IDAN KUNA KARUWA DA LABARINNAN AYI FOLLOWING DINA SANNAN AYI VOTING
Koda m.salis ya karaso wajen sa m. Ahmad yace gaskiya kana da kokari ba kadan ba kuma kana da hakuri. M.salis yace toh ya aka iya zata gane AI komai Dan lokaci ne. Haka suka fita suna hira su m.Ahmad bai tambayi m. Salis yadda ma ta kaya a daren jiya ba Dan yasan ansar tunda yaga jikin ta.
Haka dai har wajen azahar yan uwan jummalo suka San inda dare ya musu bayan m. Salis ya basu dubu biyar biyar m. Ahmad bai tursasa ya koma gidan sa ba Dan haka suka yi yawon su tare tunda weekend ne ba aiki gara ma m. Ahmad za'a iya neman sa a makarantan.
Da magrib lis m. Ahmad ya dawo da m. Salis domin a motar sa suka fita. Sallama sukayi m. Ahmad yace toh brother a kula da amarya sai munzo suna.
Baki m. Salis ya bude kamin yace kana nufin bazaka kara zuwa gida na ba? m.Ahmad yace toh ni me zanyi a gidan ka? M.salis yace ina brother baka isa ba AI kullum sai kazo m. Ahmad yace haba sai kace gida na? Barshi dai juma'a juma'a ina shigowa sai mu dinga gaisawa da amarya amma kullum AI muna tare a gidan mama.
M. Salis yace toh na yarda da wannan. Nan dai sukayi sallama m. Ahmad ya nufi gida m.salis shima ya shige gida. Sallama ya dinga zabgawa amma shiru ba amsa. Kara ya jiyo a dakin yaran hakan yasa ya fito yaje ya duba. Gani yayi jummalo da mando na cukun cukun cire hannunta da vacuum cleaner ya shanye.
Da sauri yaje ya kashe shikenan hannunta ya fita. ajiyan zuciya ta sauke tace kai kai kai gaskiya aradun Allah bani sake aiki da wannan abar kawai ni ka bani tsintsiya ta. Dafe kai m. Salis yayi Anya kuwa bai yi kuskure ba? Yace toh ya ma akayi kika sa yatsanki?
Turo baki tayi tace toh ba mando bane ya kai hannunsa wajen da yaji zubowa yakeyi shine Dan mugunta ice min in sa nawa ina karawa sai ya tura shine fa iskan taci gaba da jan hannun ga karhi ne da hi na kasa cire hannun nawa.
M. Salis yace toh ai ba'a saka hannu kinga yanda ake yi fa ba na koya miki ba? Saita komai yayi ya gyara dakin mando yace kinga yadda ake yi ba? Toh kema ki kiyi mu gani.
Daga nan ta kware tayi abinta mai kyau yace yauwa. Haka ya bita sukayi komai da komai tare domin kaman ba gidan amarya ba ita da mando daga gani kasan sunyi guje gujen nan nasu saboda me?
Parlourn gaba daya sun zubda cushion din, sun fado da labule daya gashinan gashinan dai. Yace Mata ga can dust bin a nan zasu dinga saka datti idan kuma danyan Abu ne asa a na kitchen mando ya dinga fitarwa ya zubar a can waje cikin babban dust bin din.
Tace menene dos bi kuma yace Dust bin akace ko trash bin shine kwandon shara. Bayan ta gyara ne yace sai anyi magana mutum da safe yace wa mutane yana da tsafta zaije yayi wanka.
Tace AI Dan bansan yadda zan gyara gidan bane hi yasa. Yace munji yana mai shiga dakinshi ya fada kan gado tare da rufe ido. Kamar Wanda aka zaune shi ya Mike yana kallon gadon a tsorace tunowa da basu gyara gadon inda ta bata ba kar yaje ya kwanta a kai amma sai yaga wayam.
Daidai lokacin ta shigo tana shan bakin shayi yace ashe de dagaske kina da tsafta? Tace ban fadi maka ba? Ai babu ya ni kaf kauyen mu aradu kayi dace. Nan ta zauna ta hau bashi labarin kauyensu bata ma San bacci ne ya dauke shi ba.
Sai lokacin sallah ta ga bai tashi ba anan ne da ta Kira sunan shi taji shiru nan tayi zuciya wai yace bakinta yana waring shiyasa ya kifa hula a fuskan sa yayi bacci. M. Salis Dan kar ya rasa sallah ne ya fice ganin in ya tsaya sai akai gobe bata sauko ba shi a dole za'a ce ya fadi abinda bai fada ba.
..........
M. Ahmad kuwa shima sanda yaje gida ne ya samu daman yin tunani ma. Dan gaba daya bai ma samu zama shi daya ba balle yayi tunani cikin bazance nazarcen sa ne ya tuno da sanda yaje gidan m. Salis din. Tare da tuno yadda jummalon ta bata jikin ta dadin abin m. Salis ya yaga Mata mayafi Dan idan da ta ita ne toh tabbas bazata saka komai ba.
Mikewa yayi ya zauna daga riginginen da yake yace idan kuma ba jinin al'ada bane fa? Toshe baki yayi kamar mace shima yace shege salisu ni wonder duk tsiyar da take masa ko ajikin sa.
Wani tunanin ne yazo masa wata zuciyar tace ina ruwanka? Kaide ka Samu ka nemi Mata kayi aure kamin kaji kanin ka yace ma zai zama uba kai ko mai gida baka zama ba.
Mahaifiyar sa ce ta bude kofa ita ma tana fadin baba na ashe ka dawo? Toh ka dai gani banson in takura ma amma kanin ka yayi aure kaima ka soma gyara naka gidan ka samu daga ka warke ka ajiye iyali.
M. Ahmad yace insha Allah mama AI nima gefen gidan sa ba siya gidana guda biyu zan fasa su koma gida sai na hade su. Tace masha Allah ka yi zurfin tunani toh Allah yayi albarka.
Yace ameen ba'a wani Dade ba aka Kira sallah hakan yasa shima ya tashi ya fita.
........
Bangaren su lud kuwa yanzu zaman lafiya ake ba tashin hankali. Marakisiyya ne ke saka musu kayansu da aka kawo daga wanki da guga yayinda lud ke zaune a kan gado yana neman aiki Wanda ya fara ne kwana biyar da suka gabata.
Tace wai har yanzu baka gama ba? Yace na kusa ina diba wani Abu ne. Bayan yan mintuna kalilan ya rufe laptop dinsa yace albishirin ki. Tace goro yace na samo mana gida Wanda yake daga nan ba nisa da gidan umman ki kwalta biyu ne.
Anguwan opposite din anguwan mu ne tsalle ta daka tana mai fadawa jikinsa tace kayi Allah kayi mijina Alhamdulillah! Nuna min hotan gidan ba gani.
Yace nope surprise ne kuma ban ma fara gyaransa ba jiya na siya yau muka gama komai. Tace gaskiya nayi farin ciki Allah yayi albarka ya kara arziki yace toh tashi. Tace menene? Yace da fari dai idan ba jariri kike nema ba ki tashi, na biyu kuma kalli bayan ki ta juya tace banga komai ba.
Tana Jan kwalar rigansa tace ko guduwa kake son yi? Yace ni zaki yi wa shagwaba? Young lady gyara muryanki ko kiyi shagwaba da dalili. Bude baki ta yi zatayi magana yace kalli kasa.
Dafe kirji tayi ta Mike tare da daka masa duka tace shine bazaka fadamin na barar da kayan ba? Yace kinci bashi dukan nan nawa da kika yi. Tashi yayi ganin lokacin sallah ya kusa ya bude kofa zai fita yace kuma yau bazan kwana a nan ba tunda abin harda mugunta.
Da tsawa tace baka isa ba kamin ta fashe da kuka tana mai fadin ka siyo min gasasshiyar masara. Dariya yayi yace na 'ki din mai hakwaran masara😂
INJI COMMENTS, VOTES SANNAN AYI SHARING KAMAR BA GOBE, IN AKAYI HAKA TOH ZATA FASHE AMMA ARZIKI NE ZAI FASO.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
YOU ARE READING
YA JI TA MATA
Mystery / ThrillerWannan labari me suna YA JI TA MATA shine littafina na uku.... Labarin wani saurayi ne Wanda bashida aiki sai zina, a cewar sa ba laifinsa bane Allah ne yayi sa hariji. Toh hakan ne yasa iyayen sa suka rufe ido sai yayi aure amma fa an gudu ba'a tsi...