CHAPTER 56

827 116 33
                                    

Jan kumatun ta mansura tayi da muryar tsokana tace irin baby lud ko? Yayin da beeba ke Mata signa da gira sannan suka fashe da dariya. Mansura tace ni Dan tuna min wani hadisi ne ma yayi magana akan abin da ake bukata a neman miji.

Haka dai suka ci gaba da hiran su har suka rabu ko wacce tayi gida. Marakis na shigowa dakin su ta samu lud yana saka Riga tare da daukan mukulli.

Tace ustazu ina zuwa ? Yace zanje na duba gidan mu ne naga progress din. Tace ko na zo mu tafi tare pecking goshin ta yayi tare da shafa kanta yace karki damu wifey ki yo hutawan ki I want to surprise you.

Gyada kai kawai tayi ta sake taje masa gashi bayan ta ajiye jakan ta sannan ya fita.

........

M. Ahmad ne zaune a dining table din gidan m salis yana shan shayi kamin jummai ta fito daga kitchen dauke da farantin abinci dauke da ciki niki niki.

Da sauri ya taro ta tare da karba yana fadin yi a hankali matar my kar kiyi mana asara. Kasa kasa tayi da murya tace hmm gara da kashe matar ku kam da naka Mata kuma nashi.

M. Ahmad yace ni kam har yau ina nadaman abinda na aikata amma naga ke ko da damun ki baiyi ba. Tace toh in na damu ma mai zai shanza? Ni fa kai Nike so kawai dai Dan na aure shi ne.

M. Ahmad yace nikam aure zanyi gaskiya, wani harara jummalo ta aika masa tare da cin kwalar sa tace ka kara maimata wannan magana a bakashin danka. Indai ina raye baka isa ka auri wata ba.

M. Salis da ya sako kafa daya ne yayi mutuwar tsaye kamin yace me kike nufi dansa. Jummalo da idonta ya rufe da kishi batasan sanda tace yo danshi mana ko da anshe ma danka.

Wani kwallo m. Salis yayi da ita ta kifa kan titsetsen cikin ta ba tare da bata lokaci ba jini yayi Male Male.

A zabure m Ahmad ya tashi daga mummuna mafarkin da ya fara yi yau kwana uku kenan, gaba daya ya jike da gumi sai haki yake kamin yayi addu'a ya sauko daga gadon sa ashe lokacin sallahn la'asar ne yayi.

Sallah yayi tare da addu'a sosai kan Allah ya sa shawarar da ya yanke ita ce mafita a gareshi akwatin shi ya hada tare da zama ya rubuta letter ma mahaifiyar sa tare da sanar da ita kar ta sha wahalar neman shi zai nemeta in yabar kasan sannan ya saka akwatinshi a mota ya dauki duk documents da yake bukata. Ya kama hanyar birnin taraiya domin tafiya Chicago Dan samo karatun PhD wanda ya nemi admission kuma ya samu.

Wajajen magrib m. Salis ya shigo domin gaida mama sannan ya samu ya duba Dan uwan nashi. Bayan sun gaisa da mama tace bari ta kawo masa ruwa yace tayi zamanta bari ya dauko da kansa. Jiki a sanyaye ta ga m. Salis ya fito gaban ta yayi mugun fadi Dan tayi tunanin ko cutar da ta kama m. Ahmad ce ta kama shi.

Mikewa tayi tana fadin salisu kayi wa Allah karma ka fara kaga Ahmad ma daga haka ya fara. Miko Mata papern kawai yayi kamin ya zauna ya saka hannun sa cikin tafukan hannunshi.

Umma kam kin karantawa tayi tace ni fada min abinda ke ciki banshirya hawan jini ya bige ni ba. Haka ta dinga magana har ta cure rai cewa m. Salis zai kulata kawai sai taga ya dago idon sa abun tsoro yayi ja sosai dukjijiyan jikin sa sun tashi kamar zai zubda hawaye yace ya bar kasan.

Tace wa? Waye ya bar kasan? Kallon kofar dakin m. Ahmad yayi da sassarfa ta bankada AI kuwa bayanan. Tace kai salisu Kira min shi, ka Kira sa nace.
M. Salis yace yace karma mu Kira shi.

Daukan wayanta tayi ta lafta masa Kira har ya datse bai dauka ba zata sake Kira m. Salis ya karbi wayan yace in kika fiya Kira zai kashe wayar tunda dai a bude take na San me zanyi.

Wayarsa ya dauko ya tura ma m. Ahmad din sako cewa mama ta yanki jiki ta fadi. Cikin minti biyu m. Ahmad ya Kira sa ysna dauka yace masa ya jikin nata ? kun kaita hospital? Me likitan yace? M salis da ransa ya baci saboda yadda m. Ahmad din ya musu yace ka damu da mahaifiyar taka shine ka tattara zaka bar kasan?

M. Ahmad sanda yaji tsoron m. Salis ya shiga zuciyar sa Dan basu taba ganin ranshi ya baci ba kullum abun tausayi kuma unserious. Mama ne tace kai salis karkuyi fada kawai kace masa ya dawo gida.

M. Ahmad yace dama karya kayi min? Salis ashe zaka iya min karya kuma karyan ma da mahaifiya ta? M. Salis yace au kai abinda ya dame ka ma kenan? Ahmad nace abinda ya tsaya ma a rai shine nayi maka karya? Kai da ka bar mu fa? Ashe dama zaka iya barin mu ba ko sallama bare bayani?

Me aka ma? Me aka rageka da shi me ka nema ka rasa da zaka bar gida kuma harda rubuta letter na jinginar da aiki? Toh indai Allah ne ya halitta min hannuna toh ba shakka ni dai bazan kai wannan letter ba. Cikin daga murya m. Salis din yace wai me ka nema ka rasa ne duk kabi ka tada wa mutane hankali ka zama kamar zaucacce?

Cikin daga murya shima m. Ahmad yace MATAR KA ko zaka bani ne? Salisu nace ko saka bani ne? Na tabbata in naci gaba da zama ina kallon ku dayan biyu ne ko na cuci kowa ko na cuci kaina.

Shiru ba Wanda yayi magana har lokacin da m. Ahmad ya ji ana ce mai your call credit has been exhausted and your call is terminated, dial.........

Sauke wayar yayi daga kunnensa yana mai goge kwalla dake kokarin sauko masa sannan ya ja akwatin sa ya shige hotel domin samun makwanci kamin su daga washe gari da daddare.

Shi kuwa m. Salis tunda yaji kalaman m. Ahmad ya saka wayar sa yayi a aljihu bai damu da ya kashe ba sannan ya nufi gidan sa yabar mama tsaye ta ma rasa me zatayi ko tace dukda ko bata ji me suke cewa ba.

YAN WATTPAD PLEASE DON'T FORGET TO VOTE AND COMMENT OOO, THAT'S MY ONLY MOTIVATION.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

YA JI TA MATAWhere stories live. Discover now