Typing~~~~📱
*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
'''(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)
🌼 *Saboda* *duniya* 🌃
Writing by......
<<<<≤<≤<<<<<<<<<<<<
*Annafie*💗07051376476
Nafeesa A Guga @ wattpad
*bismillahir rahman rahim*
Page 50⏩51
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
Har lubna ta shiga daki kyakkyawar fuskar Ammar bata bar yi mata yawo ba dukda bacci yake hakan bai hana ta ganin kyansa ba ga ya matukar daukar hankalinta tana hango yanda eyelashes dinsa suka kwanta luf kamar na mace ga gashi da pink lips snn sumar sa mai kyau skin dinsa mai daukar hankali.. A ranta tace "to koma shikeda wnn motar" dan lumshe idanu tayi tace "gsky gayen yy".....
Da daddare anata yin isha'i khadija ta fara jin tsayuwar motoci a kofar gida kida na tashi.... Babu jimawa ta fara jin hayaniyar su maina suna fitowa alamar zasu fita party lokacin tana corridor tana juna ruwan zafi zata hada masu tea.. Taji suna kiran sunan ta.. Fita tayi ta gansu duk sunci kwalliya barin ma maina da taci wata uwar make up kuma bawani kyau ne da ita ba duk cikinsu ba kyauta da lubna sun fi kyau sae wata da bata san sunan ta ba amma sauran duk sae a hankali.. Duban wacce kekiran ta tayi me suna aziza tace "gani" sakin baki sukayi suna kallonta aziza tace "ya naga baki shirya ba ynx zamu fita fa" girgiza kai khadija tayi "no kuje kawae ni baxani ba bacci xanyi" da sauri maina tace "why?.. Mufa ynx mun xama yan uwa kidena baya damu indae kina tare damu baki da wata damuwa common jeki shirya" da mmki take kallon su sae kace ta bude baki tace masu bariki ta shigo.. Kafin tace wani abu saega kyauta da lubna sun fito suma sunci kwalliya karasowa wajen sukayi suna taunar cingum kyauta tace "lpy naga kun tasata a gaba" aziza tace "wae baxata je ba pls kisa baki" kyauta tace "akan ne?.. Ana dole ne pls kubarta tace maku bariki ta shigo ne? Ku kyaleta mana kinga khadija je kiyi baccin ki karki biyewa kowa kinji kanwa ta" tana fadar haka tayi gaba suka bi bayanta lubna ce tace "to me taxoyi meya barota gidan su dama dole tace babu inda zata tunda ta aje wani a daki yana mata komai.." Cak kyauta ta tsaya ta juyo tana kallon khadija sai kuma ta kalli lubna... Ware hannu lubna tayi tace "gatanan ki tambaye ta idan na mata karya" kyauta ta kalli khadija still tanaso ta gasgata hakan... Daki khadija ta shige.. Suma saura suka fice suna fadin dole dama wnn yar yarinyar da motar nan... Tsaye sukabar kyauta tana kallon dakin khadija da ta rufe ta dade a waje snn ta fice...
Gyarawa Ammar kwaciya tayi snn ta dauko cups din da sukayi amfani dasu da plate don ta wanke gidan shiru duk sai taji tsoro da kyar ta fito ta nufi bakin tab tana cikin wankewa taji tafiya a bayan ta da sauri ta juya a matukar tsoraci wata matashiya ta gani a itama rike da cup tayo wajen tap din a tsorace khadija ke kallon ta.. Murmushi ta sakarwa khadija tace "sannun ki" gyada kai khadija tayi da kyar ta iya fadin "dama da mutum a gidan" murmushi tayi tace "ai nima nan nake saedae nida aurena jiya ina wanka sanda kuka shigo" ajiyar zuciya khadija ta sauke dan saiynx ta tuna kyauta tace mata a kwai me aure kuma idan baxata manta ba jiya taga dakin bude... Khadija tace "amma ke meyasa kk zaune anan bayan da aurenki.." Matar tace "wlh wani aikine ya kawo mu nan kuma bamu samu gida ba Amma ba dadewa zamuyi ba..." Gyada kai khadija tayi snn tace "to Allah ya shirye su" matar tace "Ameen.. Amma ke me kikeyi a nan kina yar yarinyar ki" murmushi khadija tayi snn tace "nima ina tare da mijina ne Amma mun kusa tafiya".. "Eyyer Allah sarki ai gidan nan ba nazama bane ni duk cikinsu ma kyauta tafi birgeni har mmkin ta nake duk tafisu kirki gashi duk sunfi tsoranta idan tace eh tofa eh ne" mikewa khadija tayi tace "Allah dae ya shiryesu ni bari na wuce saeda safe" matar tayi murmushi "Allah ya kaimu saedae bansan sunan ki ba" juyowa khadija tayi tace "khadija" "sannu khadija naji dadin haduwa da ke nikuma Hamida amma anace mun maman umar khadija tace "ina yake" maman umar tace yana malunfashi mu yan canne" godiya khadija tayi snn ta shige daki... Har tayi bacci bataji dawowar su ba... Wajen karfe biyu ta tashi tayi tafiloli snn ta fara addu'a tana mika kukanta ga mahallicci akan rashin lfyr Ammar... batayi bacci ba har asuba.. Sae bayan sunyi sallah ne Ammar tasha tea snn ta samu bacci.. Ammar ya bi kyakkyawar fuskar ta da kallo gabadaya tausayinta ya lullubesa gata yarinya karama amma sae hankali.. Tunda aka aura masa ita baitaba bata wata kulawa ba a mtsayinsa na mijin ta amma duk da haka baisa ta gujesa ba a irin halin da yashiga bata taba barinsa da yunwa ko kazanta ba duk abinda tasan yana bukata bata taba gajiyawa wajen yi masa shiba duk abinda tasan yana so ada bata saena masa shiba duk da ynx bashida komai kuma bashi da kowa she never get tired of him ta rabu da kowa nata sbd shi iskar bakinsa ya hura mata .. Gyara kwaciya tayi ta kara matsowa daf dashi batare da tasan tayi hakan ba Ammar ya lumshe idanu yana shakar kamshin ta... Ahaka shima baccin ya dauke sa ..
Kyauta ce wajen zaune saman kujeran rober a kofar dakin ta wajen karfe shadaya tana jiran fitowar khadija dan har ynx hankalinta yaki kwanciya tunda taji maganar da lubna ta fada jiya.. Haka nan kawae taji batama khadija sha'awar rayuwar da suke because the girl look very innocent.. Ganin basuda niyar fitowa yasa ta tashi ta nufi dakin direct ta tura jin kofar a bude yasa ta shiga.. Da sauri khadija dake tuyar arish ta dago tana duban ta kyauta kau cak ta tsaya tana duban Ammar dake zaune saman wheelchair dinsa idanun sa a lumshe.. Kyauta ta maido da dubanta ga khadija... Kashe gas din tayi bayan ta tsame arish din batare da ta dubi kyauta ba ta tura Ammar zuwa cikin snn ta dawo har lokacin kyauta na nan tsaye... Da kyar ta iya kakalo magana tace "khadija zo inaso muyi magana" bata jira cewar khadija ba ta kama hannun ta zuwa dakin su kasancewar yau lubna bata dawo ba ita kadae ce dan su biyu keda dakin.... Da mmki khadija tace "wae lpy" a fusace kyauta tace "kika cemun ke ba yar bariki bace" gyada mata kai khadija tayi snn tace "eh wani abu"... "To wancan dana gani wanene dama knn abinda lubna ta fada gsky ne khadija karuwanci bai kamaceki ba you look very innocent why do you spoil your life at very tender age khadija why? " kyauta ta fada kamar zatayi kuka.. Zaunawa khadija tayi tana duban kyauta lokaci daya taji ta birgeta cikin sanyin murya tace "am not a prostitute" a fusace kyauta tace "to waye waccan" lumshe idanu khadija tayi tace "he is no one but a husband to me" da mmki kyauta ke kallonta khadija ta gyada mata kai... Zaunawa kyauta tayi calmly tace "are you sure" khadija tace "sure" wata ajiyar zuciya kyauta ta sauke wacce har saeda khadija ta kalleta.. Kyauta tace "don't mind I don't know why I really care about you I don't what anything wrong to happen to you I take you as my sister... Amma kuma meya kawoku nan tunda kince mun baki san kowa ba why do you live home ko ba'a san kunyi aure bane shiyasa kuka gudo" girgixa kai Khadija tayi snn tace "aa ko daya hasalima iyayen mu ne suka auren mu bansan sa ba baesanni ba" "Allah sarki menene ya samesa ne naga kamar bashida lpy" cewar kyauta cikin damuwa idanun khadija suka cika da kwall da sauri kyauta ta kama hannunta "am srry bansan hakan zae maki ciwo ba amma kiyi hkr" girgixa kai khadija tayi tana goge hawayen idon ta tace "mu ma bamusan kan ciwon ba kawae mun tashi mun gansa dashine ne rana tsaka snn kuma iyayen sa masu kaunar sa sunki yin komai a kansa ko inda yake basa zuwa ganin yanda ake farautar rayuwarsa ne yasa muka gudu nan wnn shine dalilin xuwan mu nan... " kyauta ma idanun ta yacika da kwalla jikin sanyin murya tace "wane magani yake sha" "suna daki wani likita ya rubuta" cewar khadija kyauta tace "kun jaraba na hausa" girGiza kai khadija tayi... Kyauta ta mike tana zagaya daki snn ta maido da duban ta ga khadija tace "wnn ciwon na mijin ki asirine baya bukatar maganin asibiti" kallonta kawae khadija take batare da tace komai ba.. Ta dawo kusa da khadija tare da dafa kafadar ta tace "ni asalina yar meduguri ce mahaifina ya kasance mai hada magungunan hausa snn yana karyar da asiri nasan wasu daga cikin magungunan kuma na iya hadawa idan baxaki damu ba sae na hada maki inshallahu nan da lokaci kankani sai kiga yaji sauki da ikon Allah..
Da mugun farin ciki khadija ke kallon ta "bata san sanda tace "da gaske" murmushi kyauta tayi snn tace "yau inshallahu zanje na samu abin hadawa a kwae wasu a wajena saina hada maki.. Rungumeta Khadija tayi harda hawayen farin ciki... Snn tace "ngd Allah ya saka da alkhairi.... Amma kamar nawa zan baki... Girgiza kai kyauta tayi karki damu indae dan tanine kar ki bada komai but ki bada 15k sai a siyo wasu a bubuwan da murna khadija tace nagode sosae murmushi khadija tayi snn ta fice...
Kallon ta kawae Ammar Yake bayan ta gama fada mata duk abinda suka yanke da kyauta ba bata boye masa komai game da ita ba tun ranar da suka fara haduwa... Ganin yy shiru yasa ta langwabar da kai tace "plsss mu jaraba mu gani" kasa Ammar yy da idonsa... Kara hawa saman katifar tayi ta kamo hannun sa ya zuba mata idanunsa kamar zatayi kuka tace "idan baka so saina ce ta barshi... Kallon ta yy.. Ita kuma ta langwabar da kai tace "shiknn zance ta barshi" ya dauke idon sa daga kanta... Da sauri tace ka amince" ya lumshe idanun sa.. Wani murmushi tayi wanda ya fito da ainahin kyanta dimple dinta ya lotsa.... Ta runtse hannun sa sosae cikin nata "thanks" daga haka ta mike ta ta dauko kudi 30k ta nuna mai tace bari na bata wnn ya lumshe idanu tayi cute smile dinta snn ta fice ya bita da kallo...
Magunguna kusan kala uku kyauta ta hada masa nasha na shafawa da kuma na wanka sosae khadija ke yi masa amfani dasu yanda ya kama ta snn ta dage da addu'a ba dare ba rana kullum cikin rokon Allah take snn bata karaya ba wajen basa kulawa ko daya bata taba nuna gajiyawar ta a kan hakan ba kyauta na tafi maka mata yanda ya kamata.. Matsalarta daya shine lubna da aziza kullum cikin yi mata maganar sa suke dan tun ranar da suka daura idanu a kansa suka rude kuma har ynx basu san cewa mijin ta bane.. Kuma kyauta ta hana ta koda wasa ta nuna mata hakan... Sae kuma kewar gida da ta ishe ta gaba daya bata jin dadin zaman dakin da suke...Yau suna corridor Ammar saman wheelchair dinsa Khadija kuma na fere dankali sae kallon ta yake dagowa tayi suka hada ido ta dauke kai tana tura baki... Bata Ankara ba taji ta ferde hannu har cikin kanta taji zafin nan dan bata san lokacin da ta saki wata kara ba... "HANAN" Ammar ya kira sunan ta hankali tashe hannu yasa yana gungura wheelchair din da kansa har ya karasa inda take yy saurin kamo hannun yana fadin "what? Let me see".. tuni khadija ta manta da wata yankewa da tayi ta tsaya kallon sa...
More comments more typing... ✍
*#VOTE*
*#SHARE*
*#COMMENTS*✨✨✨✨
*NAFEESA A GUGA*
😍😍😍😍😍😍😍😍
YOU ARE READING
SABODA DUNIYA
RomanceLabarin yana dauke da abubuwan bn mmki.. Labarine akan wadanda duniya ta rufe masu ido sun manta Allah ne mai komai snn yana dauke da salon soyayya mai bn sha'awa.. Zai fadakar kuma ya nishadantar daku