CHAPTER 55

943 107 17
                                    

Da wanna tunane tunane har bacci ya kwashe m. Salis bai sani ba. Hakan yasa bai samu yin sallar magrib ba sai hada ta yayi da isha'i.

Shida abin har ciwon kai ya fara bashi Dan baiga m. Ahmad a masallati ba, kai me jummalo tayi ne wai? Ko da ya shiga gidan mama kamin ya karashe sallama ta nufo sa kamar zatayi kuka tana fadin salisu wai me ya Sami Dan uwan ka ne?

Yace mama nima abin da nazo ji kenan tun dazu na kasa gane kansa na ga ko masallati bai zo ba. Abin har ya fara bani tsoro ma wallahi.

Dakin m. Ahmad din suka sake nufa sukayi knocking har suka gaji amma shiru ya ki ya bude. Jiki a sanyaye ya nufi gida yana shiga kamar zai wuce dakin jummalo wani Abu yace mai ya duba dai. Muryan mando ya jiyo Wanda ke kwance akan kujera.

Mando yace ina wuni ya salisu? Gaisawa sukayi tare da yin musbah kamin m. Salis din ya nemi waje ya zauna a gefen sa.

Mando yace ya salisu wai adda ta tafi anguwa ne naga bata daura abinci ba kuma yunwa nake ji. M. Salis yace tana nan ba ta jin dadi ne mu je mu siyo abin ci ko?

Rufe gidan m. Salis yayi tunda ba sa gida akwai hatsari amma ya bar Mata mukulli ko da wani bukata zai taso na dole sai ta fita Allah ma ya tsare.

Bayan kamar minti 20 suka dawo, mandi har yaci abinci yayi bacci amma jummalo bata fito. Ganin fa zata kashe kanta ya saka m. Salis ya tafi ya fara Nemo inda ya ajiye mukullan gidan da kyar ya samo shi a madabak ina nufin kitchen.

Ko da ya bude tsamo tsamo yaga tana zazzare ido  tare da girgiza kai kamin ta fara fadin wallahi ni ban San shi bane Allah bansan ya Ahmad bane.

Dafa kafadan ta m. Salis yayi yace kwantar da hankalin ki jummai haba ya kika azalzali kanji kamar wacce tayi kisa? Baki na rawa tace ba.. ba zaka dakeni ba?

Gira daya m. Salis yayi yace me zai sa in dake ki? AI baki yi min laifi ba. Ajiyan zuciya ta sauke kamar ba ita ba ta washe baki tace 'kanhin abinci nake ji me ka sayo mana ?

Yace yauwa yanzu naga jummalo na. Shredded chicken salad da kebab na siyo. Tace tab wannan sunan AI kai kasan abin ka ni yunwa nake ji.

......

Wasa wasa m. Ahmad ya rubuta letter ya dauki hutu na sati biyu ya kulle kan sa a gida kullum bashi da aiki sai addu'a na Allah ya yaye masa ko ma wani masifa ce ke tare da shi ya kuma tsare sa daga cikin Wanda zai fada.

Haka m. Salis take zuwa makaranta shi daya ya zama abin tausayi. Jummalo ma dai duk sanda ya fita toh ta dinga fadawa tunani iri iri wasu masu ma'ana wasu kuma dai... kin dai San mutuniyar.

.....

Yau an yashi a makaranta marakisiyya, habiba sa mansura suna shirin tafiya suka hadu da m salis. Beeba ce fara ta gaisheshi kamin marakis ma ta gai da shi sama Sama Dan basu wani Saba ba.

Mansura kam dauke kai tayi kamar bata Ganshi ba. Beeba tace malam dama naga kenan biyu malam Ahmad baya zuwa lectures dinsa da muke da su shine nace bari mu takabaye ka muji ko lafiya.

Kasa kasa mansura tace ki tambaye shi de, uwar iyayi sannan ta tabe baki. Da ido marakisiyya ta Mata alamun irin me haka? Ba dadi fa. Kafada ta daga alamun ita ba abin da ya dame ta.

Murmushi m. Salis yayi ma beeba yace  lafiya kalau kawai tafiya ce yayi zai dawo soon. Yana kai wa nan ya shige motan sa yayi gaba Dan kare mutun cin sa.

Motar sa na barin wajen ms madeena wanna me son m. Ahmad din ta bullo gaban beeba tazo ta aika Mata wani kallo tace katuwar banza kawai, ke shugaban aji ce zai dame ki in malamin ki bai zo ba.

Marakisiyya ne tayi taku daya wato one step forward tare da daga gira daya yanda lud keyi Mata yare da Dane baki  wanda bata ma San ta koya ba tace toh sannu magajiya in ita karuwa ce, ni ban masan me ya samu idon Wanda ya dauke ki aiki ba. Mtsww! Banes muje Dan Allah.

Nan suka bar madina ta ma rasa me zata ce tana kumfa Dan taso ta ci mutuncin beeba ba kadan ba. Bayan sun Dan yi nisa ne sun kusa zuwa inda motan su yake mansura tace duk ai laifin ki ne me na wani tambayan inda m. Ahmad yake?

Beeba tace kawai mutumin burgeni yake shine Dan na tambayi inda nake nayi laifi? Mansura tace ba tambayan bane damuwa ta, ki rasa aanda zaki tambaya sai wannan mutumin?

Marakis tace beeba kin dai yi sa'a yanzu banason m. Ahmad da na bige miki baki ke kuma mansura me naki da salis dinnan bai rike miki komai ba kawai ki kullaci mutum?

Mansura tace ni fa mutumin ne kawai bai yi min ba, mutum yana Abu kamar mace sanyin sa yayi masa yawa haba Dan Allah,  ji yadda yake da ido sanda yake mana nagana Lamar na cokale.

Marakis tace ni kinga bazaki zo gefen mu kici mutuncin musulmi ba, kin dai San bazamu biye miki muyi gulma ba. Ajiyan zuciya mansura ta sauke tace bazaki gane bane ni Allah banaso ko mace naga ta fita sanyi ana dannar ta balle namiji. Ko Dan yaga yana da hakan fata ne oho.

Murmushi beeba tayi tace AI kuwa sanda kika fada na gani wallahi ya kai marakis ma haske ya ma fi Ahmad, awwn! Waiyo kyau. Dungure Mata kai mansura tayi suka fashe da dariya marakis tace kede farin namiji ne ajalin ki.

Beeba tace haba kema kin San kawai ina fada ne amma AI a aure ba a suba wadannan indai mutum zai bi shawaran annabi Muhammad SAW shi yace muyi aure ne saboda addini da kyawawan halin mutumin ko matar toh amma yanzu fa ba haka bane abin jama'a sunyi cilli da shawarar ko ince umarnin sa sun koma yin aure Dan wani abin duniya.

A hadisin da Abu hurairah ya karbo manzon Allah tsira da abincin Allah su tabbata a gareshi yace

Ana auren mace ne saboda Abu 4, dukiyar ta, nasabarta, kyawunta da kuma kyawun addinin ta. Sai yana yin nuni ko ishara ga me addini.

Hadith na 4802 a sahih bukhari, kuma hadith na 1466 a Muslim.

Mansura tace saide kuma kinsan wasu fa sun fahimci hadisin nan a baibai wasu suna ganin manzon Allah yana fadin mutum zai iya auran mace saboda wannan abubuwan ne wasu kuma suna ganin ma dole sai tana da duka kamin a aure ta.

Dariya mansura tayi tace ba San ba abin dariya bane amma ya ban dariya wallahi. Marakis tace abin fa me sauki ne. Kawai manzon Allah yana fadan fact na dalilan da yasa mutane ke aure ne sai ya bawa musulmai shawara cewa su me addini zasu aura.

Beeba tace ni abin da ke ci min rai, ke ci min turo a kwarya wai sai wasu mutane suce ma AI shawara ce alhalin wasu mala ma suna ganin umarni ce. Mansura tace toh idan ma shawara ce AI dole is dauka.

Yanzu ko Abu zakayi idan mahaifiyar ka ta baka shawara kuma bai Saba addini ba in kana da mutun ci AI shi zaka dauka balle shawaran manzon Allah. Wato dai a takaice in aka fassara aikin su fa kamar manzon Allah yace ka auri me addini su kuma suna cewa mun ji mun gode amma me kudi zan aura ko kyakkyawa zan aura ko yar babban gida zan aura.

Marakis tace ba laifi bane in ya kasance ta samu daya daga cikin wadannan ko duka indai tana da addini Abu ne mai kyau Romo ce Allah ya ga daman bawa mutum.

Jan kumatun ta mansura tayi da muryar tsokana tace irin baby lud ko? Yayin da beeba ke Mata signa da gira sannan suka fashe da dariya. Mansura tace ni Dan tuna min wani hadisi ne ma yayi magana akan abin da ake bukata a neman miji.

KWANA DAYAWA YAN UWA BA MU HADE BA DON ALLAH A SAKA NI A ADDU'A INA DA PHYSIC RANAN MONDAY.

INSHA ALLAH IN NA HUTA KO TALATA NE ZAKU JI NI. KAMIN MU SAKE NITSAWA CIKIN KARATU.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

YA JI TA MATAWhere stories live. Discover now