Wannan kalaman yasa m. Ahmad juyowa yana kallon m. Salis da ya makale shi. Tabbas ya Dan fada ba karya yayi ba. Ajiyan zuciya m. Ahmad ya sauke tare da share ma m. Salis hawaye yace shikenan toh Dan kani na na yarda.
Murmushi ne ya fadada a fuskan m. Salis din yace da gaske? Shima m. Ahmad din murmushi yayi masa tare da gyada kai yace ni matsala na da kai baka girma Abu kadan sai ka fara yin kuka rungume juna sukayi tare da fita daga area din jummalo na biye da su.
Da gudu ta rufe wajen m. Salis yace yanzu zaka siya min gurgurun? Yace a ina kika gani da yatsa ta nuna. M. Ahamd yace toh sauke hannun ba'a nuna Abu a cikin mutane kar wani ya dauka shi kika nuna ya gutsire miki yatsa.
Da sauri ta dauke hannun ta m. Salis yace ina zuwa kamin ya nufi wajen da ake sayar da abubuwa dayawa ya sayo musu apple pie, drinks tare da gurguru wato pop corn din jummalo.
M. Ahamd kuwa shiru yayi toh me ma zai ce Mata? Kawai kallon ta yake tana waite waige daga yaga zata juyo sai dauke kai. Saide a karo na uku bai yi sa'a ba domin kuwa ta kama shi dumi dumu yana kallon ta.
Hade rai tayi cikin hausan ta na fulani tace la kallo na kake? Kaga na zo binnin taraiya na kara kyau ko? Gira daya ya daga tare da ninke hannu a kirjin sa ya gyara tsayuwa yace wani kyau kike magana ? Kyan Kayan jikin ki?
Tace lallai ma Dan uwan ya salis dinnan kana nuhin kaya ya hini Kyau? Yace yanzu ko sunan nawa ma baza'a iya Kira ba ? Jummalo tace kashe min mummuna sannan na Kira sunan ka?
M. Salis da ta hango rike da ledoji yasa ta mance da zancen da suke yi taje ta karba ta fara ci a wajen. Gutsiran farko tayi ta sauke ajiyan zuciya tace kai aradu kaman kasan yunwa na bugu na.
Dariya sukayi kamin suka nufi inda m. Salis ya bar motan shi suka shiga domin tafiya su Sami makwanci.
......
Bayan dawowa su komai ya dawo normal m. Ahmad ya koma aikin sa yanzu kawai jira ake yi jummalo tayi jini uku a tsarki na hudu a daura musu aure. Saide kuma ana wata ga wata, don kuwa ana dara ga dare yayi amma kamin nan.....
(Akwai wani Abu da mutane dayawa basu fahimta daidai ba game da idda, wato shi wata 3 da aka ce AI ana nufin jini uku ne duba da cewa yawanci wata wata ake al'ada yasa wasu masu fadakarwa dunkule maganan da wata uku. Toh wasu sukan yi jini a 20 20 dan haka su a wata biyu ma suke kare idda saide ance rashin sani yafi dare duhu.... duba da cewa maza na karanta littafin ina ganin kar na zurfafa ga duk mai bukatan Karin bayani ko take da wani Abu da ya rikita ta ko yake daure Mata kai game da al'ada ko ma wani hukunci na daban ta tuntunbe ni ta numba na.)
Dalilin da yasa kuwa nace ana dara ga dare yayi hajiya mansura fa ta fara zuba ido taga ra ina ciki zai billo amma shiru shikam oga lud ya ci gaba da karatun sa tare da nuna Mata yaushe ma akayi auren da har Dan bata Sami juna biyu ba zata tada hankalinta?
A makaranta kuwa miss madeena kullum tana cikin zirya a office din m. Ahmad dukda ko tasan cewa zai yi aure ita dama ba alkhairi ya kawo ta ba. Ita dai burin ta sai ta maida shi Dan wuta ta hallaka sa ta tsoma kansa a ruwa, ita dai sai ta hallaka al'umma ta shiga cikin masu cewa Allah kayi mana kyautar masifa ko Rabin ludayi ne.
Saide Allah cikin ikon sa bata samun sa domin kuwa yayi busy sosai amma kamar maiya kai tafi maiya ma naci. Ban garen kawayen madam mansura kuwa suna nan yadda suke saide wani hanzari ba gudu ba.
Yanzu m. Salis ya fara daukan su wani course a semester din Dan haka kullum su marakis ba suda kwanciyan hankali Dan beeba ta dinga tsaki tana yatsine.
Har ta kai ta kawo indai suna da ajin m.salis toh ba sa zama waje daya Dan bata bari su riban ta da abin da ake koya musu kuma dai physics ne.
A kwana a tashi tau da gobe lud ya gama gidan su kaf sannan suka kaura. Masha Allah gidan su daidai da su kuma tsarin ginin irin na m. Salis ne saide paint da irin su kofa da window ne ya sha ban ban.
Da daddare maraki na zaune a parlour tana da CDS dayawa a gabanta tana nazarin wanne zata zaba ne ? Tafsir ok hadith kuma na wani malami? Ko kawai ta hau you tube ne ma? Ji tayi an kwantar da kai a cinyanta amma ko kallon sa bata yi ba Dan tasan inda zancen zai kare duk sanda ya fara like like da bin jiki kamar kulya.
Ganin ta shareshi yasa ya ja zirin gashinta da ke reto bige hannunshi tayi yayi dariya yace madam wai me nayi ne? Tace Maltina zan sha yace toh shine like hade rai tashi yayi ya dauko musu a fridge ta ce Kofi nan ma ya je ya kawo.
Tace zata ci kwai ya soya Mata ya kawo sanda tayi nat sai ta Mike kamar zata kitchen tayi masa gwaliyo tare da fadin ni bana sallah ma. Dariya yayi yace toh AI kinyi a banza Dan dama ni din ma ba wani Abu nake nema ba.
Ko banida ikon na kula da Mata ta sai ina neman wani Abu? Ya fada yana daga gira daya. Jikin ta ne yayi sanyi ta dawo ta zauna har ta mance ta ji caraf ya riko hannun ta yace wa na kama? Tace waiyo Allah na zata gudu yace ke wasa nake matsoraciya.
Dauko musu pop corn yayi suna ci suna kalle kallon su can yace why not gobe mu gaiyaci su umma da kawayenki da aminina suzo su saka ma gidan mu albarka? Tace hakan ma yayi amma de ni kar suzo tare da umma una so randa umma na zata zo mu kadan mu ne ta yini min.
Yace ji bakin wai umma na sai kace nata ne mutum da mamar sa a kwace masa. Tace AI nima mama na ne kuma kowa ya San da hakan. Dungure Mata kai yayi yace tafi can da wani goshin ki a wajen. Washe gari kuwa haka akayi suka gaiyaci friends din su.
Su mansura ne suka fara zuwa suka gida suka yaba domin kuwa ba almubazzaranci a ginin komai daidai misali. Suna cikin cin cup cake din da marakis tayi oga lud da aminin sa zannurain suka yi sallama lokacin mansura taje dauko musu cups da zasu sha kunun aya.
Gyara hijab dinsu suka yi. Kamin suka basu daman shigowa. Zama lud yayi a gefen marakis tace matas karde aiki suka sa min ke naga kin gaji. Zannu yace my guy basai ka tuna min banida aure ba. Mansura tace a yi zuciya toh.
Mansura ne ta shigo parlourn tana masifa wai garin wanke Kofi ruwa ya taba Mata waya. Hakan yasa bata ma lura da su lud da ke parlourn ba.
Beeba tace ke mansura kyankyaso tace a ina, marakis tace danger dago kai tayi daga wayanta ta kalli beeba ita kuma beeba da ido ta Mata alama tana kallon inda ta nuna taga lud, marakis ne ta wulla Mata hijab dinta ta saka daidai lokacin suka hada ido da zannurain.
Da sauri ta dauke kai har tana hardewa take fadin bari na karo cups. Zannu ne ya kalli lud yace Allah yayi lokaci ya kawo mu yana kallon marakis da sauri ta nuna masa lud da yatsa.
Lud yace ni bana ciki tukunna ma mune kyankyaso? Dariya suka kyalkyale da shi 😂ya matso kusa da kunnenta ta yace bashi kika ci. Kwaduwa kawai.😂
PLEASE KAR A MANTA DA YIN VOTING DA COMMENTING SAURA CHAPTER DAYA YA KARE ME DA ME KUKE SO NA RUBUTA? DUKDA DAI NA SHIRYA ME ZAN RUBUTA AMMA INA SON JIN RA'AYOYIN KU.
GA WANDA BASU YI FOLLOWING DINA BA FATAN ZAKUYI BADAN HALINA BA😉
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
FINAL CHAPTER IS LOADING........
YOU ARE READING
YA JI TA MATA
Mystery / ThrillerWannan labari me suna YA JI TA MATA shine littafina na uku.... Labarin wani saurayi ne Wanda bashida aiki sai zina, a cewar sa ba laifinsa bane Allah ne yayi sa hariji. Toh hakan ne yasa iyayen sa suka rufe ido sai yayi aure amma fa an gudu ba'a tsi...