AFWAN FOR THE TYPING ERRORSWanka ta shiga Dan taga lokacin har Goma ta wuce bayan ta gama ne ta sake dawowa ta dawo ta zauna ta dauko wayar ta. Tana tura baki tana chatting a haka har bacci ya kwashe ta.
Bata ji shigowan lud ba domin kuwa da sanda ya shigo Dan baisan me zai tarar ba ajiyan zuciya yayi ganin tayi bacci yaje yayi wanka abin sa.
Har yazo zai kwanta ya ji kamar tana magana haka yasa ya Dan kafo kunnan sa. Tsaki taja cikin magagin bacci tace dan rainin hankali kawai ka dauka ana yin wasa da feelings din mutum ne? Banza, shashasha, dan Iska , mugu na tsane ka.
Nasan da m. Ahmad Dina ne da bazai yi min haka ba da zai.... Damian hannun ta lud yayi hakan yasa ta bude idonta tana mai furta m. Ahmad? Yayin da murmushi ke dauke a labban ta.
Yace shhhhh in muna tare karki kara kiran sunan wani namiji, tace mene?yace na fada miki in kika kara zan hukun ta ki.
Tace kawai Dan nace m.ahmad? Pecking dinta yayi tace m. Ahmad fa nace toh menene a ciki ? Ya sake pecking dinta tace m. Ahmad malami na ne fa.
Jinjina kai yayi yace da alamu wannan bazai yi aiki ba tare da janyo bargo tace me kake nufi? Yace me kuwa nake nufi.
Harara ta aika masa tace nayi maka kama da yar tsana ne ? Kawai Dan kanaso ka kamani shine zaka ce kana so na kuma ka fashe da dariya ? Ance maka ana wasa da kalmar so ne?
Yace ayi min hakuri mana tsumburbura! Make kafada tayi yace Dan Allah fa kinji tsayawa yayi da maganar da yake yace wai al'ada kike yi? Tace me kaji ? Yace kamar pad nake ji a jikin ki kuma last week ma naga kin saka. Tace uhmm.... na... na .. ina ruwan ka ne ma?
Yace da ruwa na mana ko kin manta ni mijinki ne? Tace uhm sannu sai yanzu kasan kai miji na ne ko? Sannun ka. Yace ko ki fada min ko na hadaki da umma.
Tace wai mu yara ne duk abin da ya faru tsakanin mu sai kace zaka fadawa umma? Yace ji bakin ta sai kace ba kece mai wannan halin ba.
Ni banda yau yaushe na taba cewa zan hadaki da umma? Cikin borin kunya tace naji dai ko ma menene ni bazan fada ba. Yace sai kin fada min tace anki din yace wallahi in baki fada ba gobe bazan siya miki breakfast ba.
Tace ina da sadaki na a account yace haka kika ce ko toh sai kin fada min ko kin ki ko kin so. Cikin kulewa tace wai ina ruwanka da ni ne kaji min kai toh ko umma batasan ina fitsarin kwance ba shine zan fada maka a matsayin ka na wa? Ji min mutum fa.
Jin shiru bai amsa ta yayin da ya saki baki yana binta da kallo yasa ta nazari, dafe bakin ta tayi tana dungure kanta tace me yasa? Marakisiyya me yasa bakida control ne? Toh kin fada masa kin huta.
Gado ta koma ta kwanta kusan minti Goma taji lud ya zauna a gefen ta Dan a tunanin sa tayi bacci ne. Rike hannun ta ya yi zuciyar sa tayi nauyi a hankali yace Anya kuwa zan iya zama miji na gari? Ace muna neman kusan sati 4 da yin aure amma ban taba sanin matata tana fitsarin kwance ba?
Kila ba shi daya ne matsalar ta ba ma. Me zan cewa mahalicci na? Yaya zanyi oh Allah ka dafa min ka gani ina kokari na kar ka tuhume ni akan kuskura na ya Allah.
Har tausayi ya bawa marakisiyya da taji ya daura kansa a kafadar ta daga gani daurewa yake bayason yayi kuka. Haka ya dinga maimata umma ki yafe min na kasa rike amana, na kasa, na kasa a haka har bacci ya kwashe sa.
..........
M. Salis tsaye yayin da m. Ahmad ma ke tsaye kowa na kallon kowa. Toh me ma zasuyi ne? In ma zasuyi wani abun wa zai fara motsi ? M. Ahmad na gudun kar a Sami matsala ya cutar da m. Salis yayinda m. Salis din ke gudun kar ya janyo m. Ahmad din ya fada ruwa.
A ajiyan zuciya suka sauke kamar Wanda akace su kashe juna kuna sai suka saki dariya. M. Ahmad ne ya dara takowa wa Wanda yasa m. Salis din nutsuwa yana kokarin karanta kansa yaji yadda jikin sa zaiyi reacting.
Abinda bai sani ba shine lokacin nan da m. Ahmad yace zai karbi sako maganin kashe bukata ya siya duba da yadda yaga hankalin mahaifiyar sa bai kwanta ba bayaso ya bata kunya.
Toh bayan jawabin da likita ta musu kawai sai ya watsa guda 2 maimakon daya kamar yadda ya Saba. Ko da m. Salis yaga fa tsakanin sa da m. Ahmad din baifi taku uku ba sosai ya tsorata kar ace treatment din da ake masa baiyi ba hakan yasa yayi tsamo tsamo kamar beran da ya fada cikin kunu.
Dukda cewa kuwa ba wannan bane karo na farko da suka sha taba jikin juna amma wannan yasha banban saboda tunanin dake zuciyar mutum ne.
Yadda zakaji a yayin da kayi karo da dayan jinin halitta a kasuwa ba abinda zakaji illa dayan biyu ya faru ko ka bada hakuri kaima a baka, ko kuma cece kuce ta kaure Wanda ke haddasa dambe.
Amma yadda Dan Adam zaiji a yayin da dayan sashin ya tabasa koda kuwa hannu ne inde har yasan ba hatsari bane toh dayan biyu shima zai haddasa. Ko wannan mutumin yaji bukata da kaunar dayan sashin ko kuma yaji bakin ciki da kuma tsana.
Yanzu dai kubar wannan maganar tunda ni ba malamar psychology bace kamar de yadda nake cewa,M. Ahmad Jin babu wani sauyi a jikin sa yasa ya kama hannu m. Salis din yayinda yake iya kokarin sa wajen ganin ya kalli cikin idanun sa domin wannan gaji ne ba boye boye.
Dan haka duk abin da zai motsa shi dole su gwada daga nan ne za'asan me za'ayi. Saboda idan bare ya tashi motsa shin ba kunya zaiji ba kar aje sai ya dauka ya warke yaga da sauran zance.
Hannu m. Ahmad yasa ya dago da fuskar m. Salis din kamar zai sumbace shi yana karanta fuskan sa. Ganin ba canjin yanayi yasa ya daura labban sa a nasa ba tare da ya motsa su ko wani Abu ba.
Jin m. Salis din ya Dan matse hannun m. Ahmad din yasa m. Ahmad din sakin sa yace a gani na ka fara samun progress amma me zaka iya cewa kai?
Bude fridge m. Salis yayi da sauri ya dauko ruwa ya kwankwade tare da sauke ajiyan zuciya kamin ya zauna. Yace brother kallon shi m. Ahmad yayi yace ya akayi ka iya romance ne kut? Dafe kai m. Ahmad yayi Dan shi a tunanin sa wata tambaya me muhimmanci m. Salis din zai yi duba da yanayin da ake ciki.
M. Ahmad yace me yasa kayi tambayar nan? M. Salis yace tunda nake ba'a taba min kiss da naji kauna a cikin sa ba wai bukatuwa ba sai yau.
😳UHM! UHM! NI BAZANCE KOMAI BA DAN LAMARIN YAFI KARFI NA.
DON ALLAH ACI GABA DA COMMENTS DA VOTES DAN HAKAN NA KARA MIN KWARIN GUIWA SOSAI.
GODIYA NAKE MASOYA NA. TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
YAUWA NA MANTA BA SAI KUNCE MIN HAPPY BIRTHDAY BA KAWAI KU SAMBADA MIN ADDU'O'I ZAFAFA ZUWA GA MAHALICCI NA ZANYI FARIN CIKI DA HAKAN.
A BLESSED SWEET SIXTEEN TO ME ALHAMDULILLAH!
Miss untichlobanty 💕
18th September,2020
YOU ARE READING
YA JI TA MATA
Mystery / ThrillerWannan labari me suna YA JI TA MATA shine littafina na uku.... Labarin wani saurayi ne Wanda bashida aiki sai zina, a cewar sa ba laifinsa bane Allah ne yayi sa hariji. Toh hakan ne yasa iyayen sa suka rufe ido sai yayi aure amma fa an gudu ba'a tsi...