Fadawa tayi jikinsa lokacin daidai waitress zata kai masa special coffee dinsa kamar kullum. Sanadin fadawan da tayi jikin sa hakan yasa ta tankwabe kofin coffee din.
Sulewa sukayi dukan su biyu ta bige bayanta. Ihu ta kwala da sauri ya rufe Mata baki ya Mike dam shima ya bige guiwar sa. Daukarta yayi da sauri suka fice Dan bayasan yan restaurant din su kawo masa raini.
Receptionist kuwa sai zuba murmushi take tace awwn ashe matarsa kyau gareta wallahi sun burgeni ko ba shi ba fa amma da kullum yana tare da wannan sh*giya dukurkuran karuwar. Rike hannun wata waitress tayi tace Dan Allah bata yi miki kyau ba?
Gyada kai tayi wata ma'aikaciya ma dake gefe tace har na ga yaransu wallahi sun shiga raina. Receptionist tace kede bari da ina planning yadda zanyi na samesa amma yanzu na fasa wallahi matar tashi ta shiga raina Allah ya basu zaman lafiya. Ameen kowa ya amsa.
Shugaban ma'aikata ne yazo zai wuce yace ms tahir(receptionist) ya naga hat yanzu kece a duty bayan shift dinki ya wuce. Tace wallahi sis mariya ne tace bazat zo da wuri ba yau shiyasa ban tafi ba.
Har ya wuce zai tafi ta biyo sa da sauri ta nuna masa hotan su lud tace sir kaga mutumin mu oga luma. Kalla yayi yana murza hana yace kai amma wannan karan yayi kamu mai kyau saide daga gani sabon shiga ce yarinyar ko?
Kallon me yasa baka zuwa gana ta masa ta sauke ajiyan zuciya tace kash dadi na dakai ba kyautata zato toh aure yayi matar sa ce. Yace what? Dariya ya fashe dashi yace cabdi oga luma manya me salo salo yau kuma hotel ya kawo matar ? Toh Allah ya bada zaman lafiya.
Har yayi gaba yayi baya yace baki ji ba, kur kur kur ta matso yace naga alamun nutsuwa a jikin sa dukda cewa hotone. Dariya suka fashe dashi tace kamar kana raina oga yace toh ya isa ya isa maza koma bakin aikin ki. Nan dai suka ci gaba da hiran lud da marakisiyya da yadda sukayi
Suna shiga mota ta kifa kai a cinyanta. Cikin bacin rai yace me haka tsolon rake ya zaki tsinkani gaban mutane kaman wasu sakarkaru. In so like ki taba six packs Dina ba sai kinyi wannan drama din ba.
Dagowa tayi fuska shabe shabe da hawaye tace wato kai abinda ya dameka kenan wani mutuncin da babu shi? Baka damu da cewa baya na yaji ciwo ba ko? Kai mutane ne suka dameka matar ka ko oho ko? Da sauri ya taba wajen ta danyi kara yace sorry yi hakuri bansan kinji ciwo bane.
In Munje gida sai inyi miki ruwan dimi ko? Ya fada yana danna wajen a hankali ture hannunsa tayi tace ka matsa banaso. Ba dai fada kake min ba? AI sai ka yankani ka huta.
Dafe kai yayi cikin tsawa yace wai ku Mata menene matsalarku? In an muku tsawa kuce an muku tsawa ba'a damu daku ba in an lallabaku kuma ku tsaya kuna jan aji wa mutum.
Hannu tasa tana dangwalan kirjinsa tace matsalar mu shine bakwa fahimtar mu da fari bamason ana mana mu'amala Lamar anayi da bayi. Qur'an mai girma ya tabbatar da cewa mu Mata a matsayi abokiya ya kamata ku rikemu saboda babu abinda mukeso kamar muga an nuna ansan Kumar mu.
Toh mu kuma a matsayin shugaba akeso mu rike ku domin babu abinda mukeso kamar respect sannan kun tsani raini kaga in haka ta samu sai zaman lafiya ta wanzu. Amma ya zakayi ka bawa kura dusa ka bawa akuya nama kace yunwa bazata kashe su ba?
Amma kai a rayuwanna....jamyota yayi ya rungume yace shhhhh! Ya isa ni banason kukan nan haka nace na daina ko? Kuma AI bansan ba da gangan kikayi ba. Yi shiru yar umma dariya suka kyalkyale dashi Dan tasan tsokanan ta yakeyi domin kuwa duk sanda take kuka haka umma take Mata, kuma ranan abinda take so shi za'a dafa a gidan.
Tunowa da wannan yasa yace kin samu paper din da na ajiye miki? Dan hade gira tayi yana goge Mata hawayen da ya fara bushewa tace ah ah ban gani ba. Yace okay.....
Waya ya daga yace large special threat muna mota. Tace abinci kayi mana order ? Da gira ya Mata alamun eh yana gyara sajen dake shinfida a fuskar sa.
Bayan minti 5 zuwa 6 sai gashi an kawo musu karba yayi ya kunna motar sa ya kama hanyar gidan su. Bayan sun isa ne ya tsaya daga bakin gate ya bude abincin da suka siya.Dauke kai tayi kamar bata gani ba ya bubbuga kafadar ta yace uwani abincin ma fushi ake dashi turo baki tayi ta sake kallon gefe ya kamo fuskanta ya rike bakin kyam ya tura Mata abincin furzarwa zatayi yace kina furzarwa zaki ga me zan miki a motan nan. Haka ya dinga dura Mata abincin abinda bai sani ba shine tana da allergy na green beans tace ya lud na koshi.
Yace baki isa ba so kike umma tace kin rame a sakani a gaba ko? Wai ke yaushe zakiyi imani ne kullum burinki kiga umma na tana min fada ko? Kicin kicin tayi da ido tace da inaso ayi maka fada da na fada Mata abinda kayi min jiya kuma da kake ce min yaushe zanyi imani kai kana da shi ne? Ko makiyiyar ka ce ni bazaka fitar dani cikin dubun daren nan ba amma haka ka diro dani ta window.
Sannan kuma ba umman ka bane umma ta ce ni daya can ka tafi ka nemi naka tunda saka ta kuka kake yi. Murkude baki tayi tana Dan yatsine domin jin yadda zuciyar ta ya fara daurawa. Yace God have mercy! Me zanyi da yarinyar nan ne ?
Kallon ta yayi yace wai ke wace irin zuciya ce dake baaaakida tafoya ko kadan ince abun nan ya wuce ko bakiji me bature yace bane past is past iye?
Tace ba wani past is past da an sameni da yanzu kana can kana fiki fiki da ido kana fesawa umma na karya yadda kayi wa yan sandan nan.
Yace iko sai Allah yau naga ma mutum ke wai ba har hakuri na ba....... shiru yayi ganin in yaci gaba da biye Mata raini ne kawai zai shiga tsakanin su nace wanne ne ma ba'ayi ba?
Tace inajin ka yace share kawai cire robbin yayi masu abinci kuma ya mayar cikin package dinsu ya ajiye a motan fita yayi ya fara shirin shiga.gida tace ah ah ni kuma fa ? Yace me zan miki ? Tace bazaka shigar damu gidan bane ? Yace me aiki kafafun ki ? Abin tausayi tayi masa tace Ayya banana banida baya ko ka manta ne?
Tsaki taja yazo ya dauke daidai zai saka kafarsa a gate yaji wani dam a kirjinsa hakan yasa ya tsaya da taku kallon fuskarsa dake kallon straight hanya tayi tace menene kuma?
Kin kallon ta yayi tace da taga kamar bayason ya kalle ta ma tace akwai wani Abu a fuskanta na ne? Waiyo Allah na karde muni nayi? Ko pimples ne ya fito min?
Baisan sanda ya kalleta ba yace wani makaryacin ne yace miki kina da kyau? Maiya kawai yana kaiwa nan yaci gaba da tafiyar sa yayinda marakis ke cika tana batsewa.
Yana salo kai kuwa yan aiki kowa sai zai miko gaisuwa sai mamaki ta rike masa baki. Da ido hanci da baki har da kunne haka suke binsu da kallon wasu har muttsika ido suke domin tabbatar wa wai shin da gaske Alhaji karami da hajiya karama ne kode matsala aka samu.
Me gadi ne ya jinjina kai yace aure dadi lud yace a gidan uban ka ba. Yana wuce wa kowa ya saki dariyar da yake kunshewa me yanke flower yace duk yadda Alhaji karami zaiyi hankali halin bazai canja ba. Knocking din kofa lud yayi yayinda yake fadin tsolon rake gaskiya nauyi gareki kan bala'I.
😂😂YACE BAYAJIN GARI YA DAUKA ZAI JI TA KAMAR PAPER
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
23rd August,2020.
YOU ARE READING
YA JI TA MATA
Mystery / ThrillerWannan labari me suna YA JI TA MATA shine littafina na uku.... Labarin wani saurayi ne Wanda bashida aiki sai zina, a cewar sa ba laifinsa bane Allah ne yayi sa hariji. Toh hakan ne yasa iyayen sa suka rufe ido sai yayi aure amma fa an gudu ba'a tsi...