CHAPTER 54

854 131 19
                                    

M. Ahmad yace ni na isa na shiga sabgata Mata da miji ? Allah ma yasa bata parlourn karban mukullin gidan yayi yayin da m. Salis ya juya tare da komawa.

Mukulli m. Ahmad yasa ya bude yaji an daka tsalle an fada jikin sa ana fadin baby oyo oyo kamin yace wani Abu ta hade bakinsu.

A cikin makokoron sa yake jin bugu zuciyan sa yayin da ya saki mukullin da ke hannun sa yayi mutuwar tsaye saide kash jummalo bata zo da sauki ba, caraf ta riko harshen sa.....

Saide haka kawai take mamakin yadda taji banbancin jilin mijin nata kamar ya Dan kara tsayi sannan kuma haka kawai taji tana so ta zauna a haka har ta mutu, wannan ne yasa ta fara tunanin ko ta fara son m. Salis din ne?

Murmushi ta tayi a wannan yanayin tana kara narkewa a jikin m. Ahmad din Wanda Allah sarki bata San shi bane. Hannun hagun tasa ta lankayo wuyan sa yayi da tayi anfani ta da hannun daman ta tasa cikin rigan shi.

Wani numfashi m. Ahmad yaja Dan shi gaba daya ya daina tunani ma da kwakwalwar sa kawai ya tsaya ne kamar gunki.

Ba abinda ke tada masa tsikan jikin sa kamar turaren da ta fesa, a yau ne ya yarda babu sarki sai Allah, a yau ne ya yarda akwai yanayin da Dan Adam ke shiga ya kasa aikata komai da jikin ya ma kasa banbanci fari da baki, ya kasa banbanci me ya faru da shi, me kuma ke faruwa da shi.

(Toh toh toh ga m. Salis nan zuwa Dan! Dan!! Dan!!! WASA NAKE HAR KUN WANI DAFE KIRJI KUNA ZAZZARE IDO😂)

sakan masa baki tayi tace I lob yu sannan ta fara kai hannun ta wajen maransa. Flash din wuta ya gani a idonsa hakan ya baisan dalilin da yasa ya dura Mata yawun sa Dan ta sake sa ba saide kashe da alamu bai yi aiki ba Dan ji yayi tace kara min.

Yasan in yayi kokarin yin tsawa ma maganar a rada zata fito hakan yasa ya yanke hukunci kawai ya since Mata idanu kila Allah ya kawo masa agaji.

Mugun nauyi hannunsa ya masa ji yake ko biro bazai iya rikewa ba amma a haka ya ja gyalen nata Wanda hakan yasa idan sa fadawa kan kirjinta da mugun sauri ya rufe ido daidai lokacin hawaye suka sauko mai kuma shima baisan na menene ba.

Mutuniyar ma tana ganin sa tasha jinin jikin ta. A second daya tana kyafta ido yakai sau 10. Baki na bari tace yyyyy...yya...ya ah..Ahmad? Bude ido yayi suna hada ido wani Abu ya soke ta.

A zuciyar sa addu'a daya yake iya yi Wanda banda ita ba abinda ya tuna

"أعوذ بكلمات الله التامة من شر ما خلق"

"a'uzu bi kalmatil lahi tâmmati min sharri ma kala'ka"

Tsoro yasa tayi saurin sakin sa ta fada daki tana daura hannu a ka shikenan ta zama yar wuta ta shiga uku!

Shima m. Ahmad din juyawa yayi ya fice da gudu sukayi karo da m. Salis wartan mukullin motar sa ya yi ya bude gate kamar mahaukaci ya kunna motar sa ya fice.

Dan ma gidan su kusa yake da tabbas babi shakka sai yayi hatsari saboda a seconds baifi biyar ba ya isa gida. A kofa ya bar motan ya bawa mai gadi mukullin kawai ya wuce.

Koda ya fada parlour sanda gaban mahaifiyar sa ya tsinke ganin yadda yake sauke numfashi ga wani gumi da ya hada yana sauri ya shige daki.

Biyo shi tayi tana Kiran sunan shi tare da tambayar sa ko lafiya? Bai ma San ta zo ba kawai zama yayi sai a lokacin ma kwakwalwar sa ta fara tunani.

Lissafi ya fara wai me ma ya kaida gidan wannan yarinyar ? Kai ya shiga uku wayar sa ya janyo tare da shiga Google yayi searching me yake nufi idan zuciya mutum yana bugawa da sauri in ya kalli wani?

Amsan da ya gani yasa idon sa fitowa kamar wani karamin yaro.

Yace abubuwan da ke janyota in kana tsoron mutum ko kana son shi? Yayin da ka fada son mutum system ma gangan jikin mutum yana sakin abinda ake Kira 'Epinephrine' da kuma 'norepinephrine' lokacin da adrenal medulla na cikin kwakwalwar sa ta saki sinadarin 'catecholamines' cikin hanyar jinin Dan Adam hakan yasa bugun zuciyar mutum ke karuwa.

YA JI TA MATAWhere stories live. Discover now