Typing~~~~📱
*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
'''(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)
🌼 *Saboda* *duniya* 🌃
Writing by......
<<<<≤<≤<<<<<<<<<<<<
*Annafie*💗07051376476
Nafeesa A Guga @ wattpad
*bismillahir rahman rahim*
Page 56 ⏩ 57🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
Shine ya fara tashi saida yayo alwala snn ya matso da kusa da ita a hanakali yace "time for subhi madam" bude idanun ta tayi me cike da bacci shi kuma ya fice zuwa masallaci sae da ta fara jona masa ruwan tea snn ta shiga tayo alwala tare dayin sallah tana saman prayer mat tana azkar ya shigo shi da kansa ya hada tea din mikewa tayi tana ninke sallayar ta aje snn ta tafi zata kwanta yace "ain't you take the tea" girgiza masa kai tayi "ni bada yunwa na tashi ba" waro idanu yy kafin yace "to waye ya tashi da yunwar" "ni na kama suna ne" ta fada tana kokarin danne dariyar ta cigaba da shan tea dinsa yy sae da ya gama snn taso zuwa inda take batare da tasani ba taji ya kamo kunne ta "waye ya tashi da yunwa" runtse idanu tayi cikin tsoro tace "nifa bada kai nake ba kawae dae na koshi ne"... Rankwashinta yy tayi saurin dafa kai tana rau rau da idanu nunawa yy kamar bai ganta ba ya juya yy kwanciyar sa tabi sa da harara tana murguda baki....Misalin karfe 10 khadija durkushe tana kokarin hada breakfast Ammar ya shigo corridor din rigar wanka ce a jikin sa dukawa yy kusa da ita kamshin sabulun wanka sa duk ya cika mata hanci... Kallonsa tayi ganin yanda ya mata kyau a hankali tace "ina kwana" shiru yy baice komai ba hakan yasa ta dago suka hada ido tayi saurin yin kasa da nata... Ya tallafo habar ta yana kallon ta kafin yace "morning wife kintashi lpy" cire hannun sa tayi saboda yanda ya sakar mata da kasala da kyar ta iya amsa masa...
Shi da kansa ya dauki komai zuwa daki bayan ta gama saka komai a tray har suka gama breakfast idonsa kyam a kanta da ta dago sae su hada idanu ...... Can dae ta ta gaji ta tura baki "wae ni ka dena kallona"... Ya waro idanu "nida halak dina matata na kalla fa" kamar zatayi kuka tace "nide ka bari banaso" kasaitaccen murmushin sa yy yace "ke ba matata bace" a takaice ta ce masa "ehh"... Still smiling yace "oh eh hakane kuma ashe fa har ynx ban maidake matar tawa ba dake da budurwa duk daya but..." Sai kuma yy wani murmushi tare da kashe mata idanu ... Ya tashi inda cartoon din drinks dinsu suke yaje ya dauko bottle water daya ya haye saman katifa tare da janyo system dinsa yana dannawa itakam sae binsa take da kallo a tsorace kamar zatayi kuka dagowa yy suka hada idanu yace "why the look madam mijin wata fa kk kallo" kasa tayi da kanta jiki a sanyaye ta tashi ta kwashe kayan ta fita zuwa corridor ta dade bata dawo ba dan sae da ta wanke su tass. Snn ta shigo Ammar dae ya bita da kallo kasa kasa kamar yy dariya.. Cutting kid ta dauko tana fara gyara farcen ta har lokacin jikinta a sanyaye yake... Tashi tayi zata mayar bayan ta gama taji yace "zo nima ki gyara mun ya fada ba tare da ya kalleta ba... Saeda ta bisa da harara kafin ta karaso inda yake kafar sa ya nuna mata ta murguda baki kafin a hankali ta dago kafar tabi fararen toes dinsa da kallo kamar na mace kuma babu abinda sukayi tass suke haka dae ta gyara tana masifa cikin zuciyar ta.... Aje system din yy ya mika mata hannunsa batare da yace komae ba.... Shima babu abinda yy tade gyara ne kawae.... A hankali yace "why are you silent" tsuke fuska tayi ba tare da tace komai ba ya kamo hannun ta yana murzawa kafin yy kissing din hannun yace "thanks love"
Dauke kai tayi tana kokarin zare hannuta amma yaki saki saema janyo system dinsa da yy yacigaba da aikin gabansa... Sun dade a haka bai ko dago ya kalleta da bare yaga hararar da take masa... A hankali tace "nifa ina so naje zan siyo fruit sae nama da kayan miya" duban ta yy tare da jan hancin ta "ai bakin kine fruit din" ta dauke kai tana murgude yace "eyeee baga bakin yin murguden" marairaicewa tayi tace "dan Allah" ya maida hankalinsa ga abinda yake kamar ba zaiyi magana ba sae kuma yace "to ammafa tare zamu je dan karki bata". Dariya tayi snn tace "nifa ba bakuwa bace kaine bako saedae na nuna maka Gari. Shima murmushin yy yana rufe system dinsa
YOU ARE READING
SABODA DUNIYA
RomanceLabarin yana dauke da abubuwan bn mmki.. Labarine akan wadanda duniya ta rufe masu ido sun manta Allah ne mai komai snn yana dauke da salon soyayya mai bn sha'awa.. Zai fadakar kuma ya nishadantar daku