CHAPTER 41

1K 144 30
                                    

Marakisiyya tsaye a bakin drower dinta tana neman rigan baccin da zata  da zata saka Dan ba karamin gajiya tayi ba lud yace wifey wai da gaske kike bazaki sake yi min maganan ba?

Allah wasa nake miki nifa ba tsokanan ki nake ba. Sharesa tayi yace toh yanzu dai me zanyi ayafe min? Still bata kulasa ba saima since towel dinta da tayi zata zura Riga.

Yace kutma yana juya kansa gefe murmushi ne yaso ya subuce Mata tayi sauri ta juya tare da saka riganta  ajiyan zuciya ya sauke yace amma tsumburbura kinsan dai abinda kika yi yanzu ba kyau ko?

Na San da gangan kikayi Dan ki tada min hankali kuma bazaki bani ba. Daga gira tayi taci gaba da shafe shafen turaren ta ya taso yazo ya rike bakin gashinta yana wani kashe murya.

Yace haba manan tsumburbura kinsan fa wasa nake yi kuma na bada hakuri hukuncin ya isa haka ma. Sharesa tayi yasa hannu yana Mata tafiyan kulya a wuyan ta.

Bige hannunsa tayi tace banaso yace kinaso tace banaso yayinda tasa hannu ta fara masa cakulkuli.

Bude makokoro yayi tsakani da Allah yana dariya yarinda yake kokarin guduwa riko rigansa tayi tace AI baka isa ba babu wajen da zaka.

Samu yayi ya sassabe ta ya daura a gado ya fara Mata cakulkulin shima dariya itama ta fara Allah yasa ta zame saboda rigan satin da ke jikin ta.

Center table ta nufa ta janyo pop corn din da lud ya siyo wai duk Dan ya lallaba ta. Daukan pack daya tayi ta diba ta watsa masa cike da dariya ya sauko daga gadon ya biyota yace AI nasan dai bazaki iya fita ba.

Dalesa gadon tayi yare da masa gwaliyo daukan kushin din dake kan kujera ya yi ya jefeta da shi. Kara watsa masa pop corn din tayi yace lallai ma yarinyar nan kina neman magana na ne ko?

Kinsan Allah in yau na kamaki Allah yaji kanki kawai ko? Murkutsa Bali tayi yace duk sigan nan da kika shafa min sai kin lashe abin ki tas.

Tace mafarkin ka wallahi ni yau bacci ma zan......ihu tasa ganin ya daka tsalle zai rikota hakan yasa bata San sanda tayi cilli da pop corn din dake hannun ta .

Pillow itama ta dauka tace kana tabani zan Rama yace AI ba ko wace irin tabawan bace zaki iya ramawa tace haka kace yace uhm.

Tace zan baka mamaki fa. Yace hakan zai faranta min sosai ma kuwa AI ni ba abinda ke burgeni kamar mace ta bani mamaki. Marakisiyya.

Kiran sunan ta da yayi yasa sanda tsikan jikin ta ya tashi. Yace tun ranan da mahaifa na suka kawo ki gidan mu nake jin haushin ki saboda gani nake zaki kwace min duk abin da nake da shi ne.

Na kara jin haushin ki ne ganin yadda umma na ta maida hankali take kula dake ba wai bata kula da ni bane amma idona ya rufe Wanda nima bansan dalilin hakan ba. Abinda na kasa ganewa abune me saukin fahimta.

Kinsan me na kasa ganewa? Girgiza kai tayi matsowa yayi batasan yadda akayi ba sai ganin ta tayi kafafun ta sun zaunar da ita a gadon.

Haurawa yayi ya riko hannunta yace abinda na kasa ganewa shine ..... son ki nake yi. Mai sunan mama ina son ki. yana kaiwa nan ya hade bakin su waje daya.

Bayan wasu mintuna cike da dishewan murya yayi wata dariya yace yanzu wa na kama? Kuma zaki iya ramawa? Bata Dan sanda ta bude idon ta ba ta saki baki sannan a karo na farko da lud ya taba jin tayi ashar kenan.

Ta ma rasa me zata masa, pillown da ya Dade da sanin inda dare ya masa ta janyo ta jefe sa tace kai ka dauka komai wasa ? Ya zakayi wasa da irin wannan kalmar kawai sai ta fashe da kuka ta dauki bargon dake gadon ta koma kan kujera ta kwanta taci gaba da kukan ta.

Yace marakisiyya cike da wani zafi da batasan tana da shi ba ta zauna tace in ka kara kiran sunana sai na zage ka tare da fincike ribbon da ke kanta ta wulla masa.

Tare wa yayi da hannun sa yana fadin me yayi za fi kiyi hakuri ni fa ban dauka ranki zai baci ba kuma naga ke da kanki kince ba so na kike ba toh yanzu kuma menene harda kuka.

Tashi yayi ta cacumo hannunsa ta bude kofa ta hankade sa tace kar ka dake ka dawo sai na huce in ba haka ba zaka ga abinda zan ma. Bude baki yayi zaice toh ta yaya zaiyi yasan ta huce kawai ta rufe kofar yace iko sai Allah.

Toh in zanje yanzu? Yanke shawara yayi bari kawai ya tafi wajen aminin sa daya daya shekara da shekaru Wato zannurain.

Zannurain na ganinsu yace ango manya ko sati bakayi da yin aure ba shine ka mance da ni ko? Amma a da kullum sai munyi waya yanzu ko text message sau daya ka aiko min.

Cabdi bazan yarda da wannan juyin mulki irin na marakisiyya, lud yace AI nima Malkin take min dalilin da ya kawo ni ma kenan ta hada min zafi matar nan yanzu fa kora ta tayi daga gida na ni da gida na fa.

Zannurain yace ba gidan ka ba kace dai dakin ka hotel din kam AI ba naka bane. Lud yace ko ma menene ka dai gane me nake nufi ta hada min zafi buddy ya zanyi wai haka Mata suke a rikice?

Ni sauran matan tsoro na suke amma wannan ta maida ni kamar Dan maraya , kai na kare ma zance nima fa tsoronta nake ji kawai de Dan ni namiji ne yasa nake tsarewa.

Zannurain tmyace dakata mana malam kamar ya tsoranta kake ji kara min haske. Lud yace nasan bazaka yarda ba amma yarinyar nan ranan amarcin mu kaga yadda na Mata amma ko dingishi fa batayi ba.

Zannu yace kai tsaya wannan bayanin naka har yanzu da kullu sake ware min shi na tabbata ba wai a baibai na fahimta ba.

Lud yace wai kai wani irin karfa ne yarin yar nan marakis inason tafiya da ita kuma banaso.

Wani irin kallo zannu rain ke aika masa irin ina baza ka yi bayani ba sai ka kara gaba. Lud yace wai kai bazaka dauki hannu ba ?

Da na tabata noti na ke since amma Allah dazu naji tsoro kawai an gama Abu ni har ina da niyar bata hakuri ina ganin nayi mugunta wai hajiyar ka sai ce min tayi bata koshi ba.

Kusan second ashirin ba Wanda yayi magana har lud ya fara tunanin ko dai zannurain baiji me yace ba kawai zannurain ya fashe da wani mugun dariya har ya fadi😂😂 yana fadin waiyo waiyo Allah na!.

Hakan yasa lud din binshi da kallo yana nazarin kode maganar da ya fada bai dace a dinga fadawa gauraye bane tana taba musu kwakwalwa ?

KAR DAI KU MANTA WAJEN ANTAYO MIN COMMENTS DA VOTES GODIYA MARA ADADI.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

miss untichlobanty 💕

YA JI TA MATAWhere stories live. Discover now