Da asuba marakisiyya na tashi ta zabura shafa inda ta kwanta tayi ta sauke ajiyar zuciya tunowa da cewa ta sha maganin ta muma ta saka pad yau bata tsula ba. Da sauri ta shige bandaki ta cire ta gyara jikinta tayi su alwala sannan ta fito sai lokacin ta lura ma ashe ba a gida take ba tunowa yayi da duk abinda ya faru jiya Wanda yasa ta kara murtuke fuska tana jin kamar tayi wa lud mugun duka Dan ba karamin haushi ya bata ba jiya bayan tayi sallah ne tazo ta tsaya a kansa.
Sai zata tashe sa sai ta fasa sai zata tashe sa sai ta sake fasawa. Rufe ido tasa hannu a kafadar sa ta bubbuga, juyi yayi yace uhmm? Menene? Cikin dashesshiyar muryarta Wanda bai gama gyaruwa ba tace ka tashi kayi sallah. Sake gyara bargonsa yayi yace Sally ki rabi dani don Allah me zan miki da sanyin safiyan nan? Sake bubbuga shi tayi a kufule ya tashi ya zauna ya finciko ta ya manna Mata peck a baki ya sake kwanciya fuskarsa na kallon sama yayinda Rabin jikinta ke kan cinyarsa yana fadin shikenan AI ko? Bye bye sai kin dawo. Mikewa marakisiyya tayi ta goge bakinta kamar zatayi amai ta daka masa duka a cinya.
Da ashar don da ta fara da k*tma ya Mike ya Damkota sai a lokacin ya kalli marakis ce yace tsolon rake Dan.....ki me kikeyi anan? Ni sa'an ki ne zaki dakeni? Tabe baki tayi ba raini ba gimamawa tace yi hakuri ba da niya nayi ba da farko dai so called aure ne ya kawo ni dakinka.
Ba biyu kuma ni ba sa'ar la bace ka girme ni, saide dalilin da yasa na dake ka shine..........
Yace kaji makaryaciyar banza da wofi. Ni me zanyi da tsiya irinki wai ke tsolo in bakiyi karya bazaki rayu bane ko me? Yanzu ace mutum kamar sandan rake AI ko yaro ba abinda zaiyi dake bare babba. Tace munji dai ko ba komai AI sanda rake yana da zaki ga ruwa ta ko ina kuma yafi gundiren doya Wanda sai anci wuya ake dafawa.Kaga sandan rake ko na 200 ka siya ta ishi kowa ya samu amma doya fa ansiya karama yar 900 kuma ba kowa zai koshi ba mutum 2 ma sai su cinye,abinda nake nufi shine nafi albarka akan o'o.
Yace kut! To ke banda shirmen ki daga an shanye rake ake watsar da totuwar a titi, race shi kuma bawon doya kirashi ake gaban madubi ko? Yace bitch, wai Sally na kike zagi ? Tace sallyn ka? Kananu tayi da ido tace ka sake kira na da bitch ? Wow! Hmm ni na jawa kaina.
Kama kanshi tayi ta kwantar a pillown tace ayi bacci lafiya ta koma kan kujera ta kwanta taja bargon ta bashi baya. Nazari ta fara ya akayi ta samu bargo bayan da liffayar ta ta rufu? Murmushi tayi da tayi tunanin lud ne yasa Mata daure fuska tayi da ta tuna rashin mutuncin da ya Mata.
Shima saukowa yayi kamar barawo da sanda ya leka fuskarta yaga ta rufe da bargo hakan yasa ya fara dagawa a hankali. Tunani marakisiyya tayi what if jiya ya yi Mata wani abun da sauri ta dago zatayi masifa suka gware goshi yace what in h*ll is this ? Kanki daya kuwa jiyadda kika gwara min wannan jirgin naki a goshina.
Tace ba ma wannan ba me kamin jiya da ka saka min bargo ? Murmushi yayi yace ba komai fa kawai Dan kalle kalle nayi kuma ma sai naga babu abin kallon amma bari muga. Ya kai hannunsa wajen riganta da sauri ta dafe tasa kafa ta turesa tace Dan iska kawai me ma ya kawoka kusa da fuskana? Yace morning kiss nazo karba amma sai na samu morning collision a goshi.
Yake tayi tace AI da ka fada da wuri zo in baka tsugunawa yayi ya sakala hannunsa biyu a kwankwason ta yayinda take zaune a kujera saka hannun ta tayi ta riko fuskarta ta kawo kusa na nata a take murmushin dake kan fuskarta ta dauke tace me zai hana kaje wajen so called Sallyn ka? Sai ta baka warm k*ss ko ya kace? Um? Ta daga gira? Dariya yayi yace Allah yasha dake bakya sona bare ki samu heartbreak dama gwadaki nati kin wuce test number one.
Yana kaiwa nan ya shiga toilet yana sauke ajiyan zuciya. Tsaki taja ta kwanta yayinda shi kuwa ya kunna kansa ruwa yana nazarin yadda zaiyi ya kwato kurwansa a hannun marakisiyya domin kuwa tana kara cinye kurwarsa Dan yanzu a cikin jikinsa yake jinta. Solution daya ne kawai zaiyi kokari su rage yin fada daga nan sai ya roketa ta bashi kurwarsa tana bashi sai ya Mata na jaki.
Da wannan shawaran ya fito daga wankan ya samu har ta koma bacci. Sallaya ya shinfida yana tunanin ta ina ma zai fara sallar kuma raka'a nawa? Dan shi banda sallah na Eid sai juma'a sauran kawai sai rabbi yayi ne yake jona masallati ayi dashi. Tagumi yayi yace kai ya kamata na hankalta fa kar mala'ikan mutuwa yayi wuf dani Dan tun sanda aka daura mina ure da wancan yar tsana na gane banida iko da kaina.
Daukar wayan sa yayi tare da searching komai akan yadda ake yin sallah tare da sunnoni har ma farilla duk ya koya Dan kusan 30 min ya ribanta yana research. Bayan ya idar ne yaga marakisiyya tayi fale fale Rabin jikinta ma ya sauko a kujeran. Daukota yayi ya daura a gadon bayan ya gyara ya rufeta da bargo yana kallonta.
Riko hannunta yayi a hankali yace yar kanwata na gode da kika tashe ni nayi sallah. Gaba daya jikin sa ya mutu saboda a Dan binciken da yayi ya ga yadda hukunci marasa yin sallah da bari ta fita akan lokaci take yaga yadda Allah ke kafurta su. Baisan sands hawaye ya zubo masa ba. Haka kawai ya ji a ransa yanason ya samu Karin Ilimi akan Islam.
Shiryawa yayi cikin wasu manyan kaya wanda bai taba saka su ba ya fita domin siyo wa marakisiyya kayan da zata Dan saka kamin ya kaita shopping.
Kamin ya fita ne ya rubuta letter ya ajiye kamar haka "morning tsolon rake! Idan kin tashi kiyi order din abinci kice dakin LUMA za'a kai. Sauran kiyi order mai tsada ni da ke ne. Sai na dawo."
.......
Umma kuwa tana zaune a gefen daddy Wanda aka daura ma drop a gida sbd yanayin NASA baiyi tsauri ba. Riko hannunta yayi bayan ta gama bashi shayi lace Mata ta ni kadai, mai zai hana ki kaiwa yarannan ziyarar ba zata? Kallonshi tayi tace amma Alhaji AI bakada lafiya ya zanyi na barka cikin yanayin nan.
Yace karki damu bacci zanyi in kika tafi zan jira ki dawo. Kinsan halin yaron nan ba kadan daga aikinsa bane ace yarinyar ba a waje ta kwana Dan tunda kika tafi da ita hankali na bai kwanta ba.
Tace toh shikenan mijina zanje. Gyara masa kwanciya yayi taje ta shirya, driver ya kwashe ta bai tsaya ko ina ba sai hotel din da lud yake kamar yadda umma ta sanar dashi.
Receptionist na ganinta ta gane ta. Gaishe ta tayi umma ta amsa sama sama. Receptionist din tace oga Luma ya fita fa. Umma tace ba wani luma nake nema ba Dana nake nema. Receptionist race eh shi nake nufi AI umma tace matar sa da. Girgiza kai receptionist tayi.
Hawa sama umma tayi direct ta nufi dakin da ta kai diyar ta tana budewa taga hajiyarku an Sami gado ta Mike cinya tayi dai dai a tsakiyar gado. Ribbon ma yasan inda dare ya masa. Dariya kasa kasa umma tayi ta sauke ajiyan zuciya. Tace umm su cuwuna (mai suna na) an Sami dadi sai bacci ake.
KAI KAI HANNUNA CIWO YAKE MIN TSABAR WAHALAR TYPING. NASAN JIYA KUN JINI SHIRU IN FADA MUKU WAI SAIDE MESSAGE YA SHIGO NI NAWA BAYA TAFIYA SHIYASA MA KO TIRAWA BANYI BA SANDA NA KIRA CUSTOMER SERVICE TUKUN YA GYARU.
TUNATARWA: A CIKIN ISLAM ADDININ ANNABI MUHAMMAD (SAW) BABU WANI ABU KAMAR BIKIN ZAGAIYOWAR SHEKARA. DOMIN WANNAN BIKIN ARNA NE KUMA MU A KOWANI LOKACI SO AKE MU SABA MUSU. A LOKACIN SA SAHABAI BASUYI WA JUNA MURNANR SHIGA SABUWAR SHEKARA KO MAKAMANCINSU SAIDE:
HADRAT BN ABDULLAH BN HISHAM YA RAWAITO CEWA SAHABBAI SUNA KARANTA WANNAN ADDU'AR IDAN AN SHIGA SABUWAR SHEKARA KO WATA:
اللهم أَدْخِلْهُ عَلينا بِالأمْنِ وَالإيمان وَالسَّلامَةِ وَالإسْلام وَرِضْوَانٍ مِّنَ الرَّحْمن وِجوارٍ مِّنَ الشَّيْطانAllahumma adkhilhu 'alayna bil amni wal iman, was salamati wal islam, wa ridwanim minar Rahman, wa jiwarim minash shaytan
(Al-Mu'ujamul Awsad' Na Tabarani, Hadith: 6237)
WACE LITTAFIN HADISI NE MU'UJAMUL ASWAD?
Al-Mu'ujam al-Awsat (a larabci: المعجم الأوسط للطبراني), daya daga cikin manya kuma sanannun littafi ne na hadisai Wanda wani babban malami me suna Abu 'l-Qāwsim Sulaimān Ibn Ahmad ibn Ayyoob ibn Muṭawyyir al-Lakhmī ash-Shāmī at-Ṭabarānī Al- Hambali
Na shekara(874-971 CE, 260-360 AH).FATAN DAI KUNA YIN AIKI DA DARUSAN DAKE CIKI DAN IN BAKUYIN AIKI DASHI BABU ANFANIN SHI..
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
20th,August,2020.
YOU ARE READING
YA JI TA MATA
Mystery / ThrillerWannan labari me suna YA JI TA MATA shine littafina na uku.... Labarin wani saurayi ne Wanda bashida aiki sai zina, a cewar sa ba laifinsa bane Allah ne yayi sa hariji. Toh hakan ne yasa iyayen sa suka rufe ido sai yayi aure amma fa an gudu ba'a tsi...