CHAPTER 46

947 116 11
                                    

Yace me kike fadi ne tace ka fini sanin me nake fadi me yasa wannan luba ko laraba ke kiranka harda cewa ka aure ta. Tsawa ya daka Mata yace marakisiyya ta daga hannu zata falla masa Mari.

Rufe ido yayi tare da kauda kai yana tsammatan saukan Marin dan gaba daya tunanin sa ya rufe kawai duk abin da Allah yayi shi zai faru.

Amma me? Sai ji ya yi an daura hannu a kumatun sa a hankali. Bude ido ya yi kawai yaga marakisiyyan na zubda hawaye. Murmushi ta yi tace ka dauka zan mareka ne?

AI duk lalace na bazan taba saka hannu na dake ka Dan raina ya baci ba. Juma na yarda da kai nasan bazaka taba cin amana ta ba. Kuma nasan baka kula ta ba ita ke damun ka.

Nagode maka da ka rike amana ta. Kwantar da kanta kawai yayi a kirjin sa. Ba Wanda yayi magana bayan minti 3 yace eh wai batun wani ciki kike yi?

Dangwale kafadan sa tayi tare da lankaya hannun ta a wuyan sa tace ba wani ciki bane fa. Maganin ta nayi maka shine ba nuna kamar kai ka amsa wayan ni kuma ina gefe na nuna kamar ciki ne da ni zamu tafi asibiti.

Dariya suka kyalkyale dashi yana Mata cakulkuli yace iye iye iye kawai kice na ja mana wanka. Tace umman fa? Yace umma AI ta iya jira ko?

Marakis tace yunwa nake ji.  Yace see your face duk kinyi kumatu kuma wancan take away din ni na ci miki shi? Tace ban koshi ba AI. Bude fridge yayi ya dauko yogurt ya mika Mata.

Yace toh kwankwade  maza tace muje zansha a mota Dan ita a tunanin ta ya mance da zancen sa na farko ba sai taga mutumin ya cire hula ya zauna ba.

Fuskan tausayi tasa tace haba daddy ayi hakuri mana please! Cikin farin ciki yace toh kema kinji me kika Kira ni dashi kika ce daddy kuma shine kike ta kwana kwana?

Abinda bata sani ba fitan da yayi yaje ya shawo wata ne. Tace toh naji bari na sha wannan din. Rike Kagan ta yayi yana wasu abubuwan sa Wanda ba wai ta mayar da hankali bane don burin ta kawai tayi transfer din kudi ma mansura.

Tana gamawa tayi message ba ma ta WhatsApp ba tace ki Nemo min abin kamin na dangana wajen umma domin samun sahihi.

Tana ajiye wayan ta kalli lud da ke ta makalkale Mata kamar kulya ba Dan taso ba haka ta bada kai.

........

M. Salis da m. Ahmad a office din doctor yayinda yake tambayan su me ya faru suka dawo da wuri m. Salis yace AI ya samu partner Wanda zai din gwada kansa ba tare da ya koma ruwan ba.

Likitan yace you are doing well fa. Kamin ya kalli m. Ahmad yace ya naka bangaren fa? M . Ahmad yace eh toh ni kwana biyu ina shan magani kwata kwata banida bukata ma.

Likitan yace AI ba a haka zaka kare rayuwa ba dole ne ka nemi lafiya dazu nake cewa nurse ta kawo min result din gwajin ka. Bari na Kira ta. Sanar da ita yayi ta kawo musu file din.

Dubawa yayi yace toh malam Ahmad ina so na yarda da abin da ido na amma kuma ina shakku. Kace ka haura 30 ko? Gyada kai m Ahmad yayi. Likitan yace a gaskiya wannan allura ce da ake yi a cikin kwakwalwar mutum wadan da suke son su canja jinsin halittar su.

Bayan anyi musu ita ne zai canja akalar sha'awan su zuwa opposite gender sai ayi musu tiyata. Wato idan mace tana son ta koma namiji za'ayi Mata wannan sai a canja halittu jikinta da na haihuwar ta zuwa namiji

Cikin wata 3 muryarta zai fara fashewa a hankali a hankali hatta kwayan haihuwar ta zai dawo na maza, tayi su gemu shikenan zata dawo namiji kuma babu wani Abu na matan taka da zai yi saura a jikin ta.

Haka shima namiji idan yana so ya koma mace toh saide lokacin da namiji zai dauka yafi na mace. Amma abinda nake so ki sani shine wannan haramun ne a musulunci. Idan mutum yana son kansa da zaman lafiya toh kar ma ya fara.

Toh irinshi me muka ga anyi maka Wanda ya matukar bani mamaki sosai ma kuwa domin shekaru 30 da suka wuce ba'AMA San abin sosai a duniya ba balle ta zo Nigeria.

Dan Allah zan iya sanin family background dinka? M. Ahmad yace nide abinda mahaifiya na ta sanar da ni shine mahaifi na ya kasance me neman Mata da maza a lokaci daya hakan ya haifar Mata da INFECTION me tsanani har takai ana tunani kar ta haihu shi ya fi Mata sauki.

Toh a wannan yanayin ne ta Sami ciki na sai ta saukar da ranta ma ni domin anyi anyi ta zubda ni amma ta ki yarda kuma an sanar da ita idan har ta bari nayi wata biyar a cikin ta dukan mu muna cikin hadari ko ta mutu ko na mutu ko mu koma a tare.

Tace indai akwai chances zan rayu ta yarda ta mutu. Tun daga lokacin ta dauki damaran kareni kuma ta sha alwashi mahaifi na bazai taba daurani a wannan kazamar hanyan ba.

Yana gane tana da ciki yace sai ta basa Dan taki daga karshe tayi kokarin guduwa nan ya kalleta. Wani laraba Allah ya bata daman guduwa. Gadon nata kuwa dama shi ke juya wa domin an bar Mata kudi na fitan hankali.

Kawai ta dauke takaddun da ta gani ta saci iya dalolin da zata iya dauka. Mahaifi na na samun labari ta tsira ya fara neman ta domin ya kwace ni Dan yasan in dai ina hannun sa dole ne ta bada dukiyan a bani.

Har yau bakusan inda yake ba, ya mutu ko yana raye Allah ne ya sani. Likitan yace bana so na yarda da kai amma kar ka ce min Alhaji  mai haja ne mahaifin ka?

M. Ahmad yace mai haja family name din mahaifiya ta ne bana aiki da sunan mahaifi na. Abinda na sani dai shine sunan mahaifi na jibril. Zaro ido likitan yayi yace jibril wa? M. Ahmad yace gaskiya sai na tambayi mahaifiya ta.

NA YAU BABU YAWA AYI SORRY ☹ DAN ALLAH AYI MIN COMMENTS, TARE DA VOTES.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

24th September,2020.

YA JI TA MATAWhere stories live. Discover now