Murmushi tayi tace ba komai kawai de yau dinne nake ji nan wani iri. Tana kaiwa nan ta bashi waje sanadin wani Kira da ya shigo wayar ta.
Abinda bata sani ba kuwa shine da jikan kawar ummi yake hira yarinyar bata da zance sai cewa in ta girma zata auri uncle lud.
Toh shine maman ta takura lud din take sanar dashi zasu zo bikin kanwar ta anan ne fa yarinyar ta karba take ta yi masa karadi.
Daukan wayan yayi yarin yar me suna nabla tace uncle nayi mantuwa yace me kika manta tace iye baka gane ma me na manta ba? Yace ah ah. Dafe kirji tayi kamar yana kallon ta tace waiyo zuciya ta.
Dariya yayi yace gaskiya zance wa mummy dinki ta hana ki kallon TV. Muryan maman nata ya jiyo tana fadin ke habla me kuma kike min a waya. Da sauri tace I love you uncle bye ga mummy kar ta dake ni.
Dariya shima yayi yace love you too sannan ya kashe wayan zuciyan sa daya Dan bai dauka marakis din zata ji wani abu a ranta ba.
Dagowa yayi zaiyi wa marakisiyyan magana amma ganin yadda tasha mur yasa shima ya share ta Dan ya lura wani jujun rashin mutunci ne ya hau kanta Dan haka in ta nutsu sa zo su fafata.
Research dinshi ya ci gaba da yi Dan shi yanzu da ga ya Dan samu lokaci toh research yake yi akan addinin sa. Tunowa yayi da zai siyo littafin koyan hada baki hakan yasa ya Mike.
Kallon marakisiyya ya yi yace ni zan fita karki bude kofa ma kowa sai na dawo. Ciki ciki tace da nace ma zan budewa wani ne?
Sarai ya ji ta amma ya basar yace kar ki manta ji bi ne za'a fara bikin shamsiyya su aunty kwaise ma zasu zo.
Okay kawai tace shima ya fice abin sa kofin ruwan da ta ajiye masa tabi da kallo taga ko tabawa bai yi ba kwafa kawai tayi.......
An fara biki kuma da shike kawar umman su yan boko ne suna ganin sun waye yasa aka tsara shagali iri iri gidan su lud kam wannan baya gaban su in zasuyi biki babu wani tashin hankali..
Saboda bikin yasa su lud da marakis basu wani fiya hadewa ba sai dare lokacin ko duk sun gaji anyi tilip yayin da oga lud ke ta kokari yana hada baki abin yayin da yake koyan rubuta su.
Tana shigowa ta canja kaya ta kwanta a gado Dan babu abin da zata tattare. Kallonta lud yayi yace iyayen biki kinci abinci? Kinsan anyi ruwa fa kar ki zauna da yunwa ulcer zata kama ki.
Tace na ci tare da su shamsiya amarya yace toh yayi. Can ya matso yace marakisiyya in tambaye ki mana tace ina jin ka. Dauko littafin sa yayi yace Dan Allah ya zan furta wannan ? Kinsan larabci ba dai wuya ba.
Fada masa tayi haka kawai ta ji tana hucewa ganin yadda ya maida hankali yake karatu. Tashi tayi ta hado masa shayi tace in saka maka madara? Girgiza kai yayi ta kawo masa ya karba tare da yi Mata godiya.
Leka takardan tayi tace ka manta bakayi wa ن din digon ta ba yace tana da digo ko? Tace eh yace toh AI ni na rikice ne amma banason na duba littafi kinga dai nayi me digo daya da na biyu da me uku toh ita na Mata hudu sai na ga ba haka bane.
Tace toh digo daya ne da ita itama kamar ب tunda na ب a kasa ne ina kake ganin nata zai kasance yace sama? Tace kwarai kuwa.
Cigaba da rubutawa yayi yana karban shayin sa. Mika ta ga yayi tace da alamu ka gaji ko? Bari na yi maka tausa. Mikewa tayi ta ke waya ta bayanshi tana masa tausa suna Dan hiran karatu yayin da take masa tambayoyi.
Hamma tayi Dan lokacin har 11 ma yayi yace kije ki kwanta abinki nima yanzu zan kwanta. Kwanciya tayi tare da shigewa bargo. Bayan kamar minti talatin yazo ya yaye bargon ta kasa ya daura kafar ta a cinyar sa yana Mata tausa Dan yasan ta gaji da hawa da sauka ba biki Dan yasan Benin gidan su shamsiyan yawa gareshi.
Haka ya dinga karanta huruful ija'iya abinsa har ya fara gyangyadi kamin ya Mike ya kwanta a gefen ta kamar yadda sukeyi yanzu saboda fadan da suke yi.
Juyi tayi ta daura masa kafa yace toh madam ta fara.Tunowa yayi da shekaran jiya yadda tayi birgima tazo ta shige osin sa amma da safe da ta tashi ta rufe ido ta shuka masa rashin mutun ci da yace Mata ita ce ta kawo kanta wajen wai karya yake duk birgima ta bazata juya har haka ba.
Sai fita yayi ya barta yana jin wani irin mugun bukatar mace hakan yasa ba bata lokaci ya hanzar ta wajen likitan sa yace masa ya kara yi masa allurar wata allurar likitan yace zai iya yi maka illa in akayi lokacin yi bai yi ba ka dai bari ka daure kayi hakuri ka karashe sati dayan ka sai a sake maka wata in yaso wannan karan sai nayi maka yar wata 3.
Haka ya hakura ya dawo gida toh sai ya fice a harkar marakisiyya Dan yasan duk sanda ya matso kusa da ita toh Abu daya ne kawai zai wanzu.
Ajiyan zuciya ya sauke yana ganin kwana biyar din sunki su zo gashi hakurin sa ya fara karewa. Rungumeta yayi tare da rufe idanun sa har bacci ya kwashe sa baki daya bayan ya kammala addu'ar bacci guda daya da ya koya jiya.
Washe gari aka daura aure inda za'ayi dinner da daddare. Shiryawa sukayi yace tsumburbura ki dai saka wani irin kaya in kika saka farin gone amarya ma tasa fari AI sai a rasa wacece amaryar.
Tace na farko nawa baya Jan kasa kamar amaryar coci sannan kuma nasa farin ne domin shine kalar da nake so ba wai Dan shine kalan da amare suka fi sakawa ba. Kuma ni duka jiki na a rufe sannan nawa babu shape yayin da ba shamsiyan yake sabanin hakan.
Yace kuma kinyi gaskiya. Janyo hannunta yayi yasa a nashi yace tsabar kyan da kikayi ne AI yasa na fadi hakan. Murmushi tayi tace na gode yace amma me yasa kika ce idan kayan amaryar yana Jan kasa kamar amaryar coci? Ba ga dai ana son kayan mace ya ja kasa.
Tace eh tabbas ana so kayan mace ya ja kasa amma ba wai irin yanda suke dinka nasu ya bajen nan Wanda kasan kawai sai a dinka wa wani kaya dashi.
Ai kwaikwayon turawa ne wannan Wanda a ka'ida ya kamata mu Saba musu, wasu sun sani wasu basu sani ba. Yace okay I see yanzu na gane, toh zo mu tafi dai kar muyi latti.
Fita sukayi suka shige motan su tare da bawa titi kura yayin da ya bawa motar wuta. Ba abinda marakisiyya ke so kamar taga an kwashi mota da gudu hakan yasa ta dinga dariya cike da farin ciki.
Kallon ta kawai yayi ya girgiza kai kamin ya kamo hannun ta da hannunsa daya yace ko wani lokaci ki kasance cikin farinciki kinji murmushi tayi. Juya Mata gefen kumatun sa yayi ya nuna Mata da yatsa tace me yace kin gane ai. Make kafada tayi yace please yana turo baki yadda take yi. Peck tayi masa tace toh ya ranka? Yace wasai in fada miki😂
DAMA A MIKO MIN DUBUN GODIYA NAYI UPDATE BIYU KAMAR YADDA NAYI ALKAWARI SANNAN KUMA KAR KU MANTA A SUBURBUDO MIN COMMENTS 🥰
TAKU CE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
4th September,2020.
YOU ARE READING
YA JI TA MATA
Mystery / ThrillerWannan labari me suna YA JI TA MATA shine littafina na uku.... Labarin wani saurayi ne Wanda bashida aiki sai zina, a cewar sa ba laifinsa bane Allah ne yayi sa hariji. Toh hakan ne yasa iyayen sa suka rufe ido sai yayi aure amma fa an gudu ba'a tsi...