CHAPTER 57

818 112 21
                                    

Shi kuwa m. Salis tunda yaji kalaman m. Ahmad ya saka wayar sa yayi a aljihu bai damu da ya kashe ba sannan ya nufi gidan sa yabar mama tsaye ta ma rasa me zatayi ko tace dukda ko bata ji me suke cewa ba.

Kawai zama tayi ta fara cin abinci Dan kar ta daga wa kanta hankali, Abu daya da ta sani shine komai rintsi wata rana zai wuce kuma ba yadda za'ayi danta ya barta har abada.

M. Salis kuwa yana zuwa gidan sa ya samu mando na zaune a gefen jummalo ya baza tagumi yana tambayar ta wai me ya faru kwana biyu bata wasa da shi kamar yadda ta Saba ko Dan tayi aure ne?

Girgiza kai kawai tayi ta barsa ya ma rasa abin cewa. M. Salis zama yayi ta dago ta kalleshi shima itan yake kallo bai yi magana ba itama bata ce komai ba. Tace na kawo maka ruwa? Jingina yayi da kujera tare da daga kai sannan ya sauke ajiyan zuciya.

......

Bayan ya sha ruwan mando ya Mike ya basu guri domin sun gaisa lokacin da jummalo ta tafi kawo masa ruwa. Zama jummalo tayi a gefen sa ya Dan matsa Wanda bata ma lura ba.

Tace wai mi ya faru ko wani Abu ya samu mama ne? Kace min zaka je gaishe ta yanzu kuma ka.dawo min a haka. Bai ce Mata komai ba tana ta zuba saida kaf ta tsayar da maganan ta lokacin da taji yace KINASON YAYA NA?   Kyakkyafta ido ta fara da sauri tana kallon shi tace mi kashe?

Mando dake labe a bayan kofa yayi saurin toshe bakin sa Wanda ya kasa rufewa tare da zaro ido. M.salis yace yanzu ace idan na mutu zaki iya auren ya Ahmad?

Tace chabdi jan ya amadu da yake shewa ina da rawan kai din ni gaskiya bana sonshi gara dai kai din zan iya zama da kai har in fara sonka. M. Salis yace idan kuma yana da wata cuta Wanda sai dole kin aureshi zai warke fa?

Tace eh toh wannan lokacin zan aure shi Dan in taimaka mishi saide.... hannu ya daga Mata yace kar kice saide shikenan dama Ansar ki nake son ji.

Tashi yayi ya shige dakin shi jummalo da ta rike saide dinta ne ta karashe... saide idan ya min ba daidai ba zan Rama.

Sansadawa mandi yayi zai shige dakin sa dake waje ya bige kwandon shara. Jummalo tace toh zo nan munafuki Allah ya kama ka. Shigowa tayi har ya fara hada gumi tsamo tsamo da shi sai kace beran da ruwan sama yayi masa duka.

Tace duk maganar da nayi maka shewa babu kyau sauraran maganan da bai shafe ka ba baka daina ba ko? Yace kiyi hakuri adda juma na daina.

Hararran sa tayi tace zan kamaka fita kamin inyi kwallo da kai. Fita yayi da gudu Dan yasan halin ta yanzu sai tayi masa dukan.

M. Salis ne ya fito da wani karamin jaka a hannun sa ya mika Mata hijab tace muje. Tace ina ? Bai kulata ba ya fice dakin mando ya shiga yace masa ya dauki kayan sa guda uku ya sa a jakar da ya ajiye masa a gado sannan ya fita.

A mota ya samu jummalo ta kalle sa kamar zata yi magana wani Abu ya gwabe ta. Mando ne yazo shima tsilif ya shige m. Salis ya tsaya a gidan mama ya sauke mando tare da mika masa dubu biyar yace masa zasu yi tafiya ne zasu dawo ga wannan koda zai bukaci wabi Abu.

Godiya yayi ya karba sannan ya sauka daga motan sallama suma suka yi wa mama m. Salis ya shiga dakin m. Ahmad bayan kamar minti Goma ya fito daga nan suka hau babban titi sai birnin taraiya. Jummalo tun tana rike maganar ta taga fa kai bazata iya ba hakan yasa tace wai me ya faru zamu tafi birnin taraiya ? Ina ne shi wannan garin ?

Kawai kallon ta yayi kamin ya dauke kai wani Abu ya sauka a fuskan sa shi ba murmushi ba shi ba kuka ba shi ba farin ciki ba haka shi ba bakin ciki ba yace gyara zaman ki.

Tace ba kai kace in ina tare da kai in saki jiki na ba? Yace AI yanzu a mota muke. Ganin bai bada wani kofar yin magana ba yasa ta gyara zaman nata.

Kallon window ta fara tana kirga bishiyoyin da suke wucewa a haka har bacci ya kwashe ta ba tare da ta ankare ba. Hakan ne ya bawa m salis daman kare Mata kallon tare da tsaida zuciyar sa kan abin da ya yanke.

Wajen 2 dare suka isa Federal capital territory Dan haka m. Salis ya nema musu makwanci. Washe gari da sassafe ya tafi neman Wanda zasuyi masa tracking din numbar m. Ahmad duk sai suke cewa wayan sa a kashe babu location.

Paper da ya gani a dakin m. Ahmad din ya ciro daga aljihun sa ya bude tare da sake kallon lokacin da jirgin su m. Ahmad din zai tashi da kuma airline din da zai bi.

Wata dabara ne ta zo masa bayan yayi sallan magrib yace a nema masa inda wannan wayan tayi aiki last nan aka fada masa gaban hotel din da m. Ahmad take. Da hanzari yaje ya dauko jummalo tana kallon sa kamar  ta mai duka saboda ya taso ta daga baccin ta mai dadi saide ganin yanda yake ta sauri yasa ta Dan fara damuwa ko wani Abu mai muhimmanci ne ya taso.

Ko da suka je reception na hotel din suka bukaci sanin ko m. Ahmad na ciki receptionist tace wannan hotel din suna da tsauri wajen bada information na client dinsu. Menene alalakar su? M. Salis yace AI m. Ahmad din Dan uwan sa ne kuma ya manta staff ID Card dinsa ne.

Tace saide ta duba in m. Ahmad din yana ciki ta Kira musu shi. M. Salis yace ba matsala a ransa kuwa yace indai mun tabbatar yana ciki sai mu jira a waje har ya fito. Dubawa tayi tace minti 30 da suka wuce yayi signing out.

Da sauri m. Salis ya riko hannun jummalo ya wulla ta a mota suka sake kama hanyar airport Dan shi m. Salis yaso su rike sa tun daga hotel din ne amma da alama sunyi latti toh sai su same sa a can. Duba agogon sa yayi yaga saura awa 2 su tashi Wanda chances din su hadu da shi awa 1 da rabi ne.

Kuma daga inda suke zuwa airport zai dauke su kusan awa 1 Dan haka minti 30 suke da shi idan yayi sauri kenan. M salis yace ma jummalo ta koma baya ta kwanta. Ba musu tayi hakan tana turo baki tace ni AI nayi fushi ma ina cewa ka siya mmn farin abin nan ka ki ka siya min.

Yace kada ki damu zai siya miki a inda zamuje. Tace wa? Bai bata amsa ba saima gyara zaman belt dinsa da yayi tare da godewa Allah a Nigeria babu speed limit. Kunna injun motan sa yayi ya bata wuta yace ki rike kujeran nan gam gam kuma kar kiyi min ihu.

Kawai ya finciki motan a wani gudun da shi kansa bai San nawa yake tafiya ba kila 180 ko 200 Abu daya da ya sani shine yana shan gaban motocin da ke gaban sa ne yadda ake shan gaban napep marasa yin sauri dukda ko babu Wanda yakai yan Abuja bawa titi wuta. KOMIN RINTSI SAI YA HANA M. AHMAD TAFIYA DOMIN SHI YA TAIMAKA MASA YA ZAMA MUTUM.

KAMAR DE YANDA AKA SABA KAR A MANTA DA YIN VOTING DINNAN SABODA SHI KE SA WATTPAD SU NUNA MA WASU LABARIN PLEASE  AYI SHARING DA FRIENDS. GODIYA MARA ADADI GA MASOYA NA.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

YA JI TA MATAWhere stories live. Discover now