Mansura tace kuma fa mutuniyar magana ki dutse Allah ya yafe mana na baya ya kuma tsare mu daga aikata na gaba. Beeba tace wannan haka yake ke kinsan gara ke ma kina neman tsari daga ba gaba amma mutane in anyi magana ki lura fadi suke "uhmm toh Allah ya yafe mana wato zasu maimata kenan "
Marakisiyya tace ni ba wannan ba mansura akwai wani jarida da nake so ki sayar min fa. Beeba tace wato dama yar zagaye kuke yi min?
Toh wallahi sai an fada naji marakisiyya tace ba fa wani abun bane kawai ce Mata zanyi in taje makaranta tayi min duka handout da banida su. Zan fara fita shikenan fa.
Beeba tace nima abinda ke raina kenan zance wato ke yar dadi miji saide suyita yin note muna aiko miki hoto muna saka miki attendance ko?
Marakisiyya tace ku de kuka jiyo wai meke going a school din ne? Beeba tace AI dakika yi kwana uku baki zo ba tsohon class rep marakisiyya tace kice Yakubu.
Tace ke gara ke kin ma San sunan sa toh shine fa wai ke baki cancanci class rep ba ko semester daya ba'a gama ba kin fara fashi shine fa na rubuta letter na aika wa m. Ahmad dinki anan ne yace toh ya bani rikon kwarya kamin ki dawo tunda dama yasan da auren naki.
Kawai de bazai yuwu ya tsaya miki babu wani official letter bane kundai gane. Mansura ne ta zunguri beeba tace ke kin fiya kaudi yayinda take yi Mata nuni da yanda yanayin marakisiyyan ya canja.
Hakan yasa beeban tayi shiru tare da tashi tace ke bari kigani in rage mara sannan ta shige bayi. Mansura ne tayi saurin cewa ina jinki kawas marakisiyya tace ke ina ganin fa bawan Allahn nan daga min kafa kawai yayi.
Mansura da yake tana da sauri fahimta tace kice kin gurzu. Marakis tace AI naga dalilin da yasa suke guduwa Allah kuwa. Mansura tace toh me kike da niyan yi yanzu?
Marakisiyya tace tace me kuwa kike tunanin zanyi AI bazan zauna na mutu ba. Kamo kunnan ta tayi ta fada Mata abinda nima kaina banji menene ba.
Beeba ne ta fito tace hmm wallahi ban Baku wani labari. A tare suka kalleta tace jiya in fada muku bayan munje taron Q and A muka samu an tashi kin tuna ai ta fadi hakan tana kallon fuskan mansura.
Gyada kai mansura tayi beeba tace toh ba na sauke ki ba kamin na wuce gida. In fada miki ina tafiya ina ta nazarin ko me ya faru kawai mota na ta baci na ta sa yadda zanyi gashi yamma ya soma yi.
Marakisiyya tace nasan inda zancen nan ya dosa waye Dan samarin tsallake mana labarin. Beeba tace shegiya mutuniyar kamar kin sani in fada miki a banki yake aiki shine manager na branch din kano road.
Mansura tace kice in munje banki ba jiran layi. Dariya sukayi marakis tace me zamuci inyi muku order yayinda take kokarin bude fridge.
Beeba tace nikam wannan rayuwa sai kace a turai tabdi wai yaushe zaki bar hotel dinnan ne?Marakisiyya tace ke ni yanzu abun ya daina damuna in fada miki har na Saba banason mu tafi ma. Mansura tace hmm ke mu bar zancen yanzu tunda yau lahadi ne gobe zaku shigo ko yaya?
Marakis tace zamuga yadda za'ayi de zamuyi shawara da ya lud din. Mansura tace ratan dai kin shirya? Dan kinsan me ke jiranki a makaran tan nan. Marakisiyya tace kwantar da hankalin ki na shirya da izinin Allah. Nan suka ci gaba da hiran su har sanda lud ya dawo tukunna sukayi Mata sallama.
Yace ke haka ake yi tsumburbura? Nace ki shirya kuma sai ki rashe da hira ke da kawaye? Tace yi hakuri nima bansan zasu zo ba zancen makaranta ne ya kawo su kaga yanzu kusan wata nake nema a gida.
Ya kamata na koma kaga kuma an bani class rep. Ba dadi in Dade banje ba. Yace toh bayanin me kike yi min nace zan hadaki zuwa ne? Tace la wai ka yarda?
Daga kai yayi da sauri ta daka tsalle ta fada jikin sa tana fadin godiya nake Allah ya bar min kai tsaya ma na hada maka shayi. Hanyar bayi ya nufa wayar sa tayi ringing.
Har ta datse bai daga ba same ringing din tayi marakisiyya dake ajiye shayin tace ana kiran ka a waya fa. Yace waye ne ? Tace number ne baka yi saving ba yace ki dauka.
Ta na dagawa kamin ma tayi magana akayi caraf wajen cewa kai Allah na gode ma Allah ka dafa haba mana my luma karkayi min haka Dan Allah ka taimaka ni ko aure na ne kayi Allah na gane gaskiya.
Wallahi bazan iya rayuwa babu kai ba me yasa zaka zabi wannan halittar fiye da ni? Ka manta ne ? Ka manta yadda muke rayuwa cikin farin ciki? Ni na yarda yanzu zan haihu maka please Dan Allah. Kayi hkr bazan kara shan maganin da zai hanani daukan ciki ba.
Allah gaskiya kake fada min cewa muyi rayuwar mu irin na turai mu haihu duk sanda muka shirya muyi aure ni ina ganin kamar cuta na zakayi ashe gaskiya kake fada min kawai ta fashe da kuka wani mugun tsaki marakisiyya marakis tayi niyan yi.
Amma wani Abu yace Mata yi maganin ta kawai sai ta matsar da wayan gefe tace baby wai da wa kake waya ne kazo mu tafi a duba a tabbatar ko ciki lafiya lau yake tunda na suke a ban daki.
Wani mugun faduwa gaban sailuba yayi yayinda marakis din ta kashe wayan. Aka bar sailuba da tywan hawaye.
Lud kuwa da sauri ya fito yana fadin me kike fada ne? Wani ciki? Hade rai tayi tace ka kyauta wato baka rabu da wannan katuwar ba ko? Ya zakayi ka ci gaba da cin amanar a kan ido na.
Yace me kike fadi ne tace ka fini sanin me nake fadi me yasa wannan luba ko laraba ke kiranka harda cewa ka aure ta. Tsawa ya daka Mata yace marakisiyya ta daga hannu zata falla masa Mari.
Miss untichlobanty 💕
23rd September,2020.
YOU ARE READING
YA JI TA MATA
Mystery / ThrillerWannan labari me suna YA JI TA MATA shine littafina na uku.... Labarin wani saurayi ne Wanda bashida aiki sai zina, a cewar sa ba laifinsa bane Allah ne yayi sa hariji. Toh hakan ne yasa iyayen sa suka rufe ido sai yayi aure amma fa an gudu ba'a tsi...