Part twelve

49 4 0
                                    

Typing~~~~📱

*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*

'''(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)

   🌼 *Saboda* *duniya* 🌃

Writing by......
<<<<≤<≤<<<<<<<<<<<<
*Annafie*💗

07051376476

Nafeesa A Guga @ wattpad

*bismillahir rahman  rahim*
Page 23⏩24
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
Da asuba da ya tashi saeda ya leko bedroom din jin karar ruwa a toilet ne ya tabbatar masa da ta tashi.. Wucewar sa yy masallaci da hanzari jin an fara sallah ...
Tana idar da sallah ta dauki qurani ta fara karantawa,. Tana gama kiran aunty fati ya shigo wayar ta... Hello Hanan" a hankali ta amsa da na'am ..nasan ya fita masallaci don't bother 'ur wajen hada  breakfast zan ai ko maku dashi but wajen 10 ki shirya zakuje gaisar da maimartaba a fada da Dada" saeda gaban Rahma ya fadi da kyar ta iya amsawa da to....
Bayan sun gama ta tashi ta kara gyara dakin ta sann ta sauka kasa har masu gyara gurin sun zo har kasa suka xube suna gaishe ta da fara'a ta amsa tana cewa su tashi... Tashi sukayi suna cigaba da aikin su itama tana tayasu bude kofar akayi Ammar ne ya shigo... Gaba dayansu xubewa sukayi a wajen suna gaishe sa kamar zasu shige kasa hannu kawae ya daga masu yy hayewar sa sama khadija ma ko kallon inda yake batayi ba kamar yanda shima bai kalleta ba tacigaba da saka turaren wutar da take suna gama gyarawa a kayi knocking budewa akayi.. Baiwar aunty fati ta shigo rike da flacks har kasa ta zube tana kwasar gaisuwa wajen khadija ta amsa mata da fara'a.. Mika mata flacks din tayi snn ta mika mata wayar hannun ta gashi zakuyi magana da gimbiya fati karba tayi ta kara a kunne ganin wayar on call take. "Hello aunty" "hello Hanan ga tea din yana sha duk safiya bayan ya dawo sallah idan kuma zaije motsa  to idan ya " "ok " Khadija tafada daganan ta kashe wayar ta mikawa baiwar ta dauki flacks din tayi saman stairs dashi... Sai da ta shiga bedroom din ta ta dauko ninkakken hijab sai kamshi yake ta saka snn ta fito... A bakin kofar bedroom dinsa ta tsaya gaban ta na dukan uku uku tafi minti biyu kafin ta fara knocking..  Shiru ba'a amsa ba kusan sau uku har ta juya zata koma sae kuma ta dawo.. A hankali ta tura kofar ta shiga wani sassanyan kamshine ya bugi hancin ta dan lumshe idanu tayi kafin ta bude tana bin dakin da kallo ko ina tsaf kuma komae na dakin mai kyaune bata ta kalli ko ina a dakin amma bata gansa ba hakan yasa ta aje flacks a saman wani karamin table da tagani a dakin juyawan da zatayi ta hango sa kwance cikin wata katuwar teddy pink mai kamar kujera  ya rufe da cream colour din blanket kyakkyawar fuskar sa ce kawae a bude.. Idanun sa a lumshe..samun kanta tayi da kallon sa kamar karta dauke kanta dan kyawunsa yy bala'in tafiya dashi.. "take up your eyes on me" ya fada batare da ya bude idanun sa... Waro idanu tayi  dan duk a tunanin ta bacci yake. Sai kuma ta tura baki ta juya zata fita "hey come back" dawo wa tayi tana daure fuska.. Tashi yy zaune batare da ya kalleta ba yace "who will serve the tea" komawa tayi ta dauko flacks din tare da cup taxo ta duka ta zuba masa snn ta mika masa tare da fadin "Ina kwanah" karba yy batare da ya amsa gaisuwar ta ba... Muryar sa can kasa yace "wash the toilet" dan kallon sa tayi ganin kamar bada ita yake magana ba dan tea dinsa kawae yake sha ganin bashi da niyar yin magana yasa ta mike ta nufi toilet din ya bita da kallo.. Saida ta tabbatar ta wanke toilet din fess snn ta fito lokacin har ya gama shirin sa na wanka .. ganin haka yasa ta koma saeda ta hada masa ruwan wanka snn ta fito zaune ta same sa saman kujera..  A hankali tace "nagama" "tnx" yafada snn ya shige dakin ta fara gyarawa duk da ba wani datti yy ba saeda ta gyara ko ina snn ta saka turaren kamshi har ta gama bai fito ba ficewa tayi zuwa dakin ta itama wankan ta shiga ta fitowa taji ana mata knocking .. Hijab ta saka tazo snn taje ta bude Ammar tagani tsaye wasu kaya ya mika mata "kiyi amfani dasu  and the breakfast is ready xaki ynx ko sae mun dawo daga fada" "sai mun dawo" tafada tana karban ledan kayan  komawa yy dakin sa itama taje ta fara bude kayan.. Na sarauta ne daga ganin su kasan masu tsada ne sae kamshi suke bayan ta gama shafa tayi simple make-up snnn ta feshe jikin ta da turare . ta dauko kayan ta fara kokarin sakawa wa dan ranar nan ta kula da yanda aunty fati ta saka mata .. Da kyar ta samu ta iya saka kayan sann ta dauko alkyabar tana kokarin sakawa Ammar ya shigo shima Cikin shiga ta alfarma kayan sun amshe sa sosae daka gansa kaga basarake kayan kalar nata ne..  ya zauna ganin yanda take ta fama da ita yasa yace "zo" a hankali ta karasa inda yake ya mike ya gyara mata alkyabbar ta zauna das a jikin ta kayan sunyi bala'in yi mata kyau yana gama saka mata kayan ya juya ya nufi kofa tabisa da kallo har ya bude kofa bata motsa ba.. Dan juyo wa yy "jira kike nace ki taho" kasa tayi kafin ta karasa inda yake gaba yy tana binsa a baya har suka isa bakin kofar kasa ya jira ta suka jera snn suka fita sunyi kyau sosae da ka gansu sae ka kara kallon su sunyi kyau da ka gansu kaga beautiful couples.. Suna fita aka fara take masu baya ga motoci nan dayawa cikin daya daga cikin motocin Ammar ya bude mata ta shiga shima ya zagaya aka bude masa ya shiga suka fara tafiya a bakin fada suka tsaya daga nan suka bude suka fita ya zagayo ta inda take suka jera. Babu shiri taji lallausan hannun sa cikin nata da sauri ta kalle sa shi ko kallon ta ma baiyi ba ya wani tsare gida fuskar sa babu alamar ya taba dariya tafiyar sa kawai yake hannun ta cikin nasa fadawa sai take masa baya suke suna masa kirari amma ya wani faske kamar baima san sunayi ba duk inda suka gifta indae akwae bayi a wajen sae sun zube suna kwasar gaisuwa.. A haka har suka isa fada.. Nan ma bayi da fadawa gaisuwa suka farayi suna masa kirari da barka da xuwa kan khayrah a kasa duk kunya ta isheta rabon ta da sarki tun ranar da aka daura auren su.. A gaban sarki suka xube suna kwasar gaisuwa sarki ya amsa cikin farin ciki ganin yaran nasa Khadija dae ta kasa dago kanta.. Murya Baba Rashid taji yace "diyata khadija" da sauri ta dago kanta tagansa zaune gefen maimartaba cikin kaya na alfarma... Kanta a kasa ta gaisar dashi ya jinjina mata kai tare da saka mata Albarka... Basu wani jima ba suka tashi bayan an saka masu albarka.. Shashen sauran yan uwa suka shiga wasu zasu tare su hannu biyu da murna wasu kuma bata kai ciki ba .. Dan wasu daga cikin dangin maimartaba gani suke Ammar bashine ya cancanci zama yarima ba tunda mahaifiyarsa ba yar asalin masarautar bace masarautar wata kasa ce.. Gani suke kamar walid yafi dace wa duk da shine karami  tunda shi mahaifiyar sa haifaffiyar masarautar gadanga ce.. sashen Dada shine karshe tana xaune a parlor tare da bayin ta sallamar su tayi snn ta gyara zama tana washe baki" a hankali yace "umma brk da hantsi mun same ku lpy" ji take kamar ta shakosa amma a zahiri saedae saeta murmushi brk da isowa Aliyu ya hanya" jinjina mata kai yy batare da yace komai ba.. Khadija ma ta gaishe ta ... Amsawa tayi tana dan murmushi.. Dada tace "tun jiya nake tasa ran shigowar ka har abinci na saka kursum tayi maka jiya ko baccin kirki batayi ba"  Shide baice komai ba kursum ce tashigo dakin da murnar ta "my prince tun jiya nake ta sauraren ka har dinner nahada maka baka zo ba how was your journey" mikewa yy tare da kamo hannun khadija snn yace "fne" ya dubi Dada "umma mun barki lpy" sakin baki kursum tayi sae kuma can tace "prince come and have breakfast" "dan juyo wa yy ya kalleta "wnn ba hurumki bane na matata ne" daga haka ya juya ya kama hannun  khadija suka fice" kursum kamar xatayi kuka tace umma wae sai yaushe zaki karkato mana da hankalin sa dan na kula wnn matar tasa baxatai wahalar jan ra'ayinsa ba  duba fa tun ba'a je ko ina ba kuma ni wlh baxan iya rabuwa dashi ba wlh" umma ta rungume ta tana share hawayen ta "karki damu nan da kankanin lokaci zan karkato da hankalin sa gareki zae dawo sae abinda kk ce wani abu kawai nake jira"  kursum ta rungume ta da murna yayinda Dada a zuciyar ta take tunanin hanya mafi sauki da zata halakar dashi gaba daya...
.. Suna isa part dinsu kowa ya shige dakin sa rage kayan jikinta tayi snn ta fito gurin breakfast ta nufa ta debi nasa ta haye sama takai masa yace "tnx" fito wa tayi tana mmkin halinsa dan ynx bata jin haushin yanda yake mata magana  domin kau ta kula nature ne tunda kowa ma yana masa haka.
Saeda tagama breakfast dinta tsaf snn ta kwashe  kayan ta kai kitchen snn ta wanke ta fito zata haye sama taji ana knocking zuwa tayi ta bude dan a tunanin ta Rahma ce amma tana budewa sai taga kursum tana ganin Khadija ta wani hade fuska.. Itama Khadija hade fuskar tayi tace "yes?"
More comments more typing... ✍️
*#VOTE*
*#SHARE*
*#COMMENTS*

✨✨✨
*NAFEESA A GUGA*
😍😍😍😍😍😍😍

SABODA DUNIYA Where stories live. Discover now