CHAPTER 47

927 114 21
                                    


*NOT EDITED*

M. Ahmad yace mai haja family name din mahaifiya ta ne bana aiki da sunan mahaifi na. Abinda na sani dai shine sunan mahaifi na jibril. Zaro ido likitan yayi yace jibril wa? M. Ahmad yace gaskiya sai na tambayi mahaifiya ta.
Nan sukayi sallama su m. Ahmad din suka tafi.

Bangaren su lud kuwa gidan umma suka nufa da niyar zasuyi Mata surprise tunda basu fada Mata zasu zo ba.
Taji dadin ganin su sosai haka suka dinga hira. sai yamma tukunna suka koma gida bayan an hadasu da abincin dare.

Kamin su tsafin ne sai ga mansura kuskus ta shigo tace ma marakisiyya mu ja labule. Suna kebewa marakis tace shegiya kede in irin harkannan ya taso kece a gaba gaba anji kunya.
Mansura tace ke de kika sani da babu irin mu AI da kin shiga matsala.

Nan ta fada Mata kayan itatuwan da zata samu sai ta hada da garin da ta bata shikenan ba wani kayan cutarwa a ciki. Godiya tayi Mata kamin sukayi sallama har suka rage Mata hanya.

Kamin su karasa ne take fada masa AI zata koma makaranta yace toh ba matsala. A take ya Kira driver din gidan su yace ya kawo masa motan marakisiyya su hadu NNPC  gidan mai.

Marakisiyya kuwa ana komawa aka bude fridge akayi Hadi ta saka rabi a Kofi tare da zuba garin a ciki ta sha ta ajiye sauran. Aka je aka yi wanka aka sha turare.

In takaice muku magana bayan marakis ta sha hadi nan lud ya gane an Sami matsala, kamar yadda marakis ke tunanin tausaya Mata lud keyi toh shima lud din haka yayi tunani yau Dan sanda akayi tashin hankali.

Da kyar ta barshi yayi bacci shi kuma ya dage bazai bada gari yace ya gaji ba. Da mugun sanyin sadiya ya tashi ya gudu zuwa gidan su zannu Dan bayason ma ta tashi ta kawo masa wani sabon zance.

Yanzu shi kam Dan ba kara duk yadda zaiyi ya dinga arcewa toh zaiyi. Tunda ya gama bawa zannu labari ya zauna ya dinga masa dariya har ranshi ya soma baci. Tashi yayi yace in bakada shawara da zaka bani gara nayi tafiya ta.

Riko Rigan shi zannu yayi yasa fuskan tausayi yace my lud ina zaka? Wai shi.a dole zai kwaikwayi marakis ne. Jifan shi da takalmi lud yayi yace bana son wulakan ci fa. Dan kaga ina neman shawarar ka shine zaka na tsokana ta?

Kokarin danne dariyar sa yayi yace toh I am sorry a yafe min please da alamu dai wannan matar tafi karfin ka toh kawai ka fada Mata mana kaga sai ta na tausaya maka. Lud yace kai mutumin ba wasa bane fa.
Fada daban aikatawa daban. Zankai ga yadda za'ayi.

Marakisiyya kuwa ko da ta tashi taga lud baya nan ta Kira wayan sa bai daga ba kawai sai ta tashi tayi wanka bayan tayi order din abinci ta ci abinta.
Daukan tarkacen ta tayi sai makaranta kuma shirye take da duk abinda zata riska.

Shigan ta makaranta ke da wuya yan sa ido suka hanzarta suka zanzara wa class rep. Ai ga marakisiyya ta dawo. Nan fa makaranta aka dinga binta da ido wasu kuma suna yi Mata congratulation.

Koda m.ahmad ya shiga ajinsu domin ya koyar aa kin kallon inda suke zama yayi domin rabon da yasa ta a idonsa tun ranan da wannan abun ya faru.

Haka de marakisiyya ta dinga binsa da ido tama rasa me ke Mata dadi ita dai tana ganin kamar tana son lud amma kuma kyawawan halin m. Ahmad ke Jan hankalinta zuwa gareshi.

Bayan an tashi m. Ahmad ya koma zuwa ga likita saboda m. Salis bai tashi ba yana da lectures guda daya da zaiyi. Koda ya zo likitan na ganin sa yace ah malam Ahmad Kaine da war haka aiko kazo da sauri Dan yanzu nake shirin zuwa duba wani patient.

M. Ahmad yace jiya na tambayi mahaifiya ta take sanar min da cewa sunan mahaifi na jibril mustapha arancaba(Dan Allah in akwai me irin sunan ba shi nake nufi ba). Dafe kirji litan yayi ya ja shi suka koma office yace kai Alhaji arancaba ne mahaifinka? m.Ahmad yace eh likitan yace tashin hankali mahaifinka na daya daga cikin mutanen arewa na farko da sukayi luwadu a baiyane.

Lokacin da ake kokarin kera allurar da nake fada maka ai yana daya daga cikin Wanda suka saka kudi da komai nasu akayi. Innalillah wa inna ilaihi raji'un.  AI ya mutu mutuwar wulakanci ma kuwa.

An boye mutuwar sa ne saboda in masu itin halinsa suka ji kila zasu gyara hali. M.Ahmad gaba daya ji yayi guiwan sa tayi sanyi yace toh yanzu ya za'ayi kenan? Dr yace karka damu akwai maganin allurar da akayi maka.

Saide baza'a samu anan ba amma nasan wani aboki na insha Allah har nayi masa magana tun jiya zuwa jibi ma allurar zai osoba sai kazo ayi maka daga nayi ma na kwana biyu shikenan ma.

Abinda yasa take da effect a kanka saboda kana jariri akayi maka ne kuma ina matukar zargin cewa  shi ne ya Nemo ku kuma ya same ku amma bai nuna muku ya same ku ba shine ya biku a boye da mahaifiyar ka ta haife ka shine yasa akayi maka wannan allurar.

Amma ni dai bansan me yake nema ko ya shirya yi ba toh koma de wannene insha Allah ka tsira tunda de yanzu ya koma waken alkalin da babu ya shi. Nan m. Ahmad yayi masa godiya tare komawa gida ya fada ma mahaifiyar tasa. Harda hawayen farin ciki ta rungume shi ko ba komai Santa zai samu lafiya taga jikokin ta.

Haka rayuwa taci gaba lud yana gudun marakisiyya ita kuma tana tausaya mai bataso ya neme ta tace masa ta gaji shiyasa ta dage da gyaran jikin ta.

Ankai ankawo fa to the extend lud sai ya bari tayi bacci yake dawowa gida sannan kuma kamin ta tashi yake fita har ta fara tunanin kode baya dawowa ne? Kiran umma tayi umma tace Mata ai yana yawan zuwa ya yini amma dai in yazo gobe zata tamabaye shi.

Lud fa yanzu a wajen zannu yake biya gaba daya ya mugun ramewa ne ? Har duhu yayi banda komai sai hanci Allah sarki tun zannu yana masa dariya har ya fara jin tausayin sa.

Zama yayi ya dafa kafadar sa yace my man kaje gida mana kawai sai ka fada Mata ka dena gudu kasan itama tana da bukata kar ka sata a wani hali yau 4 days fa Baku hadu ba.

Ajiyan zuciya lud ya yi yace my guy, naji kamshin gaskiya a maganar ka Allah ya gani yau zanje na fada ma marakisiyya gaskiya komai ta fanjam fanjam ta tausaya min ta daga min kafa.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

26th September,2020.

YA JI TA MATAWhere stories live. Discover now