CHAPTER 40

1.1K 125 22
                                    

M.salis yace baka da damuwa likita sai ka jini kawai wannan maganin da ka bani na kwana biyun na shanye shi. Likitan yace toh ka gwada ka gani shin ka fara rage daina son maza bawai nace kaje kayi bane fa.

Ka dai gane me nake nufi ai. M. Salis yace sosai ma kuwa muna godiya dr.

Direct zuwa sukayi aka fara waje wajen da akace za'ayi a kwakwalwar m. Ahmad din sai kusan bayan awa biyu tukunna suka fito lokacin jummalo an Sami lungu an makale yunwa na kwakularta.

Taimakon su daya mando yana da wani madara wacce ba'a dafa ba da ya ajiye a karka ita ce suka sha suka Dan tokare.

Mando ne ya fara hangosu yace jummalo sun hito waiyo na dauka mutuwa zamuyi cikin kwalin nan aradu.

Dafe kai m. Salis ya yi yace kash wallahi duk na mance da cewa mun bar mutane a mota. Shiga sukayi m. Salis yace jummalo ya haka? Bakida lafiya ne?

Cikin rashin kuzari ta kalli gefe tace yo ina naga lafiya? Cutar da tafi ko wacce ta kamani kallon juna m. Salis da m. Ahmad sukayi Dan a tunaninsu son m. Salis take nufi.

Mando ne yace ni ban gane ba tace kai banza yunwa nake nuhi ni yanzu banida karfin yin surutu dayawa ma.

Bayan su an siya musu abin ci da kaya suka canja a changing room na super market din set 4 aka kara musu Wanda zasu rike na kamin m. Salis ya samu akwati mai set 3 ya cike su da kaya makil masu daukan ido domin a shirye yake ya rikita tunanin jama'ar kauyen su jummalo.

.......

Tun da suka shiga garin kallo ya dawo kansu abin har ya fara jugular da m. Ahmad saboda ba abinda ya tsana irin abin nan kila yana daya daga cikin dalilin da yasa baya son matan ma.

Tsaki yaja a karo na takwas m. Salis yace ya dai m. Ahmad cikin turanci yace ba komai.
Kawai de yan kauyen nan basu kyautamin a rai bane Sam ko kadan ni ban wani ga dalilin da zaisa ka auri yarinyar nan ba.

M. Salis yace baza dai ka gane ba kaide muje kawai. Mando ne yayi musu NUNI har gida in ka Ganshi zaka rantse ba shi bane ya sha gezna ga hulan nan ta zauna masa tsam sai ka dauka ajebo ne dukda bashida kiba.

Itama dai jummalan haka ta kasan ce a nata bangaren bubun da ta saka yar kanti yayi Mata kyau sai kallon kanta takeyi a madubi.

Daidai kwantar gidan su mando ya hango abokin sa yace kai Dan musa ! Dan Musa! M. Ahmad yace kai mandu kake ko wa ka nutsu ,ba haka ake yi a birni ba.

Rashin tarbiyya ne da kauyanci in kaga mutum a mota ka dinga kwala masa Kira in ka daga hannu ma ya wadatar.
Ka rage yawan surutu da rawan kai haja ba komai ka gani gane sai kayi magana ko da kuwa wannan ne Karo na farko da ka fara ganin abin.

Jummalo tace ba shakka shiyasa bakuda hayaniya. AI kuwa daga yanzu idan ba ce min akayi nayi magana ba bazan sake yi ba.

M. Ahmad yace yayi kyau haka akeson ganin mace da kamun kai ba wai kiyi ta rawan kai ba. A ranta tace rawan kai? Kenan yanzu dole kaina ya daina rawa?

Kai yan birni ba dai abin mamaki ba kila shiyasa matan binni zaka gansu kamar agwagi. Waiyo na shiga uku na.

Kofar gidan su aka tsaya suka bide kofar suka fito lafiya lau kai kace ba yan kauye bane. Murmushi m. Ahmad yayi ganin suna da saurin koyan Abu kamin ya tabe baki duba da cewa ba wani girma sukayi ba.

So ba abin mamaki bane domin akan canja yaro fiye da babba ba tare da ansha wahala ba.

Mando ne yayi sallama domin yayi musu iso amma kamin ya gama inna tace kai Dan kaniya ina wannan tsinanniyar ka ganta?

Ko da gasken ne hankali take tafiya in an aika ta kiwon wato yau abin ya girmama shine har ana sallar dare bata dawo ba ko?

Washe baki mando yayi zai sabarbado zance sai ya tuna da me m. Ahmad ya fada masa hakan yasa ya wani gyara hanun Riga harda gyaran murya.

Yace abin ya girmama kuwa sosai amma dai bazaki gane ba. Yanzu dai muna da baki ko nace yayu na zaki ashe su ko na kaisu gidan kawu musa?

Tace su waye ne yace zaki gansu ai. Saratu tace eh eh eh kai mando dakata harka shi tayi da tocila tace laa ba dai idon nawa bane irin kayan da yan birni ke sawa ne a jikin ka da fari na dauka bokati ne a kanka.

Kace la tara kudi har ka siya kaya me tsada. Inna tace kuma fa sanda kika fada na gani yo Dan bakin ciki sai ya mutu da na tun yana shekara 10 yake saka kayan yan birni in ya girma a binnin zashi zauna.

Tabe baki mando yayi Dan baya jituwa ko kadan da saratun saboda tafi takura jummala har gara mairo sukan Dan yi dadi.

yace ba ni na siya ba mijin jummalo ne ya siya min kuma batun in zauna a birni gobe war haka ma ina can aradu.

Mairo dake fitowa a ban daki ne ta cire hulan dake kanshi tana rafka salati tace na shiga uku ni mairo yau na taba hulan binni.

Bata rai mando yayi Dan ya tsani a taba masa kayansa Wanda dabi'a ce Wanda ya dauka daga wajen jummalo.

Saboda rashin kaunar ta da ake yasa ake diban mallakinta ana lalata wa hakan yasa ko takalmin ta bata bari a fili balle a saka Mata.

Karbar hulan sa yayi yana gyara Karin ta yace ni mairo banason kauyanci kinsan bana son kina taba min kaya koh? Tam.

Ganin jummalo ta samu guri ta rabe yada m. Salis yace bazaki shiga ba? Tace duka na za'ayi AI saide mu shiga tare. Wani iri yaji a zuciyar sa ganin yarinya mai kaudi da abin dariya lokaci daya ta koma abin tausayi daga zuwa gidan uban ta.

Inda nan ne ya dace ko wani mahaluki yayi farin ciki in yana ciki ita nan ne ke bata faduwa gaba tare da tada Mata hanakali.

Shinfida taburma mando yayi ya fice abinsa yace ma su m. Ahmad din su shiga sannan direct ya nufi gidan kawu musa. Wanda yake wan mahaifiyar jummalo.

Nan ya gaishe sa tare da sanar masa ya hanzarta su tafi zuwa gidan su domin anzo neman auren jummala kar inna ta hana.

A hanya ne mando yake ta shafa ma kawu musa da Dan musa labarin duk abinda ya faru daga fitan su gida har zuwa yanzu.

YAN UWA NA MASU MESSAGES DA KIRA NAGODE SOSAI. ALLAH YA SAKA DA ALKHAIRI ALHAMDULILLAH NA SAMU SAUKI DAN HAKA ZAMU DAURA DAGA INDA AKA TSAYA.

SU WAYE SUKAYI MISSING MUTANEN NE? WAI SHIN KUNA SON JUMMALO KUWA? IDAN MA BAKU SONTA KU SO TA DAN TANA DA MAHIMMANCI A LABARIN NAN😁.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

miss untichlobanty 💕

September,2020.

YA JI TA MATAWhere stories live. Discover now