CHAPTER 29

1.2K 110 12
                                    

Badan taso ba ta hadiye. mintsininsa tayi da sauri ya Mike yana dariyan wayon da ya Mata cike da jin haushi ta dauki pillow ta cilla masa.

Tarewa yayi yana Mata gwaliyo yace kinga mr handsome shi yasa bakisan ma sanda kika hadiye maganin ba.
Haki ta fara yi kamar zatayi kuka kawai ta fadi gwajab ta zauna da sauri ya dawo ya rikota yace ke tsolon rake nifa banason irin haka abu kadan sai ki wani saki jiki Allah in kika kuskura kika mutu baki bani kurwata ba in na yarda su umma sun bunker me nake.

Kwanciya tayi ta bashi baya sanadin rashin kaya dake jikinta haurawa yayi ya leko fuskarta yace wai da gaske bakida lafiyan ne? Bige masa ciki tayi Wanda hakan ya sa shi kwanciya ba tare da ya shirya ba. Toh hakan ne ya ba ta dama ta dale ruwan cikin sa tare da murde kunnen sa tace zaka kara? Girgiza kai yake yi yana rike hannun nata.

Dariya ta kyalkyale dashi yace kiyi hakuri tsolon rake zanyi miki duk abinda kike so pls karki murda min kunne na. Tace da gaske? Da sauri ya girgiza kai tace toh so nake ka goyeni kayi ta kewaye dakin nan har sai nayi bacci. yace an gama sarauniya da girman kujeran ki a taimaka min dai kunne na.

Tashi yayi ya juya Mata bayan alamun ta hau ta daka masa duka tace bazaka kawo min Riga bane? Kawai ka kama ka cire min tufafi na. Dauko Mata wani Riga mara nauyi yayi ya mika Mata yana harhada rai kamar zaiyi kuka goyan ta ya yi ya fara kewaye dakin Jun shiru ba mai magana tace dokic ayi min tatsuniya yace ke wai ni bawan ki ne?

Tace duk abin da bakayi min ba sanda nake yarinya bashi zaka biya. Hade rai yayi yace toh sauka ta make kafada tace oh oh naki din yace zan yar da ke fa katuwar banza kawai tace yau kuma? Toh ka yarda ni kadai ji me umma tace yau dole ka kula da ni. Yace u...ki munafuka kawai.

Haka yaci gaba da kewaye dakin da ita a bayansa har ta yi bacci ya sauke ta tare da karkade rigan sa sannan ya yi mika. Ya fice domin ya kora abin. Wani bar ya tafi yana shiga akayi masa sannu da zuwa tare da tambayar sa wanne yake so yace a bashi whiskey kawo mai ita akayi da cup ya bude ya zuba.

Dauka yayi yakai kusa da bakin sa kawai sai yaji kuma bayason yasha. Ajiye wa yayi yana nazarin ko me yasa ya ji baya son yasha giyar? Dauka yayi yana jujjuyawa kawai tunani matsalar da ya baro a gida yazo masa.

Mamakin yadda cikin kasa da sati daya abubuwa dayawa suka faru dashi yakeyi. Daga kofin yayi ya karbeta lokaci daya saboda yanda ya ji ransa yana kuna Wanda ya rasa dalilin hakan haushin kowa da komai ya fara ji kawai ya fasa kofin ya fice abinsa ya koma hotel din.

Bankada kovar dakin yayi ya shige Wanda hakan yasa marakisiyya bude idon ta. Ganin sa kwance akan gado Rabin sa a kasa yasata taba kafadar sa a wasa tace ya lud duka gajiya goyan nawa ne? Ido jajawur ya dago yace ban sani ba. Ke ki fita a hakarta kamin in zagi uwar ki fa. Naga alamu sake miki fuskar da nakeyi yasa raini ya fara shiga tsakanin mu, banason dabban  ci fa.

Baki da hanci ta saka take kallon as Dan tsabar mamaki.mutum sai kace me aljanu ko kuma ciri ciri kawai shi daya dazu lafiya lafiya ana dariya da walwala the next thing kuma ya fara fada? Matsowa tayi kusa dashi ta taba goshinsa ya bige Mata hannu yana aika Mata wani buhun harara.

Dariya ta fashe dashi tana ja masa kumatu tace yi dariya please kafi yin kyau Allah. Kamin dariya kaji? Kara turnpike fuska yayi. Hannu tasa tana Dan wasa da dankunnen dake kunnena yayin da tayi abin tausayi tace yanzu wai da gaske kake yi bazaka min dariya ba? Gyatsa yayi ya ture ta ya tashi ya fada ban dakin saboda tunowa da yayi a hanyar dawowa yaji ana sallah.

Wanka yayi mamin ya yi alwala ya fito tare da canja kaya ya dauki sallaya ya shinfida dawowa ta gefen da yake tayi tace me zakayi? Ba tare da ya kalleta ba yace me idon ki ya gani? Tace sallaya naga kake shinfida wa yace correct Wanda ke nuna sallah zanyi.

Murmushi tayi saboda jin yace zaiyi sallah amma sai tace ai bazai yuwu kayi sallah ba. Kallon ta yayi gira daya a sama yace ko zan iya sanin dalili? Tace ba wai Dan cin zarami ko rashin girmama ka ba amma ka iya wakana janaba? Ka taba yi? Sannan kuma ka tuna yadda ake yin sallah ?

Kuma ko ka  cika sharudan nan bazai yuwu kayi sallah ba saboda kasha giya kana cikin maye kila shiyasa kake jin haushi na. Ta karashe maganar muryar ta a raunane kamar zata fashe da kuka ko wani lokaci.

Yace menene wankan janaba kuma? Tace wankan tsarki ne da mutum keyi a yayinda janaba ta kamashi ga ku maza kukan yi shi ne yayinda wani Abu ya shiga tsakanin mu da mace ko kukayi mafarkin mace in wani Abu ya fita daga jikin ku.

Yace I see ko me hujjar ki na cewa bazan iya yin sallah ba saboda na sha giya? Naga dai sahabbai ma sunsha giyar nan har bayan zuwan musulunci. Murmushi tayi tace da farko dai bayan.sake wanzuwar musulunci Dan dama tun da akwai sa domin shine addinin ko wani annabi. Toh sahabbai sukan sha giya amma wata rana kamar yadda abdurrahman bn as sulami ya rawaito cewa aliyu bn abi dalib yace:

"Abdurrahman bn awf ya hada yar walima haka sai ya gaiyace mu inda cikin abin sha harda giya. Da lokacin sallah yayi sai sukace ni zanja sallah inda na karanta "YA KU WADANDA BAKUYI IMANI BA,NI BANA BAUTAWA ABINDA KUKE BAUTAWA,KUMA MUNA BAUTAWA ABINDA MUKE BAUTAWA" a take Allah ya saukar da aya ta 43 na cikin suratul nisa'I: "

"يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَقْرَبُوا الصَّلَاةَ وَأَنتُمْ سُكَارَىٰ حَتَّىٰ تَعْلَمُوا مَا تَقُولُونَ...."

HADISI NA 3026 A CIKIN BABIN TAFSIRI LITTAFI NA 44, JAMI'A TIRMUDHI.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

YA JI TA MATAWhere stories live. Discover now