Harara ta banka masa tace ni kaga banson neman magana in kasan bakar magana zaka dinga fadamin da can nace ka dauke ni ne ? Yace au haka ma kika ce? Tace kwarai yace AI shikenan sauke ki kuwa zanyi. Tace ka Riga kuda..... kamin ta karashe taji ta dam a kasa.
Rufe ido tayi sanda hawayen azaba ya sauko Mata kawai ta dafe gurin. Yace tashi mana uwar rash......hawayen da yaga ya sauko daga fuskarta yasa ya tsuguna yace menene? Juyar da kanta tayi ya kalli inda ta dafe daura hannunshi yayi yace nan ne ? Ture hannun nasa tayi ya ciccibe ta.
Burburwa zatayi bayan ta ya rike babu shiri ta dawo saiti. Kama hannun kofan yayi ya bankada ya shige daidai lokacin ne kuma umma ke shirin bide musu kofar.
Ganin yanayin marakisiyyan yasa a tsorace tace subhanallah me ya faru? Faduwa gabanta yayi da wani tunani ya zo Mata wani kallon kisa take aikawa lud da sauri ya daga hannu yace wallahi umma ni ban Mata komai ba kawai hannunta na rike mukayi bacci.
Cikin kuka marakisiyya take aika masa kallon da izinin wa ka rike min hannu? Tabe baki yayi yace kin manta yanzu ma na daukeki?
Ajiyan zuciya umma ta sauke ganin ba abin da take tunani bane yayinda wani bangare na zuciyar ta yayi la'asar ganin cewa bata wani canja zani tsakanin yaran nata ba.
Tace ku duba abban naku yana cikin daki yana jiran ku. Tashi lud yayi ko a jikin sa zai shige dakin daddy. Marakisiyya tace ubale kayi mantuwa fa.
Da hannu ya Mata alamun me ja manta ? Tace kayan wankin da ka jibge a Kan kujera mana. Banka Mata harara yayi ya dawo ya tallafe ta suka karasa har dakin tare da sa kai ciki.
Daddy na kallonsu ya tashi ya zauna yana murmushi yace yaran albarka kun iso? Daure fuska marakisiyya tayi tana Dan yatsine amma a haka ta daure suka gaisa da daddy.
Numfashin ta ne ya fara sauyawa ta Mike zata falla da gudu ta fada ban daki amma me? Tim ta fadi a kasa.
Amai ta kwararo daidai lokacin da umma ke shigowa tace subhanallah marakisiyya ya haka? Me ya sameki? Lud shi ya rasa ma tsayawa zaiyi ko zama?
Bayan ta gama kakare kakaren ta umma tace dauketa ka gyara Mata jiki a toilet ba musu ya dauketa dukda cewa yana jin kyankyamin suma shiga toilet ya dangwarar ta kasa ya tsuguna a gabanta yace Dan shine kika kwararawa mutane amai ko?
Hararandhi tayi tace bance maka bazanci abincin nan ba ka dage sai naci? Am allergic to green beans. Kuma baka ma fara ganin komai ba tukunna.
Ni ka wanke min jiki mu fita. Gini ya samu ya jingina a jiki yace AI Allah me rahama ne shiyasa ya baki hannu biyu yadda ya bani zaki iya gyara jikin naki.
Yake tayi masa tana shafa gemun da babu tace ya lud kasan menene? Yace me? Tace da kai malami ne zakayi bala'In haduwa saide kash....
Tunowa yayi da lokacin da sailuba tace masa in da shi malami ne da zai burge kowa sanda sukayi kwana 3 suna rigima wai so take ta maidashi Dan kauye.
Tabe baki yayi yace oya ota gyara jikin ki na fitar da ke. Tace toh ka taimaka min ka kaini bakin famfo din. Da yatsa ya Mata alamun no! no!! no!!! Sannan ya sake ninkewa ya adana ta a kirjinsa.
Fuskan abin tausayi ta saka masa sanda gaban shi ya tsinke hakan yasa ya dauke kai tare da cire rigan dake jikinsa ya wulla Mata yace shima ki wanke shi.
Haushi ne ya cika Mata zuciya batasan ta Mike ba....luuuuuu ta tafi zata fadi ya tare ta gaggawa yace ke wace irin zuciya ce da zaki tashi?
Tsaki taja tace dalla malam matsamin nayi abinda ke gaba. Kara riketa yayi gam gam hakan yasa dukan su fadawa cikin bath tube. Duka ta kaima tana fadin ka dagani banason mugunta banza,waiyo bayana nikam sunana sorry.
Janyota yayi ya rungume tayi luf a jikinsa ba mai magana... a hankali yace tsolon rake. Dagowa tayi ta kallesa yace wannan fa munafurci ne, ji yadda kika makale min a jiki amma da anyi nagana ki nuna ke zaliha baiwa ce?
Tace yanzu me ya hanaka tafoya? Fita. Yace bazan fita ba turesa tayi tace ka fita nace yace babu inda zani fa. Ture ture duka fara kawai sulbi ya kwashe su kafar marakisiyya ta bige famfo Wanda hakan yayi sanadin saukar ruwa zuwa dakin kwakwalen gami da jikin su.
Umma be tace kar de a manta muna cikin dakin fa. Wannan zancen ne yasa suka hanzarta wajen yin wanka da kaya kowa na hararan Dan uwan sa.
Suna fitowa umma ta juya fuskarta gefe ta watso musu da wasu kaya. Ba tare da ta juya ba tace kai lud ka kwashe kayanka dan haka wannan ma ka saka ne yana kayan wanki ne.
Murmushi marakisiyya tayi ganin daddy yana lekosu ta kasan bargo kama hannun lud tayi ta rike har zai kwace ta damke shi har suka fita. Yace ke uwar Mata da izinin wa kika rike min hannu? Tsaki taja ta shige dakin ta ta sauya kaya sannan ta koma.
Shima dai lud abinda ya faru kenan saide tunda ya shiga daki yake tuna yadda ta rike hannunsa. Dago hannun sa da ta rike yayi yana kalla. Murmushi yayi sannan ya fita zuwa wajen su umma.
Zaunar da marakisiyya umma tayi tace aurenki de kwananshi daya bae nace karuwa aka samu mai ya sakaki yin amai? Kwanciya tayi a jikin umma ta nuna lud da yatsa yace ni kuma?
Kallon umma tayi tace abinci me green beans ya dura min dafe kirji umma tayi tace ya kashe ki. Keda ko gani kikayi sai jikin ki yayi kaikayi?
Turo baki tayi tace sanyi ma nakeji. Umma be ta kalli lud tace maza maza dauki matar ka ku tafi kuma dama yau in ka kuskura kayi bacci ban yafe ba dole ka zauna ka kula da lafiyan matar ka, kuma yar uwarka.
Gyada kai yayi ya ciccibe ta ya dannan a mota. Yana shiga ya kama kunnenta ya murda sanda Dan kunnenta ya fadi yace ke maiya ki bani kurwata!
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
24th August,2020.
YOU ARE READING
YA JI TA MATA
Mystery / ThrillerWannan labari me suna YA JI TA MATA shine littafina na uku.... Labarin wani saurayi ne Wanda bashida aiki sai zina, a cewar sa ba laifinsa bane Allah ne yayi sa hariji. Toh hakan ne yasa iyayen sa suka rufe ido sai yayi aure amma fa an gudu ba'a tsi...