Gyada kai yayi ya ciccibe ta ya danna a mota. Yana shiga ya kama kunnenta ya murda sanda Dan kunnenta ya fadi yace ke maiya ki bani kurwata!
Kokarin ture hannunsa ta fara tana no ka sake min kunne na zafi yake min bana son mugunta kuma in ka kara ce min mayya sai na fada ma umma na banza mugu kawai.
Sakin kunnen yayi ya juyo ya kalleta da kyau yace ni kika cewa banza mugu? Share sa tayi tace gaba da kukan ta tare da dafe kunnenta da yayi jajawur.
Kunna Moran yayi ya fincika bai tsaya ko ina ba sai hotel bude kofar motan yayi ya ciccibo ta tare da matse Mata kashi ya wullata mai gadin mukulli motar sa yace ya gyara parking ya bada mukullin a reception.
Ita mur tasha kamar bata jin zafin abinda yake Mata. Kallon kallo suke kowa da abinda idonsa ke fada shi fadi yake duk taurin kanki saj kin bada gari zan kyale ki. Ita kuwa idonta fadi yake ko kashe ni zakayi bazan taba nuna ma ina jin ciwo ba a tare suka saki tsaki.
Kowa na kokarin cinye San uwanshi kai a nesa in ka kalla sai ka dauka kauna ake zubawa bakasan kwarya kwaryar yaki akeyi ba. Yana saka roomcard dinsu tana bada dit ya wani daki kofan ya fada dakin.
Cilla ta yayi a kan gadon sanda bayanta yace kat... Dan motsata tayi taji bayan ya rage zafi ashe kashi da ta Dan goce ne ta dawo saiti hamdala tana gyara kwanciya taji muryar sa yace taso Dan.....ki. Sharesa ta yi ya ce ko ba da ke nake yi ba gwamma?
Mikewa tayi tace wai meye Dan wani jiri jiri take ji. Hannun yasa ya janyo kafarta har sanda ya adana ta da kasa yace maza maza yi kneel down.
Ganin fuskarsa ya tabbatar mata ba da wasa yake yi ba hawa kan kafarta tayi yace haka akeyi a kauyen ku? Ko bakije school bane?
Kneel down me kyau tayi yace daga hannu sama. Kallonsa tayi yace maza maza bude baki tayi zatayi korafi da sauri ya tsuguna a gabanta tare da daura yatsa a bakin ta yace shhhhh! Banason korafi maza daga hannunki sama.
Dagawa tayi Dan rabi haka yace me kyau mana! Zabura tayi saboda yadda ya daka Mata tsawa hakan yasa ta nutsu ta daga hannun tare da rufe ido.
Dan sauke hannun ta sake yi tace okay na gane matsalar daga hannun nata yayi me ya fara balle botir din after dress dinta da sauri ta bude ido tare da rike hannunta tace menene hakan ?
Tsaki yaja yace me kuwa naga rigar ta miki nauyi kin kasa daga hannu me kyau shiyasa. Tace kasan inada hannu ko ? sai ka bari na cire da kaina yace ni zan cire da hannuna. Tace ban yarda ba. Yace nine miji dole kibi Umarni na.
Tace ni kuma nice me jikin kuma nace kar a tabani. Murmushi ya yi yace da jikin da me jikin mallaki na ne ai. Tace toh da jikin da me jikin da mamallakin jikin da me jikin nayi kuma mallakin waye? Yace Allah mana.
Tace correct to kuma Allah yace bayason zalinci ni kuma ga zalinci kana min ita karara tunda kasan naji ciwo a baya na kake min hukunci da ya shafi baya.
Kaga tunda kai ma ka kasa bin umarnin ma mallakin ka me yasa ni zanbi umarnin ka? Yace naji cire da kanki munafuka kawai sai shegen cakwaikwaiwa da zakin baki.
Murmushin cin galaba tayi ta cire rigan. Kunna AC yayi ya kure sanyi kawai ya kwanta ya shige cikin bargo. Kamin kace me hajiyar ka ta fara bari baki na rawa tace ya lud sanyi nake ji ya manna Mata tace ya lud sanyi nake ji. Ganin shiru ba amsa yasa ta Mike tana neman remote din.
A hannunshi ta gani ta dauka yayi bacci yasa ta fara ja a hankali har ta zare tana shirin ragewa yace kina ragewa zaki wanke bandaki.
Tace sasssanyi nake ji. Yace na dai fada miki nazari tayi Dan batason sanyi ko kadan Dan haka gara ta rage ta wanke ban dakin.
Su o'o da uhm uhm har an dauka ya kare toh da saura😝
Ragewa tayi kawai yayi murmushi ya gyara kwanciya sa. Can yaga tana wani lankwashewa ya sauko ya kewaya ta bayan ta.
Hannu yasa ta kwankwason ta ya daga sama ya tokare bayanta yace haka akeyi. A zabure ta bude ido tare da hadiye wani yawu Dan bata tsammace sa ba.
Daura kanshi yayi a kafadar yayi shiru abinsa tare da rufe ido. Kamewa tayi Dan gani take tana yin wani motsin arziki za'a Sami matsala.
Shi kuwa dama da gangan yake Mata Dan yasan lagwan ta. Bata tsammata ba taji yana hura Mata iska a wuyan ta.
Hannu tasa ta rufe yasa hannunsa ya kame duka hannun nata guda biyu ya rike tare da fara tsoran kunnenta. Rau rau tayi da ido tace bana so ya lud Dan Allah. Kamar me bacci yace kinga ni kuma inaso ba ya za'ayi kenan?
Kokuwa ta fara yi masa kamin ta samu ta warce hannunta daya ta mintsine shi. Kamar ice ta mintsina ko motsi baiyi ba yace toh daga taimako sai mintsini? Bari nayi bacci na toh. Komawa gado yayi ya kwanta abinsa.
Yanzu ne, anjima ne shiru shiru bai ce ta tashi ba. Shi kuwa angle ya samu a cikin bargo yana kare Mata kallo yana nazarin yadda akayi take da sura mai daukar hankali dukda kuwa ba irinsa yake so ba.
Kawai yaga tayi masa kyau sosai. Hannu tasa tana jijjiga kafarsa tana fadin yaya lud na gaji, Dan alkah ka barni na huta! Ya lud na gaji.
Tana kaiwa nan ta yanki jiki ta fadi. Da sauri ya Mike ya sauka tare daura kanta a cinyarsa yace ke tsolon rake ! Tsolo, tashi mana banason wasan banza fa. Amma babu wani sautin daya gani.
KAR DE A MANTA A ANTAYO MIN COMMENTS SOSAI DA SOSAI DAN ALLAH
NA GODE ALLAH YA BAR KAUNA TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
miss untichlobanty 💕
26th August,2020.
YOU ARE READING
YA JI TA MATA
Mystery / ThrillerWannan labari me suna YA JI TA MATA shine littafina na uku.... Labarin wani saurayi ne Wanda bashida aiki sai zina, a cewar sa ba laifinsa bane Allah ne yayi sa hariji. Toh hakan ne yasa iyayen sa suka rufe ido sai yayi aure amma fa an gudu ba'a tsi...