CHAPTER 38

1.1K 140 30
                                    

Umma dake cikin waya tana zabga hello tana jin haka ta Rifa wa kanta asiri Salinas alin ta kashe wayan ta. Daddy ko bai ma San shayin sa yake hadawa ya cika har yana zuba sai umma ne tace Alhaji ruwan zafi.

Yace aw bismillah tare da matsar da kafan sa da sauri. Goge wa umma tayi yayinda ya sauke ajiyan zuciya.

Umma tace menene? Yace kede Allah ya bawa yaran nan zaman lafiya kawai tace toh ameen.

.......

M. Ahmad tsaye a gaban madubi yana gyara link din rigan sa yayinda m. Salis ke gyara zaman hulansa.

Matsowa m. Salis din yayi ya dafa m. Ahmad din yace karka damu brother komai zai zama normal. Insha Allah zasu gano matsalar da kuma allurar da akayi maka.

Gyada kai kawai m. Ahmad ya yi ya ce Allah ya sa. M.salis ya ce ameen dai muje ko?

Fita sukayi suka gaisa da umma tace muje kuci abin ci. M. Ahmad yace bari mu dawo dai kar muyi latti ko? M. Salis yace mu dai cin kaga mama ta dafa mana baza ta ji dadi ba.

Mama tace ah ah ba komai kuje ku dawo din ba matsala. M. Ahmad yace bari mu cin kawai. Shiru umma tayi abin bai zauna Mata ba.

Sanda tace suci yace a ah daga saka bakin m. Salis sai ya amince. Isti'aza tayi tare da kyautata masa zato  tace toh muje din.

Zama sukayi suka fara ci bayan sun zuba mama tace salisu. Dagowa yayi yace na'am mama. Tace nikam in tambaye ka mana.

Yace toh mama. Tace nikam ya akayi kuka hadu da amadu ne? Yace a wajen aiki ne muka fara haduwa. An saka paper dinsa a cikin nawa sai na nemeka na basa daga nan muka yi sallah shikenan.

Tace Ayya allah ya kara taimako. Wannan AI sai ka bani lambar mahaifiyar ka muma mu kulla anita kila ma yafi naku.

Ajiye Conklin dake hannunsa yayi yace Allah yayi ma iyaye na rasuwa suka barmu daga ni sai kanwata. Mama tace subhanallah Allah yayi musu rahama yasa aljanna ce makomar su.

Toh ina kanwar taka take ko tayi aure ne? Yake yayi yace Allah ya Mata rasuwa AI ita ma. Umma tace innalillah wa inna ilaihi raji'un kaga rayuwa Allah ya gafar ta musu baki dayi.

Suka amsa da ameen tace kai amma wannan Abu baiui dadi ba saide ka kara hakuri. Shin wai jinya tayi ne? Ko haka kawai ta rasu.

M. Ahmad ne ya Mike yace toh mama gara mu tafi Dan naga har lokacin appointment din namu ya kusa. Yana kaiwa nan yaja hannun m. Salis suka fice.

Suna fita m. Salis ya rungume m.Ahmad din yace na gode yaya na. Yayinda ya ke goge kwalla da ta taru masa. M. Ahmad yace amma you have to man up fa kaga yanzu zaka koma namiji ne aure zakayi kar ka dinga yin Abu kamar mace.

Ko baka so ka canja ne? Dariya me kuka yayi yace inaso mana kasan abin ne ya bi jini na amma zan dinga kulawa nima in dinga tsarewa irinka babban yaya na.

M. Ahmad yace yauwa Dan kani na ban musha tafawa sukayi kamin suka shige suka tafi. A hanya suna cikin tafiya m. Ahmad yace ina zuwa bari na karbi Abu a shagon nan. Ya fita ya bar m. Salis a mota.

M. Salis na zaune yana yan nazarin sa kawai ya ji an doke madubin dake gefen da mugun karfi. Subhanallah yace tare da fitowa Dan yaga me ke faruwa. Yar fillon dake falla gudu tana mando ka saya  ko inshi ub*nka wollohi kasan banida mutunshi ko kadan AI ko?

Damko ta yayi yace ke zuciya bakiga me kika yi bane motar mu fa kika lalata tace dalla shan malam sake ni na kamo Dan iskan shan ya kama ya tsinka mun takalmi na.

M. Salis yace aiko nima zan tsinka miki Mari ne ji fitsararriya kawai. Mando dake gudu yaga jummala yayar sa ta daina biyosa yasa ya juya ya fara dawowa ganinta tsaye da wani a jikin mota yasa yace Allahu AKBAR kashe de wahalar mu ya kare jummalo zata auri Dan binni.

Dama tayi min alkawari da ni zata tafi ko ina su inna saide a mutu wallahi. Jummala na kam tayi goshi.

Jummala kuma da ta ke hura hanci fuskan nan an Zane sa da kwalli tace wai malam me kake bukata ne ince wannan Karfen na daka da sanda kuma naga ba da gangan nayi ba.

Yanzu dai ga murtala 4 anjima my hadu a karkashin bishiyar tsamiya dake dumma zan cika maka murtala daya da yobe.

Baki ma ya saka yana kallon ikon Allah yace ke wai shekarunki nawa ne? Tace 15 gareni kana da matsala ne yace kinsan me kika bata kuwa? Yace toh mecece na bata ni wannan abin naku na yan birni wai mecece ma naga sai tafiya suke a kwalta.

Kode yayan akwati mai daukan mutane ne? Yace menene kuma wannan tace la bakasan akwati mai daukan mutane ba AI hi ke kawo mutane binni kuma sau daya yake shigowa kauyen mu.

Kaga ..... daga Mata hannu yayi yace ke rufe min baki toh wannan da kike gani akwati me daukan mutane ne Wanda daga sama ta daya yake kuma shine kika cire masa idanu. Tace toh toh ni duk ka wani hade rai ba na biyaka nace kaje ayi ma walda ba? Yanzu haka sai anyi min duka na kudin da zan bakan ma.

Yace ance miki murtala 7 da Goma ko mai da zaisa motar nan tayi tafiya zai iya siya ne? Tace toh nawa ne yace ki kawo dubu 150 na yafe miki sauran tunda har fenti ma kika bata min.

Tace murtala nawa kenan? Yace AI bazata kirgu a murtala ba saide in fada miki a yobe. Yace toh gobe nawa ne indai baifi yobe Goma ba zan bayar yace yobe dubu uku ne CAS ba dadi ba Kari.

Tace tashin hankali AI ko duka yan kauyen mu zaka siyar baza mu kai kudin nan ba ni har kaina ya fara ciwo tsabar yadda lissafin yayi min nauyi.

Mando ne yace jummala kin ja wa kanki yobe 3,000? Kawai ki shirya mutuwar ki ta zo wallahi.

Kuka ta fara m. Salis yace kyayi kukan ki gama ni dai a bani kudi na. Tace haba baba na ka tausaya kaga mu daga ruga muke wallahi yau ne karo na farko da na fara biyo mando na shigo binni yanzu haka ba'a sani a gida ba an dauka ina kasuwa ina talla.

Allah inna bata da imani ko kadan bata tausaya min banyi komai ba ma duka na take ka yafe min don Allah kaji?

Mando ma abin tausayi yayi yace ka tausaya baban mu ka yafe wa jummalo inna ta ba imani ne da ita ba haka saratu da mairo ma azzalumai ne ni kadai ke son jummalo.

M.salis yace zan yafe amma da sharadi tace fadesi kawai ba bata lokaci zan amince yace in zaki aure ni toh zan yafe muku in kaiki gida ma a motar mu daga nan na auro ki.

Tace aure? Mando yace mun yarda muje kawai karka Sami masala jummalo taka ce fatan dai kana da bokan da zaka sakani a ciki ko? Dan tare zamu tafi ni da ita.

DAN ALLAH KAR KUYI KASA AGUIWA WAJEN SUBURBUDO MIN COMMENTS.  ALLAH YA BAR KAUNA.❤

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

YA JI TA MATAWhere stories live. Discover now