Typing~~~~📱
*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
'''(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)
🌼 *Saboda* *duniya* 🌃
Writing by......
<<<<≤<≤<<<<<<<<<<<<
*Annafie*💗07051376476
Nafeesa A Guga @ wattpad
*bismillahir rahman rahim*
Page 48⏩49🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
Kiran sallahr asuba ne ya tayar da khadija waro idanu tayi ganin ta jikin Ammar a hankali ta fara zare jikin ta dan kar ta tashe sa.. Bude idanunsa yy Tuni ta fara inda inda kunya duk ta ishe ta tace bari nayi alwala sae ta taimaka maka kayi ko ya lumshe mata idanun sa tashi tayi kanta akasa ta shiga toilet tayi alwala snn shima ta shigar dashi shima ita Kuma ta fito ta dauki bottle water daya kasancewar harda shida mult ta dauko katon daya zuwa corridor domin jona ruwa tana cikin jonawa taji tashin mota lekawa tayi daga wadan nan maxan ne da suka zo a motocin jiya ne suka fita da mmki ta sauke labulen snn ta dawo ta fito da Ammar... Bayan sun idar da sallah ta xo ta hada tea cup biyu ta basa ya sha itama ta sha snn suka sake kwaciya wani baccin ne kuma ya dauke su kasancewar da gajiya a tare dasu.. Sae goma da rabi khadija ta tashi shima hayaniyar ce ta tashe ta domin kau harda su kida duban Ammar tayi taga bacci kawae yake ta leka window daga corridor matan jiya ta gani zaune sae shan kida suke suna wanki wasu kuma zaune suke wata kuma na gefe tana suyar dankali tunanin abinda zasu ci take tana son ta fita domin ta kara siyo wasu abubuwan but bata san ko ina ba kuma ita wadan nan matan tsoro suke bata gashi harda gas take son tayi refiling daurewa tayi ta bude kofar tq fita duk suka dago jin an bude kofa dan babu wanda ya kula cewa ba padlock bane a jiki duk da mmki suke kallon ta gurinsu ta nufa tana kakalo murmushi tace "sannun ku ina kwana" kallonta suke kawae can wata a cikin su tace "yawwa sannu" wacce aka kira da kyauta jiya tace "sannu baiwar Allah jiya kika zo" khadija na murmushi ta gyada kai "tabdi lokacin Amma bama gidan nan" cewar kyauta khadija tace "eh" wata tace "barkanki da zuwa ni sunana lubna" murmushi kawae khadija tayi me girkin tace "masha Allah gata kyakkyawa gsky zatayi kasuwa wann ni zan xama babbar kawarta dan nasan ba karamin samu zamuyi ba" kyauta tace "dalla gafara wake take me harka da kana na kana na ai kinsan yarinyar nan ta manya ce ko baki ganta bane wnn hurumina ne dan nafiki sanin mutane" shewa yan wajen sukayi suka hada baki wajen cewa "hakane wnn sarauniya kyauta" kna kyauta ya kara sama tana wani tsuke baki waccan ta dauke kai khadija dae kanta a kasa cikin mmkin su can ta dago kanta tace "ina son xanje kasuwa nayi siyayya kuma bn san ko ina ba" da sauri kyauta ta tsame hannunta a ruwa "kar ki damu kanwata nima can nake son zuwa shirya muje ina da wasu kudi a hannuna idan Siyayyar taki ba mai yawa bace inajin kudin zasu ishemu" mikewa khadija tayi "To bari naje na shirya" kyauta ta mike tace "to bari na shirya nima sae dae kanwata bansan sunanki ba" khadija da har ta fara tafiya ta juyo tace "khadija"...
Har tagama shirin ta cikin abaya ta saka hijab Ammar bai tashi ba... Karasawa tayi saman katifar a hankali tace "yallabai" Ammar ya bude Idanun sa masu haske tace "zanje nayo siyayya tare da wata zata rakani can I go?" Tsura mata manyan idanun sa yy.. Ta langwabar da kai "pls i'll take care we need alot of things" lumshe idanun sa yy tayi murmushi tace "do you need anything before I go?" Dauke ido yy mikewa tayi tare da daukar side back dinta tana murmushi tace "bye" ya bitada ido harta fice... Saida ta dauki gas din snn ta fice... A waje ta hadu da kyauta tayi kwalliyar ta ta kashe dauri tayi kyau abinta khadija ta sakar mata murmushi tace "da nisa ne" "kai da nisa mana ai inaga ma sae mun hau a daedaeta ko na kira wani ya kaimu" girgiza kai Khadija tayi tace "no.. i think we should use the car" ta fada tana nuna motar... Waro idanu kyauta tayi "wae kina nufin ke keda motar nan" batare da khadija tace komai ba ta nufi motar bayan ta bude ta saka gas din a baya snn ta zagaya ta shiga har lokacin kyauta na nan sake da baki bama ita kadae ba har mutanen dake tsakar gidan kallon ta suke har tayi rebose ta zuge window tace "muje ko" kamar wacce kwae ya fashe wa a ciki ta shiga motar wata lubna na ce ta bude masu gate din suka fice.. Khadija ta dubi kyauta da har ynx bata gama yarda cewa khadija keda motar ba tace "ina mukayi" a hakali kyauta nuna mata dan duk bakinta ya gama rufuwa a haka tai ta nuna mata har suka shiga kasuwa....
*******************
Can kau cikin masarauta anyi nema sama da kasa ba'a gansa ba dada kamar tayi hauka idan ta tuna cewa duk wani plan dinta ya ruguje satar hanya tayi kota kan sarkin pada bata bi ba ta nufi wajen malaminta... Kamal kau duk ya tashi hankalin sa kamar bada saka hannunsa suka gudu ba.. Saedae hankalin sa yy mugun tashin jin abinda sarki yace da lvrin batar yaje masa dan sarki cewa yy "ai su ba yara bane daga khadijar har shi Ammar din......
Malam ya dago yana kallon dada da duk ta gama hada zufa yace "sun gudu tabbas amma baxance ga inda sukayi ba dan akwae tsari mai karfi a tare dasu kuma jikin su da tsarki ya nuna mata wata kasa da hoton su khadija ya fito suna tafiya.. Cikin rudani tace "malam ka taimakamin zan baka ko nawa ne domin ka kashe mun su dan banyi tunanin yarinya karama kamar wnn zata iya rusamin plan ka taimaka bana son su Kara motsi daga inda suke su bar duniyar kawae wlh kyautar da zan maka ni kaina bansan adadinta ba fatana kawae subar duniyar... Malam ya kalli hoton su khadija a cikin kasa yana jinjina aikin yy yan binkicen sa yaga hakan ma baxae taba yiwuwa ba dan idan yy wani yunkuri za a samu matsala hakan kawae yasa ya yanke gara yaci kudinta kawae watarana dama ai dole dubun ta ta cika.. yace "an gama" yanagama fadin haka yy wasu yan tabe tabe ya juye kasar snn yace "an gama da babin su babu sauran wani Ammar a doran kasa" jitayi kamar an mata albishir da gidan aljanna nan da nan tacire zobunan gwalagwaln ta ta mika masa ga wnn sauran sae kajini....
**********************
Duk abinda tasan zasu bukata saeda tq siye shi snn duk abinda kyauta ta siya ita ta biya kudin kyauta dai binta kawae take da ido har suka gama wani bracelet ta gani mai kyau ya birjeta ji kawae tayi tanason ta siyar ma Ammar siya tayi ta saka a jaka snn aka saka masu kayan a mota suka dauko.. Kyauta ta saki wata guda da har sae da khadija ta juyo ta kalleta kyauta tace "lallai kice ke da zafi zafi kika shigo wnn motar ai tafi miliyan 20 ke kau wnn kudin duk ina kk same su amma babbanki millonear ne ko.. Kokuma duk a barikin kika same su.... Hankalin khadija na titi tace "ni fa ba yar bariki bace" saki baki kyauta tayi tace "to yar meye mai ya kaiki kama gida kina yar yarinyar ki kima a gidan yan bariki domin nan ko da kike gani duk yan bariki ne daku har hudu daki daya ne kawai na wasu suma mata da miji ne" batare da khadija ta kalleta ba tace "haka nan" kyauta tace "tab lallae kam amma da kin sani kin sani baki baro gidan iyayen ki ba dan wlh nesa da iyaye babu dadi ka da matsalaidan kuma baki dasu khadija kina da kudin kina da hali kiyi auren ki kinda kena da kyau an you're very young tunda nasan ko 20yrs Baki kaiba da kyar ma idan kinkai 19 wlh ynda kike din nan kallo daya namiji zai maki saeta hade yawu nide shawara na baki snn duk yan mata da kika gani din nan karki rinka kula kowa dan zasu kaiki su baro ne... Ita dae khadija batace komai ba amma a kasan ranta mmkin ta take kuma a fahimtar da tayi masu kamar duk itace tantiryar cikin su amma kuma wnn maganar take fitowa daga bakin ta... Har suka isa babu wanda ya kara magana har suka isa tana gama parking su kafito kyauta ta kwashe kayan ta ta dubi khadija tace "if you need any help let me know take me as sister" daga haka ta juya oyoyo mutan gidan suke masu daya daga cikin su tace "lallai ke inaga da zafi zafin ki kika shigo wnn ai saedae a biyo ki" khadija dae batace dasu komai ba ta dinga kwasar kayan tana shiga dasu wata tace bayan khadija ta shiga "kai wnn daga gani a kwae jin kai" lubna tace "kinga barta tayi ai ta can canta kina ganin yarinya kamar balarabiya sae kace ita tayi kanta ga kuma kudi haba barta wlh danice a matsayin ko kallo wlh baku isheni ba... Tabe baki kyauta tayi " kwaji dashi dae" daga hakahaka ta shige daki....
Ammar na shiga wanka ta gyara dakin ko ina ya dauki kamshi.. Bayan ta gama taimaka masa ya shirya ta dauko masa bracelet din nan ta saka masa kallon hannun yy ya dago yana kallon ta itama din shi take kallo kawae saetaga ya sakar mata murmushin sa mai kyau waro idanu tayi kafin tace wani abu taji muryar sa yace "thank you" bude baki tayi tana kara waro idanu tama rasae xata ce da kyar ta fisgo maganar tace "do you just talk" ya lumshe mata idanu ta girgixa kai "no pls talk to me" ta dauke kai yy yana murmushi dan har saeda dimple dinsa ya lotsa ta langwabar da kai kamar zatayi kuka tace "plsss" ga mmkin ta saetaga shima ya langwabar da nasa kan tare da noke kafada... Idanun khadija kamar zasu fito take kallon sa sae kuma ta juya ta kalli gabas tayi sujjada tana godewa Allah ta juyo gare tace "inashaallah zaka samu lpy Allah ya baka lpy" ya lumshe mata idanu.. Ta tura baki "nide kayi magana" lumshe idanun sa yy batare da ya bude ba tashi tayi ta shiga toilet sannin halinsa na miskilanci ba lallai yayi ba amma kuma tana cikin farin ciki...
Indomie ta dafa masu sukaci snn ta bashi magani ya sha ... Tuni bacci ya dauke sa dan harda na bacci a magungunan ... Kayan da tayi amfani dasu ta dauka ta fita domin wankewa .. Ba kowa a tsakar gidan saedae tana jin kara alamar kallo ake tana cikin wankewa lubna ta fito ta zauna kofar daki tana duba mirro tace "Ki shirya anjima sae mu fita dake kiga yanda abin yake a kwae birthday din wani boo din maina da za'ayi a yanda kike ba karamar kasuwa zakiyi ba... Khadija ta mike bayan ta gama tace "kuje kawae ni baxanje ba" daga haka ta shige daki. Lubna ta bita da ido ...
Dan gyara masa Kwaciyar tayi snn ta shiga toilet domin wankewa... Lubna ce ta shigo rike da sauran omon da khadija tayi amfani dashi ta manta bata dauko ba... Bin Ammar ta dungayi da kallon mmki... Khadija ce ta leko jin kamar an shigo. Ganin lubna saeta daure fuska tace "yess" barin ma yanda taga tana ta kallon Ammar din lubna tace "kin var omon kina shine na kawo maki... Khadija ta karba lubna ta kara kallon Ammar tace "kekau ina kk samo wnn sae kace balarabe" daure fuska khadija tayi tace "madam pls get out don't wake him up" juyawa lubna tayi tana kara kallon Ammar snn tace "gsky dole ki ce baxaki fita ba kin aje kamar wnn" daga haka ta fice khadija ta bita da harara snn ta kalli Ammar da yake baccin sa shagala tayi da kallon sa yy mata wani irn kyau...
Manage the little
More comments more typing... ✍️
*#VOTE*
*#SHARE*
*#COMMENTS*✨✨✨✨
*NAFEESA A GUGA*
😍😍😍😍😍😍😍😍
YOU ARE READING
SABODA DUNIYA
RomanceLabarin yana dauke da abubuwan bn mmki.. Labarine akan wadanda duniya ta rufe masu ido sun manta Allah ne mai komai snn yana dauke da salon soyayya mai bn sha'awa.. Zai fadakar kuma ya nishadantar daku