Part thirteen

55 4 0
                                    

Typing~~~~📱

*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*

'''(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)

   🌼 *Saboda* *duniya* 🌃

Writing by......
<<<<≤<≤<<<<<<<<<<<<
*Annafie*💗

07051376476

Nafeesa A Guga @ wattpad

*bismillahir rahman  rahim*
Page 25⏩25
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
Wani kallon sama  da kasa kausar  tabi khadija dashi tace "malama bani hanya na wuce how dare you zaki rinka questioning dina... Juya wa khadija tayi tana fadin "wacce ta isa" kausar ta shigo tana wani harare harare "ai baki isa din ba kuma kema kinsan nan yafi karfin ki dan very soon zan shigo gidan nan dan prince bai dace da ke ba saboda basarake sae basarake talaka kam sae kallo" wani murmushi khadija tayi kafin ta samu kujera ta zauna ta harde kafafu "kaji karancin ilimi ko zaki iya gayamin ayar da Allah yace basarake sae ba sarake ko kuma hadisi.. Shiru Kausar tayi tana kallon ta. . dariya khadija tayi "kallon fa ko baki zo wajen ba kokuma aiki da ilimine bakiyi basaraki ya.. Oh na manta ashe fa ba diyar sarkin bace karere ce tun kaka da kakanni ... and kuma da kike cemun talaka kin ganni a yunwace ne ko cemaki akayi babana ya kasa ciyar ni ne ko ya kasa saka ni a makaranta ko ilimantar dani kije gani mahaifina yana iya saya min duk wani abunda nake so komin tsadar sa domin shida kafafunsa kuma ina alfahari da hakan ke kuma fa sai izza  mara anfani dunda nide naga sarautar ba'a hannun ku take ba kina zaune ne kawai a masarautar.. " kanta Kausar tayi "ke how dare you da zaki rinka fada mun magana" "hey are you out of your sense" muryar Ammar ta dakatar da ita dan yana tsaye saman stairs yana kallon duk abinda ke faruwa   Juya dukkan nin su sukayi suna kallon sa.. Kausar ta fashe da kuka tafara hawa stairs din har ta kai tsakkiya ya dakatar da ita tsayawa tayi tana goge hawaye  "Step down" ya fada da sauri ta dago tana kallon sa fuskar nan tasa a daure ganin haka yasa ta sauka babu shiri shima saukowa yy.. Cikin kuka ta fara fadin "prince wae kaji abinda take fada...  " "get out" kallon sa tayi.. Zata kara magana yace "I said get out" jiki a sanyaye ta juya  sae da takai bakin kofa taji yace "look" juyo wa tayi yace "as from today don't ever step in your legs here without my permission or her's ya nuna khadija.... If not. Hmmm" ficewa tayi tare da banko masu kofar bai ko kalli inda khadija take ba ya haye saman sa....
Khadija ma saman ta haye xuciyar ta fess dan wlh bata jin zata dauki wani cin kashi dan kawae  ita da jinin masarauta bace..  ta dauki wayar ta tana kiran farida wayar a kashe ta juya akalar kiran takira husna buga biyu aka dauka "hello lil sis" cikin murna tace "yaya na" "hummm ai nayi fushi kawar ki kawae kk sani ni an manta dani idan bani na kiraki ba baki kirana" langwabar da kai tayi cikin marairaicewar murya tace "yaya ba haka bane" yace "to na hakura kar nasa kiyi karya.. yarima ya dawo ko?"."eh ya dawo jiya" "to kice ina maku barka da xuwa" kafin tayi magana taji muryar husna nacewa "hayatee muje ka tayani girki tunda baxaka bani wayar ba" kwalalo idanu Khadija tayi. Sae kawae taji ditt an kashe wayar shegewa tayi da dariya   su yaya za'a shiga kitchen.. Saeda tayi dariyar ta mai isarta snn ta kira Abban ta da big dady sun dade suna waya.. Kafin ta kashe ta kwanta tuni bacci ya dauke ta...
  Da kuka kausar ta isa part din dada duk ta tsallake su walid dake wajen... Hankali tashe Dada ke tambayar ta "meyafaru bigewa kikayi ne.. Kiyimun magana mana" cikin kuka take fadin "umma ba waccan talakar matar tasa bace taita zaki na tana cimun mutunci har da wani cewa bana aiki da illimi kuma wae ai ko a masarautar ma likani akayi" "ita waccan yar tsakuwar ce ke maki haka kanne na nawa kikayi da ita?.. to shi Aliyun me yace ko baya nan...  Kausar ta kara fashewa da kuka "shima cimun mutunci yy harda cewa kar na kara zuwa part dinsa sae shi ko ita sun bani izini" har Dada xatayi magana sae ta kula dasu walid da sameera dasuke ta dariya.. Daure fuska Dada tayi "wato ku baku da kishin yar uwar ku ko kuna ganin abinda waccan banzar ta mata shine har kuke dariya ko" cikin dariya sameera tace "to umma mai ya kaita kode ni da Rahma mukaje part din Yaya koromu zaiyi balle ita ya Walid ne kadae zae shiga yasha lallai shima ynx saeda dalili tunda yana da mata ita fa dataje dan taci..."    Rufemun baki bnx kawae ku fita ku bani waje baku da wani amfani suna fita ta juyo tana huci sae kaiwa da kawo wa take takulafa idan batayi da gaske ba wnn yarinyar ita zata fara juya gidan nan tun ba'a je ko'ina ba Ammar ya fara bata damar wulakanta mutane inaga abu yy nisa ace har ta samu ciki .. 'Kai dole nasan nayi saena halakasu gaba daya dan inaji ina gani mulki baxae subuce daga hannu na ba matsalar ya iya taku amma idan tasan wata ai baisan wata ba"
       *******       *******
Khadija bata tashi daga bacci ba sae wajen 3 da sauri ta dauro alwala tayi sallah snn tashiga wanka.. Tana gama shiryawa taji an fara knocking hijab ta saka da sauri ta sauka ta bude kofar.. Abinci ne Aunty fati ta aiko masu dashi karba tayi tana godiya kafin tace "kice dan Allah ta barshi haka karta kawo da dare zan girka da kaina" kan baiwar a kasa tace "an gama ranki ya dade zan isar da sakonki ga gimbiya".. Rufe kofar tayi ta shigo "wa kike tunanin zaici jagwalgwalon ki" da sauri ta juya inda take jiyo muryar sa dan ita Sam bata ganshi ba xaune ta gansa yana danne dannen sa a  laptop kamar bashi ne yy maganar ba.. Tabe baki tayi ta juya ta nufi dining ta aje snn ta nufi stairs yace "kee" juyo wa tayi tana tura baki yadago yana kallon ta "badake nake magana ba" kamar zatayi kuka tace "na'am" duban ta yasake yi "ni kk tura ma baki" maida bakin tayi amma kamar xata fashe da kuka maida hankalinsa yy ga system dinsa snn yace "xonan" tsorone ya kama ta amma sata dake tana tsuke fuska ta matsa inda yake batare da ya kalleta ba yace "bakiji tambayar dana maki dazu ba" tura baki tayi "to mekace" dagowa yy yana kara kallonta ganin itama fa a kwai taurin kai.. Bige bakin yy tayi saurin saka hannu ta dafe harta fara kwalla "oh kuka ma kike yi ko zaki bani amsar tambaya ta ko saenayi ball dake" "kamar xatayi kuka tace "to dawane bakin zanyi magana bayan ka bige bakin" dan waro idanu yy a ransa yace lallai ma yarinyar da rasa abinda zaice mata yy dan shi bai fiya son wayan magana ba can yace "xan mare ki idan baki bani amsa ba" ganin yanda ya hade rai ya tace "srry amma me kace na manta" sakin baki Ammar yy ganin yanda take wani raina masa hankali "ke ina wasa dake" girgixa kai tayi kamar xatayi kuka "kinaso kiyi tsallen kwadi" da sauri da girgiza kai a tsorace dan sae ynx ita tama tuna cewa shi soja ne bakaramin aikin sa bane ya nakada mata duka.. Ganin ya wani hade fuska kamar hadari yasa tace "to bana iya girki ba tun a gida kuma ba jagwalgwalo nake ba" kallon ta yy da kyau "ok ashe kinji abinda nace shine kika tsaya raina min hankali I have to punish you sae kin fada mun idan ni sa'an kine" fashewa tayi da kuka zata fara bashi hakuri yace "shiiii 🤫 hold all your hakuri zasuyi maki amfani.... " kafin ya karasa yaji wayar sa na ringing daukowa yy ganin mummy ce yasa ya dube ta fuska a hade yace "hadiye kukan ki" tsit kake ji ya harareta kafin ya daga wayar "Assalamu alaikum mummy na".. shiru yy tana magana can yace "Alhmdllh"..." Yeah mum"... "She's fne"... "She's here with me"... "Ok mum" kallon Khadija yy yana boye wayar "idan kikace wa mum there's something wrong ko.. Ya cije lips dinsa snn yacigaba saena cire maki hakora and ki gyara yanayin muryar ki" gyada masa kai tayi tana karban wayar murya kamar zata fashe da kuka tace "hello mummy" sakin baki Ammar yy yana kallon ta.. Baji abinda mum tace ba yaji khadija tace "Bashine ya bugar mun baki ba kuma bn masa komaiba and the lips are still paining me" ta karashe maganar kamar xata fashe da kuka Ammar kau waro idanu yy yana kallonta gaban sa na faduwa  cije lips din sa yy yana tusa duka hannayen sa cikin lallausar sumar sa dan yasan yau ya bani wajen mum dinsa... Wayar yaga ta miko masa "gashi tace nabaka" yana karbar wayar ya yakashe snn ya kalleta fuska daure "ke ni xaki hada da mum dita ko" waro idanu tayi "lahh tambayana fa tayi". Wani kallo ya sakar mata wanda saeda yan cikin ta suka kusa kadawa kamar zatayi kuka tace "nifa bn iya karya ba Abba da ya Auwal sun hanani" ta fada tana niyar tafiya "keee did I say you go" ta girgixa masa kai tana dake wa amma da kagan ta kasan a tsorace take.. Cikin tsawa yace "xona... " ai bata bari ya kara sa ba ta ruga a dariii ta haye step din ji kake gab ta rufo kofa harda saka key... Bin hanyar yy da kallo  yar kara ma da ita sae taurin kai ga kuma tsoro...wayar sa ya dauka ya fara dialing numbar mummy snnn ya bude kofar ya fice yana kara wayar a kunne....
More comments more typing... ✍️
*#VOTE*
*#SHARE*
*#COMMENTS*

✨✨✨
*NAFEESA A GUGA*
😍😍😍😍😍😍😍

SABODA DUNIYA Where stories live. Discover now