CHAPTER 42

1.1K 138 27
                                    

Kusan second ashirin ba Wanda yayi magana har lud ya fara tunanin ko dai zannurain baiji me yace ba kawai zannurain ya fashe da wani mugun dariya har ya fadi😂😂 yana fadin waiyo waiyo Allah na!.

Hakan yasa lud din binshi da kallo yana nazarin kode maganar da ya fada bai dace a dinga fadawa gauraye bane tana taba musu kwakwalwa ne ?

Lud yace kai lafiya kuwa miye haka ina magana kana dariya ko kan da kakaba ne? Goran ruwa zannurain ya janyo ya sha har yana kwarewa yace toh AI maganar taka ce ta dauke ni Sama ta ka.

Anya kuwa Kaine lud din Dana sani kut wai tsoranta kake ji. Sake fashewa da dariya yayi yayinda lud ya dafe goshi yace banason irin haka ya zan kawo ma matsalata ķa tsaya kana min dariya.

Ni in baka da shawarar da zaka bani ka ga tafiya ta ya fadi hakan yana mikewa. Zannu yace toh nasan de bakada Wanda juma zaka fadawa in ba kuma dai daddy zaka samu ba.

Lud yace kuma fa ka kawo shawara, yana shirin fita zannu yace ah lallai kanka ya dau chaji my guy yanzu sai ka Sami dad da maganar nan?

Tsaki yaja ya zauna yace kuma fa toh me zanyi yanzu? Zannu yace kawai ka fada Mata gaskiya kaga sai ta tausaya maka ko ya kace?

Lud yace Allah ya kiyaye haba ni kuma na bada gari sai kace wani sha ka tafi? Gaskiya ka Nemo wata shawarar ni din de na bata tsoron.

Shiru zannu yayi yace inada shawara amma nasan baza ma ka amince dashi ba. Lud yace menene? Zannu yace kaima abinda Mata ke yi zaka jona sahu.

Gyara zama lud yayi yace mutumi na karo min haske mana ka saka kaina a bakin leda ai. Zannu yace maganin maza zamu nema irin maganin Mata. Lud yace iye? Zannu yace eh.

........

Bayan shigan su m. Ahmad run kamin su zauna inna tace dakata gaiyan sakarkaru yan iska ba kunya ba tsoron Allah zaku wani shigo min gida na wai ku kunzo neman aure ko?

Toh ku fice, ku fice nace. Da yatsa ta nuna m. Ahmad tace kai wannan matsiyacin da gani cikin ka ne aka zubar Mata satin da ya wuce.

M. Salis yace haba hajiya me kike nufi ya zaki dinga jifan mu da bakamen kalamai, kina aibata diyar ki? Tace yo me abun aibatawa? AI gaskiya na fada ciki 5 ta zubar cikin shekara 2 shine kai kuma ka yayubo kafa zaka kwashi guntun wani ko?

M. Ahmad ne yace brother let's go! Dan ba kadan ransa ya baci da batun tsohuwar dake gabansa ba Wanda a ko wani lokaci yasan zai iya karairaya Mata kafafu in bata rufe bakin ta ba.

Fitowa sukayi har sun shiga mota m. Ahmad ya kunna zasu taci sai ga kawu musa da mando sun iso sunata haki. Mando ne ya daga musu hannu alamun su tsaya hakan yasa m Ahmad din tsayawa yayin da m. Salis ya fito.

Mando yace yaya salis kayi hakuri daga alamu nasan inna tayi muku halin ko? Ga can kawun mu yazo kuyi mahana dashi kamin ku tafi.

Murmushi m.salis yayi yace toh ina zuwa ya nufi motan a ransa yana fadin yaron nan hankali ne dashi dukda ko kauyanci na damun sa.

Lallabo m. Ahmad yayi suka zo suka gaisa a mutunce da kawu musa nan yayi musu iso cewa suke gidan sa sai su tattauna.

A mota suka shiga suka tafi inda Dan musa da mando suka shige cikin gida. Dutse Dan Musa ya jefawa hannun saratu dake dauke da kwanon manja Wanda babu shakku kayan marakisiyya zata watsa wa.

Inna ce tace iye kai shegen yaron nan banyi maka iyaka da gidan nan ba? Zaka fita ko sai na kashe ka? Haushi ne ya kama mando yace inna Allah bazai fita ba.

In ya fita toh nima zan fita miki daga gidan ki ai dan musa ma Dan gidan nan ne tunda kanwar baban sa ita ta haifi adda mabruka.

Inna tace kai kai mando wato abin naka ya kai haka? Na haifeka wannan diyar ta ta hure maka kunne? Yau har doka ta ka take? Bance na canja Mata suna ba?

Kauyan nan ko mai gari bai isa ya kirata da sunan ta ba. Janyo itace tayi zata kwada wa jummalo mando ya shiga da sauri aka samu kafadar sa ta goce.

Kuka yake abin tausayi, a baya jummalo ta goyeshi sai gidan mai gyaran targade saboda banda kawu musa bata da kowa sai mando a duniyar nan.

.......

Bangaren su m. Ahmad kuwa lafiya lafiya aka daura auren bayan sallahn Isha'I. Nan gidan kawu musan aka sauke akwatunan da suka siyo. Maman Dan Musa dadi kamar ya kashe ta Dan ita bata haifi diya mace ba.

Kawu musa kuwa ya bada auren jummala Dan yasan ko ta wahala a birnin ma yafi Mata Dan kauyen ma in an aure ta wahala zata kwasa har gara ta auri Dan waje ana sa ran ya rike amana.

Nan m. Salis ya dinga sambado godiya tare da cewa zai dinga zuwa yana duba ta bayan kwana uku uku. Kamin ya sama musu muhalli sannan ya nemin alfarma kar a mayar da ita gida.

Kawu musa yace nima ba da son raina ba barta ba kawai Dan bangaren mahaifin ta ne babu yadda na iya ne. Shima m. Ahmad ranshi yayi Dan sanyi saboda yaga irin karban da kawu musan ya musu.

Bayan sun koma gida suka ci abin ci mama na fadin kai kun Dade na dauka ma zaku dawo kamin magrib sai yanzu ashe m. Ahmad ne ya fada Mata ai aure m. Salis yayi.

Tasha mamaki sosai amma da shike basu Saba sosai ba sai tayi masa fata na gari ba tare da ta zurfafa tamabaya dukda tayi farin ciki da jin hakan yayin da take fata itama Allah ya bawa Santa lafiya.

Tace toh yaushe zakayi walima? M salis yace sai ta tare zamuyi walima. Tace toh shikenan Allah yayi albarka salis yace ameen na gode mama.

Da shike ko sanda kuka dawo gidan ma 10 na dare tayi basu yi wani hira ba kawai suka yi sallama suka shiga domin su kwanta yayin da maman ma tayi bacci lafiya lau Dan yanzu hankalin ta ya kwanta.

Bayan m. Ahmad ya rage kayan jikin sa ya janyo laptop dinsa. Kamar mara gaskiya haka m. Salis yayi tsamo tsamo tsaye a gaban madubi har de m. Ahmad yaga rayuwar tayi yawa ya dago yace brother lafiya dai ko?

Shiru m. Salis yayi ya rasa yanda zai saka maganar. Karanta sa m. Ahmad yayi yace oh karka damu na gane me kake tunani nemi waje ka zauna.

Zama m. Salis yayi m. Ahmad yace ince batun da likita ya fada maka ne? M salis yace eh. Shine ins nazarin waye zan nema ya taimaka min na dinga duba progress Dina ba tare da ya yada ni a duniya ba. Ko kuma ba tare da ya maida ni ruwa ba.

Murmushi m. Ahmad yayi yana ci gaba da computer dinsa yace karka damu kaida kake da babban yaya kamar ni AI baka da damuwa. Zo mu gani ya fadi hakan yana rufe laptop din nasa.

.......

Marakisiyya kuwa bayan ta ci kukan ta ya isheta ta koshi. Taje ta tsaya a gaban madubi tana kallon yadda idanun ta ya kumbura.

Wanka ta shiga Dan taga lokacin har Goma ta wuce bayan ta gama ne ta sake dawowa ta dawo ta zauna ta dauko wayar ta. Tana tura baki tana chatting a haka har bacci ya kwashe ta.

KAR A MANTA AYI COMMENT FA DAN ALLAH AYI COMMENT SISTERS.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU

miss untichlobanty 💕

17th September,2020.

YA JI TA MATAWhere stories live. Discover now