Da sauri ya Mike ya sauka tare daura kanta a cinyarsa yace ke tsolon rake ! Tsolo, tashi mana banason wasan banza fa. Amma babu wani sauyin daya gani.
A gado ya daurata da sauri ya yaiyafa Mata ruwa numfashi taja kawai taci gaba da kwanciya a wajen hannunta ya kama ya saka a nasa yana shafawa a hankali idonsa har yayi ja yace ki tashi my tsolon rake Dan Allah kar ki mutu.
Idonta ne ya ciko da kwalla ashe dama yayan nata ya damu da ita? Yace ki tashi karki mutu baki bani kurwata ba kinji. Wani kululu ne ya tsaya Mata a wuya kamar ta falla masa Mari. Juya kwanciya tayi da sauri ya washe baki yace la dama kin tashi tace dalla ban tashi ba ni ka rabu dani.
Hannu yasa zai juyo da ita yaji jikin ta zafi rau rau yace tofa tsolo bakida lafiya ne? Tace ban sani ba ka barni nace. Ruwan dimi ya samo da towel ya birkito ta tayi ruf da ciki.
Yaye riganta yayi ta baya ida taji ciwo dazu yaga yayi ja wajen. Yatsu biyu yasa a hankali ya shafa wajen sanda tsikan cikinta suka Mike ciccire Mata kayan yayi daga ita dai inner wears dinta yaja bargo ya rufe Mata jiki yace ina zuwa sannan ya fita.
.........
Bangaren su umma kuwa su lud suna fita daddy ya rungume umma yace kai marakisiyya zuciya na war wallahi har naji na warke.
Na ma rasa me zanyi saboda farin ciki kai Allah na gode maka. Umma tace Allah ya kara hade kansu ya basu zaman lafiya daddy yace ameen.Umma tace amma Alhaji yanzu in kuma yaron nan ya gane auren nasu contract ne fa? Ko ita ta gane wayo mukayi Mata? Yace karma ki damu insha Allah komai zai tafi dai dai babu wani matsala da za'a samu tace toh Allah yasa.
Daddy yace da Dan uwana yana raye da bansan iya adadin farin cikin da zaiyi ba. Murmushi umma tayi tace wannan haka yake domin shi mutum ne me son zumunci.
Amma wani hanzari ba gudu ba kana ganin yaron nan bazai cutar da ita ba? Dan kasan sa ba hakuri ne dashi ba fa kar ya nakasa marainiyar Allah. Murmushi manya daddy yayi ya jin jina kai yace marakisiyya kenan. Shin ni na nakasaki ne? Dauke kai tayi tace kai wallahi Allah wani zubin shiyasa banason muyi magana dakai sai ana magana mai muhimmanci sai ka dinga tsokana ta.
Yace in ban tsokani matata nayi wasa da dariya da ita ba da wa zanyi? AI shiririta da sanin ya kamata da karamin kwakwalwa shine zaisa miji yace matarsa zata rainasa in yayi Mata wasa da dariya. AI Sheridan raini babu wadda bai cika ba da zata rainasa da ta rainasa tun daren da aka daura auren su.
Yo duk tsurar ka fa ko ka haife ta haihuwar uwarka haka zaka koma a gaban ta in ba'ayi wasa bama sai ka marairaice Mata. Amma haka zata karbe ka cikin so da kauna tana girmama ka.
Inka isa tube ka fita kofar gida ma kaga yanda yara zasu biyo ka da wakan mahaukaci. In kuwa kanka yana rawa jeka fada yadda kana hira da matar ka a parlour zaka ce kanason ayi...suma kawai ka Mike gaban sarki ka hau tubewa.
Wallahi wani batada mai zafin rai kamin a bashi umarni zai tsula maka daya a gadon baya. Dariya umma tayi tace ni dalilin da yasa nakeson hira dakai kenan ko wani lokacin sai ka sani farin ciki sannan in kayi min ba daidai ba baka jin nauyin bani hakuri shiyasa nake ganin girmanka.
Yace toh AI hakan ke kawo zaman lafiya abinda yasa wasu mazan suke kin bada hakurin sunsan matan nasu zasu ce AI dan yana tsoro na ne yasa ya bani hakuri ko Dan kaza da kaza ne yasa ya bani hakuri. Umma tace toh ai nan kuma laifin mijin ne kaima ya zakyi kaje ka dauko mace mara tarbiyya ka kawo gidan ka kuma ka tsammaci abin arziki?
Bazai yuwu ka dauko fulawa a kuji kace zata zo maka babu kwayar cuta ba ko ka dauko kuji a cikin fulawa kace AI tunda jikin fulawa ne babu damuwa.
Saide ka Nemo flower a flower zaifi maka sauki. Amma in ta zama dole ne to gara ka dauko flower a cikin jikin kila in ka wanke ta wayoyin cutar su mutu.Daddya yace wanna haka yake uwar gida ta kuma Rabin raina. Karki damu kinji bani abinda zai same diyar mu saboda kinga dai yaron nan gado na yayi itako mutuniyar taki abban ta ta gada kuma dai kinsan yaya abbanta yake. Tsabar masifa sau uku yake zubawa mahaifiyar ta ciki.
Ture kafadar sa umma tayi tace abar zancen dai shikenan ni hankali na ya kwanta yanzu dai me zakayi in dafa maka? Yace duk abin da Rabin raina zata ci shi zanci nima.
Gyada kai tayi tace toh AI shikenan ni fate fate nakeson sha yace fine nima ya min tashi tayi ta fita bayan ta bashi laptop dinsa.
........
Bangaren su m. Ahmad kuwa tun da ya tashi yayi shiru ya kafe m. Salis da ido yana tuno labarin da m. Salis din ya bashi na zalinci da akayi masa. Ajiyan zuciya ya sauke a ranshi yace ya zamto dole a karbo maka hakkin ka m. Salis kaida kanwar ka baku cancanci abinda akayi muku ba.
Hannunsa m. Salis din ya kama yace yaya na me kake tunani ne wai? Tashi m. Ahmad yayi ya zauna ya shafa fuskan m. Salis din yayi yace kawai ina tunanin idan ba mutum mara imani ba waye zai yi muku irin zalincin da kawunka ya muku shine nake ganin ya cancanta a karbo muku hakkin ku.
Matsowa m. Salis din yayi ya kwanta a cinyar m. Ahmad din yana wasa da yatsar hannun m. Ahmad din yayinda idon suka shigo da kwalla yace tabbas ban yafe masa ba kuma banida niyar yafe masa kuma koda ni na yafe masa kanwata bazata yafe masa ba.
Haduwa na dakai ALKHAIRI ne nasan zaka taima min mu karbi hakkin mu da izinin Allah amma nafi so na Samu matsalar da ya janyo min a warware ta ya zamto na daina sha'awan maza domin ni duka biyu suna burgeni dukda ban taba yi da mace ba.
M. Ahmad yace karka damu na nema mana appointment da wani likita komai zai dawo normal. M. Salis yace insha Allah amma no abinda ban gane ba shine ya za'ayi ace Kia normally bakason Mata sai maza kuma dai wannan abun ba'a haifan mutum da ita.
Kallonsa m. Ahmad yayi yace ba'a haifan mutum sa ita kuma? Yace eh kai ka dauka haifar ka akayi da ita? M. Ahmad yace eh na karanta wani article naga ance jar gadonsa anayi ma.
Murmushi m. Salis yayi yace naga wannan article din AI amma har yau babu wani likita da iya tabbatar wa kawai hypothesis ne (hypothesis na nufin tunanin da wani yayi akan Abu ba tare da ya tabbatar da abun ba kuma bayida wani shaida da zai tabbatar da abin wato dai a takaice magana ce ta" a ganina")
M. Ahmad yace toh kuwa indai hakane akwai lauje cikin nadi San ban taba yi ba kuma ba'a taba yi dani ba balle a juya ni kaga kenan wani Abu dole ya faru Wanda ni bansan dashi ba.
Kallon juna sukayi kamin dukansu biyu suka jinjina kai.TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
26th August,2020.
YOU ARE READING
YA JI TA MATA
Mystery / ThrillerWannan labari me suna YA JI TA MATA shine littafina na uku.... Labarin wani saurayi ne Wanda bashida aiki sai zina, a cewar sa ba laifinsa bane Allah ne yayi sa hariji. Toh hakan ne yasa iyayen sa suka rufe ido sai yayi aure amma fa an gudu ba'a tsi...