Part two

89 8 0
                                    

Typing~~~~📱

*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*

'''(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)

   🌼 *Saboda* *duniya* 🌃

Writing by......
<<<<≤<≤<<<<<<<<<<<<
*Annafie*💗

07051376476

Nafeesa A Guga @ wattpad

*bismillahir rahman  rahim*

Page 3️⃣-4️⃣
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

Ringing din wayar tane ya tashe ta daga bacci.. Ta bude idanun ta addu'ar tashi daga bacci kafin ta janyo wayar takara da kunne bayan ta dauka.. Cikin muryar bacci bai ishe ta ba  tace "hello abbana" daga can abba yace "my daughter wake up is already tym for subhi" ta dan lumshe idanunta kafin tace "ok abba" daga haka ya katse kiran...
Da kyar ta iya tashi ta dauro alwala tafito saeda tayi raka'a tanil fijir kafin tayi sallahr asuba.. Tana idarwa tayi addua,  azkar kamar yanda tasaba daganan kuma takira abba ta gaisar dashi sae takira yaya auwal shima sun dade suna waya kafin daga baya bacci ya dauke ta.....
Wajen karfe tara farida tashigo dakin da shirinta na makaranta ... Sakin baki tayi ganin khadija sae baccin ta take sha hankali kwance..
Ta karasa bakin gadon tana tashin ta da kyar khadija ta bude idanu har yahade fuska ganin farida sae idanun ta ya sauka a kan a gogon dake manne a bangon dakin... Ta waro idanu "oh my god 45 minute to 10 am about to late" a rude take wnn maganar tana kokarin rage kayan jikin ta sann ta nufi toilet. Farida tayi murmushi tana bin kofar da kallo "yar rainin hankali ai da tsiya xaki mun ... Tana fadin haka ta fice domin yin breakfast..
Khadija batawani jima ba ta fito cikin sauri ta shirya cikin baya ta dauko sch bag dinta snn ta fito sanda tafito har farida ta gama breakfast dinta.. Khadija ko kallon inda mutanen gidan suke batayi ba bare su saka ran gaisuwa.. Farida tace kiyi sauri kiyi break kafin lokaci ya kure khadija ta girgixa kai kafin tace "no let's go we're late idan munje zansamu wani abu naci" takai dubanta inda matan gidan suke murya can kasa tace "ina kwanan ku" sakin baki sukayi suna kallon ta itakam ta dauke kai..
Hajiya abida tace "amma yarinyar nan iskan cinki gaba yake mu kike gaidawa a haka"
Hajiya jamila tace "dan ubanta ba dae mu ba uwarki mahaukaciya kika gaisar a haka" farida kam tana jin haka ta fice a parlorn da bata son abinda akewa yar uwar tata.  .
Khadija ta juyo tana kallon hajiya jamila jin abinda ta fada kafin tace "sure" tafada tana watsa mata wani bnxan kallo... Raliya tace "dan uwarki da wa kk kuma ubanwa kk ma wnn kallon... Dubanta khadija tayi kafin tace "da wanda ya tsargu tana fadar haka ta juya xata fita sukaci karo da saddiqa... A fusace saddiqa tace "baki gani ne ko haukar ce ta tashi".. Khadija ta tabe baki tana dage kafada "who knows but bari nafada maki duk wanda ya ganni ya ganki ansan wanda za'a kira da mahaukaci ko ta yanayin magana" saddiga ta cakumo ta "ke nikike fadawa haka" khadija ta fizge hannun saddiqa daga jikin ta kafin tace "hey I don't hv tym for dis so let me pls dama haka masu hankalin suke gsky ina bukatar karin bayani because wnn bashine halin masu hankalin da kike ikirarin kinadashi ba.. But bari nadawo sae kimun karin bayani dan ynx bana da tym dinki  I've very important to do now.  So sae na dawo tana gama fadar haka ta juya ta fice..
Yayinda yan cikin parlourn suke ji kamar su shakarota barnma saddiqa... Raliya tace "wlh yarinyar nan daurin gindin da take samu yayi yawa mu sa'annin tane dazata rinka fada mana magana sae kace farida kanwar mu tanawa ce shekara nawa nabata.... Hajiya jamila tace " rabu da ita ai xata gane kurinta.....
A mota ta iske farida da da salima da aneesa duk sun shiga ita kadae kawae ake jira salima tace "dallah malama kiyi sauri mu kina bata mana lokaci" farida tace "dan Allah kurinka yi wa mutum usuri haba" "to baxanyi yi kema dawani bakin ki kodayake gsky kk fada kinsan mahaukata saeda usuri" salima tafada tana hararan khadija... Ita dae tana jinsu batace dasu kala ba duk da yanda xuciyar ta ke tafarfasa saboda farida da yaya Auwal kadae yasa take dagawa yan gidan nan kafa amma da wlh sae dae su kashe ta a gidan nan baxata iya yarda da cin kashin da ake mata ba a gidan nan....
Har suka isa sch drivern na gama parking ta bude ta fice  ta nufi department dinsu khadija ta bita da kallon tausayi sann tabi bayan ta yayinda aneesa da salima suka rakasu da harara Aneesa tace "ni narasa abinda yake damun farida kan wnn yarinyar" salima tace bar banxa kawae"...
       Fadila na hango ta tarugo ta rungume ta "nayi missn dinki habibtie..." Harsranta khadija tayi bayn ta raba ta da jikin ta "yar rainin hankali ni mushiga dan Allah kafin wnn lecturern ya yaxo ya hana mu shiga.... " taja hannun ta suka shige venue din cike yake ana ta zuba surutu suka samu guri suka zauna suna dan lvr... Har lecturer din ya shigo suka natsu dan basa wasa da karatu
  Karfe daya suka fito bayan sunyi sallah suka wuce capteria dab khadija tace yunwa take ji... Fadila ce tayi masu ordering abincin xasu fara ci knn sae suka ji ance "lahh mufeeda ga sister dinki" juyawa sukayi sukaga mufeeda tare da kawayen ta... Mufeeda tace "ai naganta" daya tace "wlh birgeni take duk tafiku kyau ita ya sunan" a fusace mufeeda tace "to sai me ai kin bnx dan tana da kyau ai bata da asali kuma ki daena cewa sister nace dan mu iyayen mu basu taba hauka ba kuma ansan asalin mu gaba da baya" idanun khadija suka cika da kwalla da sauri fadila tace "pls take heart kar ki biye mata ki nuna mata ke me hankali ce.. Khadija ta sauke ajiyar zuciya tana goge hawayen ta  kafin ta tashi ta fice daga capteria din fadila tabi bayan ta.. Abincin da basu ci ba knn  mufeeda ta bisu da harara kafin tayi tsaki yayinda frnds dinta suka bita da kallon mmki..
Can wajen wata bishiya khadija taje tasha kukanta  fadila bata hana ta ba dan tasan she's hurt....
Ranar har suka gama lectures khadija batada walwala da wunya na dawainiya da ita..
Farida taita tambayar ta a mota abinda yasaka ta damuwa amma bata tace da ita kala ba... Aneesa tace ke kam sai kace mayya ana yakiceki amma baki gani" farida tace "ina ruwanki" Aneesa ta tabe baki" babu wanda ya sake magana har suka iso... Khadija ji tayi duk wata damuwar ta takau ganin motar Abban su da sauri ta fito tana murmushi kafin ta ruga cikin gidan suma sauran aneesa da farida da murna suka bi bayan ta dan sune kadae sukayi lectures din yamma dan sauran duk sun dawo gida.....
A main parlor ta iske Abban nata xaune da dukkan mutanen gidan idan ka cire yaya Auwal  da gudu ta fada jikin sa da rungume sa tana fadin "Abbana I miss you" yayi murmushin sa na manya tare da bubbaga bayan ta "mamana i miss you more  ya studies" batare da ta dago ba tace "Alhmdllh Abbana how's 'ur journey" "lpy qlw mamana" hajiya jamila da take ji kamar ta shakota tace "to sai ki barsa ya huta ko" "aa maman yara barta mana itama din ai a gajiye take mamana tashi kije kiyi wanka kiyi sallahr magrib daganan sae kixo muci abinci ko" Abba ya fada
Ta gyda masa kae tana murmushi tace "to Abbana" kafin tayi hanyar part din ta yayinda kowa a parlorn ya bita da harara kasa kasa .. Su Aneesa ne suka shigo suma suka rungume sa suna murnan dawowar sa.,.
Bayan anyi sallah kowa ya hallara a dinning aka zauna xaman cin abinci khadija na kusa da Abban ta rabon da taxauna taci abinci lafiyayye tunda abbanta ya tafi dan ko a sch bata iya cin wani abincin kirki.. Bayan sun kammala cin abincin aka fara  labari dan abba mutum ne da yake bama iyalansa lokacin sa daya bayan daya kowa ya fara wuce wa dakinsa domin yin bacci khadija kam tuni tayi bacci a jikin abban ta sae da kowa yata fi ya rage saura matansa da khadija... Hajiya abida ce tace "ita wnn baxa ta tashi ta tafi daki bane" abba ne ya fara tashin ta "mamana tashi muje na kaiki ki kwanta" "kai alhaji  kabarta ta tafi da kanta mana sai ka rakata saikace wata karamar yarinya" Abba baibi ta kan hajiya abida ba ta kama hannunta suka nufi dakin ta sae da yasaka tayi alwala  Snn ta kwanta yy mata adduar snn ya fito .  .
Su hajiya suna nan inda ya barsu zuciyar su kamar zata fito.... Hajiya jamila ce tace "gsky alhaji kana shagwaba yarinyar nan shiyasa take abinda taga dama" duban ta Abba yy kafin yace idan bnyi mata ba waxae mata duk duniyar nan bata da kowa sama dani nine uwarta nine ubanta" Hajiya jamila tace "wato kana nufi mu nan duk ba iyayen ta bane knn" "ai baku dauke ta a matsayin diyar ku ba kuma  daga yau kar wanda ya kara kokarin shiga tsakani na da diya ta" yana gama fadin haka ya wuce part din sa suka bisa da kallo baki sake.. Jamila unman yara anya yarinyar nan bata bin malamai.. Abida tace kema dae kin gani....
   Kamar a mafarki khadija taji muryar yaya Auwal yana fadin "wake up habibtie is tym for subhi" da sauri ta bude idanun ta tana sauke su a kansa ta rungume sa cikin murna "yaya na yaushe ka dawo" "jiya da daddare kuma lokacin kinyi bacci and nasan idan na tasheki xan hadu da fushin abba, ynx dae ba wann ba tashi kiyi sallah kinji" ta gyada masa kai yy mata peck a goshi snn yace saina dawo" yana fadin haka ya fice ta bisa da kallo cikin murnar dawowar sa.... Tana gama azkar ya Auwal ya shigo ya duka gaban ta. Tace "good morning yaya na" yaja chic dinta morning kin tashi lpy" "Alhmdllh"  "Ok gud karfe nawa kike da lectures? " tace "9 to 11"
Yace "ok ynx muyi karatu ko" ta gyada masa kai kafin ta tashi ta dauko qurani suka fasa karanata wa sae wajen saven ya wuce dakinsa domin yayi wanka itama wanka ta shiga bayan ta fito tayi shirin sch. Snn tafita domin yin breakfast...
A parlor ta iske dukkan ilahirin gidan  zuwa tayi ta gaisar da abba ya amsa kicin sakin fuska sae ya Auwal shima cikin sakin fuska akasin su mama da umma da suka amsa da a dakile... Kusa da yaya Auwal taje ta zauna... Abba yace "wata yaya ya dawo an gujeni ko" kafin tayi magana yaya Auwal yace "Abba ai tafi sona" Abba ya hararesa  "kataba ganin wa yafi mahaifi" yaya Auwal yace "bade a shiga tsakanin wa da kanwa" hajiya abida ce tace "kai xaka ci abinci ko surutun bnx xaka tsaya" Abba ne ya kalleta kafin ya tashi yana duba agogon hannun sa ni xa wuce sae na dawo" duka sukayi masa a dawo lpy" ya fice hajiya abida ta dubi Auwal "kai kaga ka kiyaye ni baxabar shiga shirgin yqrinya nan mai kama da aljanu ba ko... Ko kannen ka kuka fito ciki daya baka kulawa dasu kamar wnn da ko asali bata dashi" "haba umma indae har a kira khadija da mara asali toni ma banada shi tunda da uba ake ado kuma wanda ya haifeni shine ya haife ta kuma... " "dallah rufemun baki dan ubanka idan tana da asalin uba to na uwa fa wlh ka fita ido na"  umma ta katse sa tashi yayi tare da kama hannun khadija ya dauki sch bag dinta suka fice   farida ma bi bayansu...
Saddiqa taja tsaki "wlh umma narasa abinda ke damun yaya da farida" umma tace "wlh kau nide Auwal bai biyo ni ba" hajiya jamila tace "ai ni ma farida badan a gida na haifeta ba sae nace musanya aka mun" "wlh kau mama" cewar Raliya....

Nasan kun kosa kuji lvrn khadija?  don't worry mu hadu a next page ......

*#vote*
*#share*
*#comment*

✨✨✨✨
*Nafeesa A Guga*

SABODA DUNIYA Where stories live. Discover now