please mana ki tsaya mu Dan kara yin hira. Tura shi waje tayi tana fadin jeka jeka jeka kamin kasa min hawan Jini Yunwa ma nake ji.

Yace toh wani irin nama kike so? Da sauri ta bude kofan tana washe baki tare da shafa ciki tace tsire nake so Wanda yaji albasa kai kodan bashi ba ka siyo min gas meat kawai.

Janyota yayi jikin sa hannunsa kan kwankwason ta yana da rausayawa dasu yace in ga bakin kwadayin nan nikam. Bude baki tayi ya kyalkyale da dariya yace ji kwadayi yanzu nan an koreni daga jin batun nama harda bude kofa ko?

Kinaso ki sude min account Dina ko? Dan kudin da daddy ya banin banging nami wayam abi? Tace sanda bakda Mata ma ya baka ka kashe ma wasu balle yanzu nide fatana ka fara yin aikin kanka kawai. Yace hmmm🤔 akwai kamshin gaskiya a maganar ki zanyi tunani kuwa indai haka ne.

Kinga in na fara aiki ma daddy zai ga na zama cikakken mutum kamili kuma responsible tace correct mai gida na👍🏻 ashe dai ban fahimci mijin nawa bane muka dinga yin fada a baya.

Kallon ta ya tsaya yi ta juya ta kalli baya tace menene ?  Yace a hankali yace maimata tace me? Yace me kika Kira ni yanzu? Tace mai gida na? Ya hm (yes) shi nake so ki maimata.

Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da yatsan ta tace mai gida na. Washe baki yayi yace har naji kamar nafi kowa girma da yin hankali a duniya wallahi.

Turo baki tayi ta daura hannunsa a cikin ta tace yunwa nake ji mai gida. Yace yan zu zan Nemo abinci uwar gida. Suka run tsire da dariya a tare.

DAN ALLAH FA ZAN KARA MAIMAITAWA A GUJI YIN SHARING A GUJI YIN SHARING DAN GASKIYA DUK WANDA YAYI SHARING TOH IN MUKA DAINA DASAWA YA KUKA DA KANSA.

INA KAUNAR KU KUMA INA ALFAHARI DA KU FANS DINA.  TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

2nd September,2020.

YA JI TA MATAWhere stories live. Discover now