CHAPTER 39

1.1K 136 10
                                    


Tace aure? Mando yace mun yarda muje kawai karka Sami masala jummalo taka ce fatan dai kana da bukkan da zaka sakani a ciki ko? Dan tare zamu tafi ni da ita.

Mando ya karashe zancen sa yana rike hannun jummala. Ture sa tayi tace gaji min shege yaro mai baki yaushe nace zan bika? Kasa wani Kofi a kanka wallahi bani binka.

Mando ne yace kash jummalo kiyi tunani mana, yanzu kinga in kika auri wannan kawun, inna bazata sake ganin ki ba balle ta dake ki.

Kuma kinga bazaki ji yunwa ba, kema zaki saka kayan yan binni kuma kinga zaki auri mijin da yafi samarin saratu da mairo kinga dama kullum suna cewa matsiyaci zaki aura.

Jinjina kai 🤔 tayi tace kuma fa haka ne shege mando kanina na kaina. Kai malam zan aure ka ince hikenan bazaka kama yan kauyen mu ba?

Yace shikenan ba zan kama kowa ba indai zaki aure ni. Bude musu kofar motan yayi suka shiga kamin jummalo ta shiga aka riko riganta.

Juyowa  tayi tare da daga hannu zata Mari m. Salis tana fadin kai banison iskanci fa ya zaka riko min.......tsayawa da maganan tayi ganin hannun sa a sama yana Mata kallon ni babu ruwana ba ni bane.

Wata bafulatana ce dake cika tana batsewa tace kai munafuka ina kuma zaki shiga ? Kin bige ni dubu yadda kindirmo ya bata min jiki gashi kwarya ta ta fashe shine zaki shiga akwati mai daukan mutane.

Ta karashe maganar tana cin kwalar jummalo, M. Salis ne yace ke ya haka ? Tace kai kuma waye? Yace mai motan ne kina da magana ne?

Tace la Alhaji yi hakuri , tsunawa tayi tace ina wuni tsaki yaja saboda gaba daya ta bashi haushi Dan daga gani idonta ya bude.

Dubu uku ya zaro aljihu sa ya watsa Mata yace maza tashi ki matsa wa mutane godiya tayi tace ke jummalo wai binshi zakiyi?

Kice kema kin gano kan abin m. Ahmad yace auren ta zanyi. Yana kaiwa nan ya rufe kofar ya shiga kujeranta ya zauna bayan kamar minti 2 m. Ahmad ya fito.

Da shike tinted ne motan bai lura da su jummalo dake bayan motan ba. Saida ya shiga ya kunna kenan ya daga idonsa ya kalli madubi ya hango mutum da sanda ga wani uban Zane da kwalli a fuska.

Saida gaban sa ya fadi ya waiga m. Salis yace kwantar da hankalin ka ajiya na ne. M Ahmad yace ban gane ba m. Salis yace kunna mota muje kar muyi latti zanyi maka bayani akan hanya.

.........

Lud zaune yana rubutu yayinda marakisiyya ke tattare tattare tare da hade guntun kayan sailuba waje guda. Wani drower taga kwalin whot. Dauka tayi tasa a cikin kayan ta taci gaba da aikin ta.

Lud yace tsumburbura, tace ya akayi? yace baki fada min irin mijin da kike so ba. Tace sai anjima yace amma kinyi min alkawari fa.

Tace toh naji, inason miji shiru shiru, mai nutsuwa da hankali sannan kuma ya kasance ya fire no sosai. Fuskan m. Ahmad yana murmushi ke Mata yawo hakan yasa idanun ta cikowa da kwalla.

Tace inason miji na ya fini Ilimi sosai a takaice inaso mijina ya fini komai ya kasance banida abinda zan giranta masa ma. Amma ba haka Allah ya tsara min ba. Kaifa wani irin Mata kake so?

Hannu ya mika Mata yace zo. Kamawa ta yi ta zauna a gefen sa yace um um tace me yace ni ban yar da ba. Tace baka yarda ne ba? Yace ban yarda ki zauna a nan ba.

Tace toh tsayuwa zanyi? Dan gale cinyar sa yayi ta zauna tana fadin kaide ka jiyo. Jan hancin ta yayi yace na dai San kina so. Tace a mafarkin ka.

Ta ce yanzu dai ba wannan ba zaka bani amsan da nake nema ko kuwa? Ya ce hmm inason Mata me rashin kunya, yar siririya, kuma jarababbiya, Wanda tanaso tana kaiwa kasuwa.

Amma da zaka tabo ta toh mutuwar so na take yi. Cike da kulewa tace tsokana ta kake yi ko? Yace ah ah ni na Kira suna ne? Kawai fa kwatantawa nake kema ba kin fadi naki ba?

Tashi ta yi ta ce na yi fada da kai kar ka kara min magana. Tare da shigewa toilet abinta.

.........

Su m.Ahmad kuwa cikin harshen turanci yace toh fara bayani. M salis ya hanzari masa labarin yadda ya hadu da su jummalo, m. Ahmad yace toh yanzu AI kamar kayi using dinta ne tunda dai ba wai Dan kana sonta bane.

Kuma ni banga dalilin da zaisa ka aure ta ba. M. Salis yace Ayya yi tunani mana. Yar kauye ce Wanda da alamu ana bata wahala in ta aure ni ba damunta hakan zaiyi ba tunda na tabbata ko saurayi bata da shi.

Kuma yanzu in na warke in bata so na sai na sake ta banida damuwa da hakan ai. m.Ahmad yace kuma wani gaban kayi tunani Dan matan birnin nan in suka ga anyi aure sukaji shiru ba abinda ya faru toh sai suyi maka terere.

Suna isa asibitin suka rufe su mando a mota suka ce musu su jira su zasu fito yanzu.

Koda suka shiga suka Sami likitan gaisawa sukayi kamar kullum tare da sanar da shi abin da mama ta fada musu akan batun m. Ahmad din.

Ajiyan zuciya likitan ya sauke yace toh fa wannan Abu naka yana kara sakani a duhu amma dai yanzu kuje ayi scanning sanna sati me zuwa sai ka dawo akwai wani gaji da zanyi maka.

M. Ahmad yace toh babu matsala nagode, likitan yace kar ka Sami damuwa sai kuma kanka Dan uwa salis.
Ya ake ciki ne fatan ka fara haramar neman Mata dan the earlier the better.

M. Salis yace karka damu likita AI idan ba matsala zan samu ba yanzu haka ma zamu je daurin aure na ne. M. Ahmad yace da wuri haka? Na dauka ko sati za'a Dan yi AI.

M. Salis yace um um da zafi zafi ake dukan karfe yaya na Allah kuwa insha Allah in ba'ayi yau ba toh gobe za'a yi.

Likitan yace kar ka hanzar ta haka fa kasan shi aure Abu ne dake bukatar tunani tunda da mutumin zaka karashe rayuwar ka.

M.salis yace baka da damuwa likita sai ka jini kawai wannan maganin da ka bani na kwana biyun na shanye shi. Likitan yace toh ka gwada ka gani shin ka fara rage daina son maza bawai nace kaje kayi bane fa.

Ka dai gane me nake nufi ai. M. Salis yace sosai ma kuwa muna godiya dr.

A SAMBADO MIN COMMENTS INA NAN INA JIRA.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU wato

Miss untichlobanty 💕

10th September,2020.

YA JI TA MATAWhere stories live. Discover now