CHAPTER 30

1.2K 117 9
                                    

IDAN KUNA KARUWA DA LABARINNAN AYI FOLLOWING DINA SANNAN AYI VOTING

"Abdurrahman bn awf ya hada yar walima haka sai ya gaiyace mu inda cikin abin sha harda giya. Da lokacin sallah yayi sai sukace ni zanja sallah inda na karanta "YA KU WADANDA BAKUYI IMANI BA,NI BANA BAUTAWA ABINDA KUKE BAUTAWA,KUMA MUNA BAUTAWA ABINDA MUKE BAUTAWA" a take Allah ya saukar da aya ta 43 na cikin suratul nisa'I: "

"يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَقْرَبُوا الصَّلَاةَ وَأَنتُمْ سُكَارَىٰ حَتَّىٰ تَعْلَمُوا مَا تَقُولُونَ...."

HADISI NA 3026 A CIKIN BABIN TAFSIRI LITTAFI NA 44, JAMI'A TIRMUDHI.

Toh a lokacin ne aka fara kawo takunkumi akan shan giya a haka a haka har aka haramta shi gaba daya.
Sannan kuma yana da haddi toh amma yanzu a zamanin nan namu gaba daya ma ba a yi.

Yace I see ina zuwa toh. Daukar wayar sa yayi tare da yin research kusan na 25 min kamin ya tashi ya shiga toilet yayi wanka kamar yadda ya gani a research Wanda ya tabbata ba cuwa cuwa domin an basa hadisai sannan ya kabbara sallah.

Bayan ya idar ne ya nemi waje ya kwanta yana wasu nazarce nazarcen sa.
Juyowa ya yi ya kalleta yaga ta rufe ido kamar ta koma bacci.

Yace malama marakisiyya shin bakisan cewa ba'a bacci bayan la'asar bane? Nide in ba kuskure nayi ba naji ance wai manzon Allah yace "duk Wanda ya yi bacci bayan sallan la'asar ya rasa kwakwalwar sa toh kar ya tuhumi kowa sai kansa"

Bude ido tayi ta kallesa tare da sa hannu ta janyo nasa ta sa a cikin na ta. Kallon ta ya yi alamun lafiya ?

Murmushi ta yi sannan tayi ruf da ciki kanta a sama kamar kadangaruwa tace wannan hadin bayida wani sahihanci da'ifi ne ka duba silsilat al-da'ifa lamba na 30.

Akwai hadisai dayawa da'ifai Wanda jama'a sun dauka sun tabbata saboda yadda aka da sa musu a zuciya.

Gyada kai yace I see. Kallonta ya ci gaba da yi ta tashi da kyar saboda yanda jikin ta ya yi Mata nauyi.

Sallah ta yi ta dawo ta kwanta tare da shigewa bargo domin yanzu zazzabin da take ji ya sauka Mata Dan haka wani mugun bacci take so tayi.

Jan bargon ta yi hakan yasa kadan lud ya bude. Ja shima ya yi ta ja ya ja ta sake ja ya sake ja shima.

A tare suka taso kowa zaiyi masifa ganin yadda suka turbune fuska dukan su biyu yasa suka fashe da dariya kuma kawai sai suka sake kwanciya.

Kureta ya yi da ido tun tana nuna kamar batasan yana kallon ta ba har de ta juyo tana taba fuska tace akwai wani Abu a fuska na ne?

Gira ya daga ta sauko tazo ta kalli kanta a madubi har ido ta zazzare bata ga wani Abu dake fuskar ta ba banda alamun gajiya tace nide banga komai ba.

Yace zo in nuna miki zuwa tayi ta zauna yasa hannu yana shafa lips dinta tsayawa kallon sa tayi tana jira ya nuna Mata abinda ke fuskar na ta Dan ita Sam bata kawo a kanta cewa wani abun zai yi ba.

Hade bakin su yayi Wanda hakan yasa ta sake yin mutuwar zaune kamar a karo na farko yayin da kunnuwanta suka daina jin komai sai sautin bugawa zuciyanta. A hankali ya kwantar da ita....

Can bayan wani lokaci ya raba fuskarsa domin ya shaki numfashi yayinda ita kunya ma ya rufe ta haka kuma ta rasa ma me take ji a zuciyar ta kawai de abinda ta sani shine gabanta yana tsinkewa.

Janyo ribbon dinta yayinda gefen side bed ya kama gashin ta ya daure yace wannan shine a abinda ke kan fuskar ki Wanda ya stole min idanu.

Ruf da ciki tayi ta cusa fuskar ta cikin pillow tana dariyar jin kunya tace lallai ma ya lud dinnan shima matsowa yayi gefen ta yace Allah da gaske nake my tsolon rake ba shi kadai bane ma ya stole min ido suna da yawa.

In nuna miki sauran? Da sauri ta girgiza kai yace ah ah nide sai na nuna miki.

Rufe kirjinta ta fara yi Dan sarai yasan inda zancen ya dosa. Cakulkuli ya fara Mata tana tureshi a haka har ya danneta a kunnenta ya rada Mata my beautiful wife please kinji ? Tace ni dai ban yar da ba.

Abin tausayi ya yi yace ya toh kikeso nayi kinsan dai ban ajiye kowa ba sai ke kuma de nasan bazakiso naje wajen wata ba.

Yadda yayi maganar ne ya bata tausayi hakan yasa tace toh yanzu dai naji amma kalla kawai zakayi.

Yace na yarda tace kalla kadai fa ! Yace an gama hajiya ta. Rufe ido tayi tace toh bismillah. Mutumin ku daga kallo anki a gama kallo yanzu ne anjima ne. Tace na gaji fa bacci nake ji yace ni kam ban gaji ba kallo nake son yi.

Jan bargo tayi ya bude ta ja ya bude tace ni fa bacci nakeji please ka barni nayi bacci kaji? Ya ce toh ki zabi daya ko kiyi bacci nayi ta kallon abina ko kuma ki bari in taba kadan sai kiyi bacci.

Daga karshe dai haka marakisiyya ta tausaya masa aka dauki zabi na biyu kamin ta kwanta tayi baccin ta.

Janyota jikinsa yayi shima ya rufe ido domin yayi bacci amma fa bai manta da abinda ba Dan hannunsa akai ma yayi bacci tsaban neman magana😂

.....

M. Ahmad kuwa bayan sun koma gida da sallamar sa ya isa zuwa ga mahaifiyar sa tare da gaishe ta tasa masa albarka bayan sun gaisa.

Zama ya gyara da kyau Wanda hakan ya tabbatar Mata da cewa maganar mai mahimmanci ne. Kallonta yayi yace mami na dama tambaya ne nake so nayi.

Tace toh ina jin ka Dan albarka yace shin an taba yi min wani tiyata sanda nake yaro haka? Ko a bani wani magani ko wani Abu dai da ya shafi tunani na? Tace kai gaskiya baka taba yin wani jinya ba ma balle ayi maka tiyata.

Yace mami ki dai yi nazari shiru tayi can ta dago wani hope ne yazo masa kawai sai ta girgiza kai. Take ya ji nauyi a zuciyar sa tare da sauke ajiyan zuciya tace amma dai akwai wani allura da akace za'ayi maka sanda na haifeka.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

31st August,2020.

YA JI TA MATAWhere stories live. Discover now