CHAPTER 37

1.1K 138 24
                                    

Kinga duk sauran jikin ki sun iya karya har bakin ki amma gashi nan dai lips dinki sun kasa yi. Ko shin Dan suna yi ma nawa biyaiya ne🤔?
Bai tsammata ba ya ji tace zo nan nayi maganin ka tare hade.....su

Ya matukar mugun shan mamaki domin kuwa tunda yake aure auren sa  toh abinda ya sani shine washe gari wasan buya ake yi da mayar bawai ita da kanta ta kai kanta ba murmushi ya yi ganin abin nema ya samu.

Bayan awa biyu marakis zaune dare da towel ta cin kwai yayin da lud ke cin yam balls. Latsa waya takeyi yace ki ajiye kici abinci mana.

Gyada kai tayi kamin ta ajiye Wayan matsowa tayi gefen ta ya zauna yace toh me kike cin magani bayan ke kika fara yin move ni fa banyi niyar yi miki mugunta ba Allah kenan.

Tace ance maka akai nake bata rai ne? Yace toh akan me ? Tace ba komai kawai de hankali na ne bai kwanta ba. Gyara zama ya yi yace ah toh AI hakan yayi kyau mugama cin abinci sai mu.....

Da sauri tace na koshi, yace Allah kice bazaki iya jira ba to ajiye abincin tace ba da abincin na koshi ba ai. Fuskan abin tausayi yasa yace please mana only once.

Tace nope ban yarda ba rike hannun ta yayi tace kamin ma kayi min magiya bazan amince ba in ka takura min kuma zan kai karar ka wajen umma na ka dai ji mai tace.

Dariya yayi yace sai kace zaki iya wai zaki kai kara wajen ummi toh kice Mata me? Tace baka yarda ba kenan ko? Yace AI duk rashin kunyarki, kuma duk kusancin ku yanzu sirikar ki ce.

Tace toh bari kaga ikon Allah janyo wayanta tayi taga missed call din mansura biyu da na beeba guda 3 kiran beeba ta fara yi da sallama ta dauka.

Marakisiyya tace shiyasa kike burgeni beeba ba irin mansura ba kekam ba dai iya rafka sallama ba. Dariya beeba tayi tace tace amarya kenan AI ni bansan da wani baki ma zaki min magana ba saboda fishing da nayi duk hakurin da zaki bani bazan karba ba.

Lud da ya gane da wa take magana da gangan saboda neman maganar ta yasa ya fara tsoran kunnenta janye kanta tayi tasa hannu a kirjin sa ta ture sa.

Hannun ma kamwa yayi ya fara kissing Dan tsabar neman trouble. Harara take banka masa yayinda take fadin haba my beeba karki bari mansura taji kan mu kar muyi haka wallahi ba da gangan naki kiranki ba amma AI na tura miki message ta WhatsApp amma bakiyi replying ba.

Tace Ayya sorry wallahi kinga WhatsApp din ya samu virus ne shiyasa ba Dan naso ba haka nayi uninstalling shiyasa babu messages din amma AI jiya zakiga nasa please resend your last messages.

Shiru marakis tayi tunowa da jiya rabonsa da WhatsApp tun 12 din Rama murmushi kawai tayi yace AI jiya ban hau WhatsApp da daddare bane shiyasa ban gani ba. Beeba tace Allah uwar marasa kunya toh nima de mijin nan kinsan inada shi fatiha kawai za'a shafa.

Ke ni dalilin da yasa na Kiraki ma kenan yau aka kawo kayan sa Rana.
Marakisiyya tace shegiya kice Allah! Daga rigar ta da lud ke shirin yi yasa tace me haka ? waya nake fa.

A rada yace da kawa da miji wanne ne a gaba sharesa tayi yayinda beeba cikin neman tsokana tace Allah madam? AI bakiyi bayani ba da sai kice oga yana kusa kusa da bamu takaita zancen ba sai anjima.

Kit ! Ta kashe waya, kamar kura marakisiyya har wani tada ajiyan wuya  takeyi ta jiyo tace haba Dan masani hana Dan masani ya zaka dinga min irin haka yanzu nasan haka zasuyi ta tsokana na.

Kuka ta fashe da shi tace sai na fadawa umma na in ka sake yayinda ta Mike ta koma bakin gado ta zauna. Mansura ta Kira tana dauka mansurar tace kawas ina kika shiga nake ta rantaba Miki Kira in fada miki an kawo kayan sa ranan uwale fa.

Shirun da marakis tayi yasa tace aw na manta Salam alaiki uwar tsababi. Tsaki marakis tayi tace ke de kika jiyo ni bana son neman magana yanzu ma muka gama waya da ita take fada min.

Mansura tace Ayya ina Alhaji luma ne ko ya fice. Sama ta ka taji ta bayan ta yace gani anan makale a jikin ta. Hajiya mansura gaskiya na gode muku da kuka yi wa kawar ku wa'azi na gari.

Marakis ta mintsini hannunsa da ya lankaya a cikinta yayinda yake kwance ta bayan ta. Mansura tace aha ha toh bari na wuce dama zancen abin nan ne. Marakisiyya tace kar ki damu ba sai kin kawo ba.

Lud ne yace banaji fa marakis tace saboda na rage muryar baki daya ne banason gulma. Yayinda take cewa in kin siya ki mayar kawai bashida anfani.

Mansura tace Allah mutuniyar kice anyi an gama. Marakisiyya tace ke ni banason gulma fa toh tunda kin dani menene na tambaya?

Tace Allah ya baki hakuri sai munzo suna. Marakis tace a mafar kin ki in fada miki ba sunan da zaku zo. Lud yace kawayan naki kike wa bakin ciki bakisan suyi shagali toh nikam ina so ayi sunan nan tace kai ka jiyo nide ba ni a zancen.

Bude zip din riganta yayi ta kwala ihu tare da kashe wayar da sauri ta nemi layin umma. Karewa tayi a kunnan ta tace hello umma. Dariya yayi yace ance miki zanyi tsoro ne ki ni yaro je ba umman da kika Kira zaki rainani wayo.

Umma tace diyar kirki ya kike ? Tace lafiya kalau zuge zip din nata yayi tace wallahi Allah da umma nake waya kar ka bari zaka sani. Shi a tunanin sa karya take ba waya take ba hakan yasa yace umma kice wa yarki ta bani kiss guda daya.

Baki umma ta saka tace dama yaron nan har yanzu iskanci sa na nan shine baki fada min ba? Daddy dake gefe yanaji Dan wayan umman a hands free  yake yace wai me nake ji haka.

Marakis tace waima umma bai yarda daku nake waya ni kuma na Kira ne mu gaisa. Umma tace bashi wayan, mika masa wayan tayi yace ni rike wayanki please sau daya mana marakis sai in tafi wajen karatu kinsan ....

Hannu tasa ta rufe masa baki da sauri tare da kara masa wayar a kunnan sa umma tace sannun hamshaki uban hasiya. Nasan sanda yayi cilli sa wayar a tsorace yace wai dama da gaske umman ce?

Marakis tace da wasa zan maka ko su mansurar da na Kira wasa ne a sarai na fada maka waya nake tun dazu amma kai sai gajen hakuri. Yace toh AI lallaba ki nake yi saboda kice kin koshi. Murmushi tayi tace wasa nake bazan taba koshi ba tare da balle botin riganshi.

Umma dake cikin waya tana zabga hello tana jin haka ta Rifa wa kanta asiri Salinas alin ta kashe wayan ta. Daddy ko bai ma San shayin sa yake hadawa ya cika har yana zuba sai umma ne tace Alhaji ruwan zafi.

KAR KU MANTA ANTAYO MIN DA COMMENTS. TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

8th September,2020.

YA JI TA MATAWhere stories live. Discover now