CHAPTER 60 (FINAL)

1.1K 105 28
                                    

Lud yace ni bana ciki tukunna ma mune kyankyaso? Dariya suka kyalkyale da shi 😂ya matso kusa da kunnenta ta yace bashi kika ci. Kwaduwa kawai.😂

Zuba kunin ayan sukayi zasu sha saide marakisiyya na kawo shi kusa da bakin ta ta fara makakin amai nan zannu yace my guy what's up ban gane ba. Lud yace nima ban gane ba tana kallon marakis daga hannu tayi sama tace kaina a cikin bakin leda a bakin tsumma a kasan gado. Mansura tace za ma ki since.

Nan suka tattara kowa ya watse su lud suka tafi asubiti tsabar a zarbabi daga mamakin amai😂

.......

Bayan wani Dan lokaci jummalo ta kammala iddan ta Dan haka m. Salis yace Mata za'a saka ranan sabon auren ta. Cike da murna tace da gaske sake aure na zakayi? Na dauka laihi nayi ai.

Murmushi yayi yace a ah ba sake auren ki zanyi ba ina dai son in tamabaya ki in kian so na zama waliyin ki ne. Tashi tayi ta shige dakin ta tare da cewa in de ba gidan ka zan koma ba ni bani so aradu bani auren kowa.

Mama dake zaune a parlourn ne tace au kainsalisu dam abaku taba yin maganar da ita ba sai yau? Kai haka ake ka saki mace ko dalilin ma baza ka fada Mata ba? Ko Dan kaga bata wayo shine kuka miyar da ita tamaula wanna ya buga ya bawa wannan?

Yace mama ba haka bane kawai ban Sami lokaci bane shiyasa tace toh AI shikenan nide na cire hannuna amma kar ka kuskura ta kawo karar ka waje na tace ka Mata dole ku lallaba ta kusan yadda zakuyi ku shawo kanta ko ku canja shawara.

Daga nan ya tashi ya shige dakin m. Ahmad. A kan gado ya same sa kamar kullum yana aiki da computer dinshi sallama yayi masa kamin ya shiga ya zauna. M.ahmad yace ya kuka yi da ita? M. Salis ya gyara hulan sa tare da fadin tace nan da kwana uku take so a daura amma kar kowa ya Mata zancen wai kunyar mama take ji.

Murmushi m. Ahmad yayi yace ja'ira daga baya kenan kamar ba ita bane ranan da kace ta dawo gidan mama ta makale maka wai a gidan ka zata zauna. Dan zun kudawa yayi yace amma tsaya idan har ta makale maka ranan AI yana nufin bata so ku rabu kenan.

M. Salis yake yayi yace haba dai ta dauka guduwa nima zanyi shiyasa wai ita me wayo ta makale min. Haka dai duk sanda m. Ahmad ya kawo kokonto sai m. Salis ya kafta masa karya.

.....

Bayan kwana daya da zuwan su lud asibiti aja ce suzo result ya fito da murna suka shiga office din likitan saide yadda suka ga fuskan shi yasa jikin su yin sanyi.

Bayan sun gaisa yace look nasan ku musulmai ne kuma kuna da tawakkali ba zan tsaya yi muku boye boye ba in nayi haka na cuce ku ku sani abin da zan fada cikin ikon Allah a samu canji amma gaskiyan lamari matarka bazata taba iya haihuwa ba idan ko aka dage ko ta samu cikin ma mutuwa ce!😳😟🥺😭

......

A kwana a tashi a kwana a tashi har Rana na uku ya zo mama ma bata San da auren ba sai daren washe gari take cewa Anya babu wani Abu a kasa kuwa me na gaggawa. Ni gaskiya ban yarda da ku ba bari na tambayo ta.

Koda taje domin ta tambayi jummalo ta Riga da tayi bacci hakan yasa ta kalleta Dan da ta tashe ta ma surutai take Mata ta fillanci. Haka dai tace toh zata sanar da jama'a Wanda zasu samu halar ta gobe.

Wajen karfe 8 na safe bayan jummalo ta ci abinci ta koma bacci abinta bayan ta tashi ma bata fito ba Dan an siya Mata waya an Dan koya Mata tana can tana buga game abinda tafi koya kenan😂 tunda ba wai tayi boko bane balle tayi su chatting.

Guda da ra ji ana yi yasa ta fito Dan ganin me ya faru Dan ta dauka ihu ne. Ta na fitowa taji manyan Mata sun damko ta ana fadin ga amar yar nan ma da ake fadin a damko mana ita.

Bude baki tayi zata tambayi me ake nufi aka danna Mata wasu gumba wai taci da kyar ta hadiye daga zatayi magana sai a dura Mata wani Abu ko ace kar ta damu AI ansan tana Jin kunya.

YA JI TA MATAWhere stories live. Discover now