CHAPTER 48

900 105 13
                                    

Ajiyan zuciya lud ya yi yace my guy, naji kamshin gaskiya a maganar ka Allah ya gani yau zanje na fada ma marakisiyya gaskiya komai ta fanjama fanjam ta tausaya min ta daga min kafa.

Shiru zannu yayi lud yace ko ya kace? Zannu yace ai na yarda dakai banaso ince ma ka tafi yanzu kaga kamar ina koran ka ne.

......

Da sallamar sa ya shigo firgigit marakisiyya ta Mike tare da nufi sa tana mai haki tace haba ya lud yau kusan kwana nawa ban sa ka a ido na ba kuma dai nasan kana dawowa dakin nan.

Dan ko wani lokaci zanyi kamshin in na tashi daga bacci kuma ina kallon kayan ka na wanki da kake canjawa. Wani abin na maka? Dana Allah nayi ma laifi ne kake gudu na?

Wuri ya samu ya zauna yayi Mata nuni da ta zauna a gefen sa. Bayan ta zauna ne ya sauke ajiyan zuciya yace mata... a kwai wani Abu da ke damuna ne akan ki amma bansan yadda zan fada miki ba.

Gaban ta ne yayi mugun faduwa karfa yace su rabu ko wani abun. Da ido ta kalleshi hakan yasa ya kalli carpet din dake kasa yace gaskiya marakisiyya nayi iya jurewa ta amma yanzu ina ganin bazan iya zama da ke ba akar my cutar da juna.

Hawaye ne ya tsilalo Mata yayin da kirjin ta ke dukan lissafin da itama bata sani ba. Inda za'a daura microphone kai ka dauka ganga ake buga wa.

Baki na bari ta ma rasa ta ina zata fara tace me nayi? Dan Allah me nayi ne wai me na maka Allah zan dena ko menene. Yace ba abin da kika yi ki dena kuka kawai de ina ganin yanayin halittar da Allah yayi mana ne ba daya ba.

Tace wanne a ciki? Halittar haihuwa ko ke inde wannan ne saurin me kake AI zamu haihu ko kaji nace banason haihuwa ne? Wani numfashi ta ja tace kar de kace min baka son haihuwa?!

Da hannu ya gwada Mata me yake nufi tayi shiru tana ji kamar ta rufeshi da duka. Kirjinsa ta fara duka da kafadar sa tana fadin yanzu akan wannan shine har kake cewa mu rabu? Idan ban isheka bane toh ka kara aure mana nace zan hana ka ne?

Yace kimin yawa ne Allah ya gani kinci karfi na kiyi hakuri. Dan hankade sa tayi tace kai banfi ba banza ni fa na dauka nayi ma kadan shine nasha magani. Yace magani kika sha? Nima magani nasha toh ai.

Tace toh me anfanin shan mu dena mana yace da gaske magani kika sha ? Tace sosai yace Allah yar iska shine kika barni nake ta zillewa ? Yanzu nasan akwai maganin a jikin ki dan haka nima van na sha sai mu warke tare.

Tace an gama bude fridge ka dauko glass jug dinnan bari in dauko maganin hada mai tayi yana sha yana rangaji da kai tana bashi labari kamar basu suka gama zama abin tausayi ba.
Bayan ya gama ne suka wanke jug din sannan suka shiga wanka.

........

M. Salis fa sauki ya samu kuma cikin sati biyu kacal ya samu wani gida 2 bedroom sake fenti kawai yayi ya canja kofa da window sai Dan gyare guare da baza'a rasa ba.

Ya zuba kayan daki a dakunan saboda ya rage wa iyayen nata nauyi. Ko kawota da akayi daga ummu Dan musa sai kawarta ne suka kawota va tashin hankali ba kawaye ba komai.

Toh wa zaije ma ita da wasu ke Ma ta ganin maiya? Su saratu ma ko ta kanta basu bi ba kura ta mutu suyi wasa ne. AI kuwa gidan ta fes da shi ya hadu sai godiyan Allah.

Nan suka yini, mutumin mu mando ma anyi masa dakin sa daban ta waje ba a cikin inda nasu yake ba sai dining table dake gefen parlourn. Shi da Dan musa dadi kamar ya kashe su shima Dan musa dagewa yake wai anan zai zauna.

Maman sa ne tace toh yanzu banda abinka Dan musa in ka tafi wa zai kula min da dabbobi na? Kuma yanzu sai ka barni ni kadai inyita jimami?kadai to hakuri kazo muje sai ka dinga kawo masa ziyara duk Rana da ka shigo binni.

Yace toh ya yarda da wannan din nan dai aka samu suka mance suka fita kofar gida suna ta kalle kalle kamin suka gangara karshen layi ganin magarib zatayi yasa suka dawo tunda ba sanin gari sukayi ba.

Saboda ba yau su ummu musa zasu Kwana ba yasa suka yi shawaran zasu kwana a dakin jummalo ita kuma sai a kadata zuwa na m. Salis din ko ba komai sunyi Mata dubara domin fa sunsan kan mutuniyar tasu a toshe yake.

Ita dai ta San ba kyau iskanci amma fa batasan me ke wakana ba da sun dauko zance zasu yi Mata huduba sai ta toshe kunne tace batason jin batsa. Haka suka barta kila mijin nata zakisan yadda zai shawo kanta.
......

Saboda babu tazara daga gidan su m. Ahmad zuwa gidan m. Salis din yasa suka taho a kafa. M. Ahmad yace toh ya dayan gidan da kake ciki?

M.salis yace AI na sayar da giyan dama ciki da parlour ne kawai na siya nake zaune abina shine ba sayar na sayar da mota na ma na siya Camry hybrid.

M.ahamd yace okay ashe da kudin ka hada ka siya kenan ranan muna cikin maganan aka Kira sallah bamu karashe ba. Yaushe zai iso? Yace jibi ma nake ganin zaizo.

M. Ahmad yace toh AI hakan yayi kyau Allah ya sanya ALKHAIRI ga sabon mota, sabuwar amarya, sabuwar gida kuma sabuwar rayuwa. Dariya m.salis din yayi yace gaskiya fa sabuwar rayuwa Allah ka tsare duk musulmi daga fadawa matsalar da muka shiga.

M.ahamd yace ameen m.salis yace wallahi gaba na faduwa yake har tsoro nake ji kasan ban Saba ba. A rayuwar baya ni zuwa ake waje na nine karamin nine a gurbin maven yanzu kuma nine namijin gidan cabdi.

M. Ahmad yace karka tsorata zaka iya ka dauketa kamar kanwar ka ne zaka iya kula da ita. Jinjina kai m.salis ya yi yace haka ne kam zanyi. Rike hannun sa m. Ahmad yayi.

M. Salis din ya dago yana kallon m.ahmad din da a da ne da zai rungume sa ne amma saboda m. Ahmad din ya hanasa yace masa ya zama namiji yasa yayi shiru.

Murmushin gefen baki m.ahmad din yayi saboda yasan menen a ran m. Salis din hakan yasa ya janyo sa jikin sa yace cry cry ango kawai yana shafa kansa. Dariya sukayi kamin suka ci gaba da tafiya.

Da sallamar su suka shigo BILKISU kawar maman Dan musa ne tayi musu iso kamin ta shiga ciki ta sanar da su jummalo. Fitowa sukayi da ita suka zauna m. Ahmad ne ya fara magana da innalhamdu lillah. Gaban ta ne ya fadi da ras.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

27th September,2020.

YA JI TA MATAWhere stories live. Discover now