CHAPTER 9

1.5K 130 28
                                    

Toh abinda yasa yau tsoron da take masa na yarinta ya dawo sabo harda karu shine.....

Jiya da daddare wajajen karfe Goma na dare ta fito daga wanka a dakinta ta shirya abinta tasa key a dakinta ta kwanta ta kashe wuta ta kwanta kunna wayarta tayi tahau WhatsApp. Messages  dayawa suka sauko na mansura ta bude kamar haka.

"Babe good news! Nawa zaki bani idan na fada miki?" Ganin tana online yasa marakisiyya ta Mata reply da zamu je shopping ni da ku.

Duba beeba tayi itakuma ta rubuta " ranki shi Dade har mansura ta baki babban labarin ko ? Muyi video call naga dadi kikeji ko kuka kikeyi " turo baki  tayi giranta a harde tace wadannan biyun lafiyan su kuwa?

Note:lokacin nan batasan za'a bata class rep ba.

Message taga ya shigo daga mansura kamin ta bude taji an daura Mata hannu a cinya. Da sauri ta mike tana laluman lamp. Kamin ta samu daman kunnawa taji an danneta ruf tare da toshe Mata baki da hannu.

Yace shhhhh yimin shiru shashar banza kawai kunna wuta mara haske yayi Wanda zasu iya ganin juna yace idan kika sake kikayi ihu kinga gidan nan sound proof ne ba mai jinki Dan haka kiyi min shiru.

Tace mmmmmm kwantar da kansa yayi  a kirjinta yana shafa cinyarta yace marakisiyya kike ko ta daga ksi da sauri Dan fata take Allah ya fitar dashi a dakin cikin gaggawa lar ayi abin kunya domin tunda take bata taba hada jiki da wani da namiji ba dukda cewa wannan din yayanta ne.

Dan dariya yayi yace ke uwar jarababbu dena wannan rawar jikin ai naji labarin tsiyarki wajen su mom  ashe kema jarababbiya ce sai anyi magana ki dinga ce min Dan iska ko? Cikin mugun tsoro ta janye hannunsa daga bakinta tace Dan allah yaya lud kayi hakuri ka dagani dukda cewa kai muharrami na ne yanzu mun zama baligai bai dace mu zama cikin irin wannan yanayi ba.

Yace ke uw*ki yi min shiru dalla can shinshinan jikinta ya soma yi kamar maye yace ke sandar rake sabulun wa kika Sato? Me sunan shi? Kuka ta fashe dashi sosai Dan ji take ta jika jikin ta sharkaf.

Kukan da tasa ya saka ya dawo haiyacin sa da sauri ya Mike yace ke k*tmar ub*nki da kike wa mutane kuka nace zan miki wani abun ne ? Toh me ma zanyi dake ne nikam ? jibi fa dubeki Abu kamar babu ba ta ankare ba ya yage Mata Riga ihu ta kwala ta sauka daga gadon.

Dariya yayi harda kama ciki yace what the heck babe me kike boyewa? Ba komai a wajen fa... saboda ki rufa asirin ki yasa kike bazan fankama fankaman Riga kamar limamiyar kauye. Cacumarta yayi ya lika da gini ya turmude fuska kamar bashi ya gama Mata dariyar mugunta ya Narko wata ashar Wanda jinta kadai zaisa maka jin jiri yace toh Dan ub...ki idan kika kuskura ko da wasa kika sake yi min gardama ko fitsara kinsan de nasan lalurar ki toh wa billahil azim ba yaga miki Riga zanyi nan gaba ba.

Yana kaiwa nan ya hankade ta ya fice abinsa yana fito tare da komawa wajen sailuba.

CIGABAN LABARI

Mikewa tayi tana dingisawa ta fice kicibis kuwa tayi da daddy a parlour yana fadin yauwa yarinyar arziki ina yayan naku naga motarsa a waje amma.....bude Bali yayi ganinta shabe shabe yace auta zamewa kikayi a bandaki ? Yi hakuri daina kuka ina ummanki? Nuna kofar dakin tayi ya shiga yana fadin marakisiyya me ya samu me sunanki ne? Hakan yayi sanadiyyar tsayar da fadan da take yayinda sailuba wacce akayi wulli da ita ta fada gefen kafar daddy.

Yace lafiya kuwa? Ya haka zamuyi bakuwa kuma naga kamar akwai tashin hankali anan? Umma dake kuka tace me zance maka ne Alhaji na yaran nan abinsa ya fara fice min aka yanzu ka duba wannan halittar dake gefenka wai kta fa zai aura yarinya sai kace tsatsar fir'auna wallahi in bata girmeshi bama zasuyi sa'anni.

Dukda cewa ba zunubi bane AI sai ya nemi kamila wai ita fa zamu nunawa jama'a muce matar danmu ce. Daddy na kallonta ya dage kafa yana fadin bismillah sai kace yaga najasa ko aljani.

Naira dubu 3 ya zaro a aljihunsa ya mika Mata yana fadin baiwar Allah ga wannan kiyi kudin mota kije gida kinji ? Lud din zaizo ya miki bayani kinji ? godiya tayi yace ba komai Allah yayi albarka ya haskaka rayuwa.

Haka ta tafi tana jin haushin ummi kuma tana yaba kirki irin na daddy. Tana fita kuwa daddy ya dauke lud da Mari. Har haki yake Dan bacin rai yace ban yarda cewa baka da hankali bakasan me kake ba sai yau. Duk dafa maka kafar da nake ina ganin zakayi hankali zakayi hankali bazaka taba yi ba sai kaga dayan fuskana toh ka shirya dama kaman nasan zaka bani kunya. Toh akwai yar Alhaji sabo tun last month muka gama magana yace ko wani lokaci za'a iya daura auren Dan haka nan da kwana 3 zan Aura maka ita kuma billahi in ka sake kuka rabu ko ka zalinci ta toh ka sani tana fita a gidanka muma ka fita daga gidan mu ba mu babu kai.

A tsorace yace haba daddy maganar baikai nan ba fa. Daga masa hannu daddy yayi yace tashi ka bani guri gobe dama kaje ka ganta in akwai abinda suke bukata ka basu sannan in kaga dama karkayi shiga ta mutunci kaji ko?

Yana kaiwa nan yace maman mu ki sameni a daki. Toh kawai tace ta Mike rabi bayanta Dan tasan in ta biye wa lamarin lud sai ta tsine masa ma ba tare da ta sani ba.

Nan suka barshi yayi jungum jungum yana fatan Allah yasa wancan yarinyar tana da fasali sannan wani bari na zuciyarsa tayi sanyi. Shi kanshi yasan baya kyautawa abinda yakeyi amma bazai iya dainawa ba.

Wani lokacin sai yayi tunanin ya zama mutumin kirki kawai sai yaji ya kasa idan ya suna yaga abubuwan da ake bukata kamin ka zama mutumin kirki.

MASHA ALLAH TOH A GAFARCE NI ANAN ZAN DASA AYA.

INA TSIMAYIN COMMENTS DINKU DA VOTES DINKU YAN UWA KUMA MASOYA NA.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

28th July,2020.

YA JI TA MATAWhere stories live. Discover now