Part five

66 7 0
                                    

Typing~~~~📱

*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*

'''(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)

   🌼 *Saboda* *duniya* 🌃

Writing by......
<<<<≤<≤<<<<<<<<<<<<
*Annafie*💗

07051376476

Nafeesa A Guga @ wattpad

*bismillahir rahman  rahim*
Page 9️⃣- 🔟
A lokacin Ya auwal na tare da khadija tace "ya auwal xan bika" dan kallon ta yy ganin yanda ta tashi hankalin  ta kamo hannun ta yy ya xaunar da ita saman gado a hankali yace "kwantar da hankalin ki habibtie  kinga ynx dare yy ki bari sae gobe... " dakyar ya samu ya lallaba ta barsa ta barsa ya tafi shi kadae.. Amma hankalin ta na can tana tunanin halinda wanda aka bige yake ciki...
Ya auwal na isa yaga Abba sae kaiwa yake yana kawowa.   Ya karasa inda yake yace "Abba ya jikin nasa" abba yace "da sauki to"  ya Auwal ya jinjina kai... Sun dade a wajen kafin wani doctor ya fito yasame su.... Ya auwal yace "doctor ya ake ciki" "ku kwantar da hankalin ku yadan samu ciwukane amma ynx mun samu damar shawo kansa ynx yasamu bacci kuma inshallah zai farka cikin koshin lpy" zaku iya shiga ciki" ... Abba ya jinjina kai kafin su shiga ciki inda yake kwance yana bacci kansa nade da bandage.. Cikin tausayi suke kallon matashin dattijon Abba ya lumshe idanu sae ya tuno ranar da yafara ganin matarsa wacce kullum yake kwana da ita yake tashi wacce yakejin baxai taba dena jin sonta a zuciyar sa ba har gaba da asuba.... Abba ya lumshe idanu yana jin radadin mutuwar matar tasa.... Ya Auwal yana kula dashi kuma yasan tunanin da yake yasan har yau akwau soyayyar ummi a zuciyar abba... A hankali yace "Abba ka zauna mana" babu musu ya zauna kafin yace "Auwal je kasiyo kayan tea idan ka dawo ni sae na wuce kai ka kwana dashi" "to Abba" yaya Auwal ya fada kafin ya fice....
Washe gari khadija nayin sallahr asuba ta nufi part din Abba lokacin dawowar sa daga masallaci knn... Sunkuyawa tayi ta gaisar dashi yace "mama na  yana ga kamar kina cikin damuwa" tayi kasa da kanta tace "Abba ya mai jikin nima zan je na gaisar dashi" dan kallon ta yayi yana tunanin ko ya akai tasani can kuma sae yayi wani tunani.. Can yace "kin kwantar da hankalin ki kinji ba wani abu bane ya same sa kuma xakije ki gansa amma bayanxu ba sae anjima ai yau evening lectures ne dake ko" ta gyda masa kai" yace to kibari wa wajen biyu kixo masa a abincin rana" daga can saeki wuce sch kinji" gyada masa kau tayi kafin ta juya zuwa dakin ta.... Ya bita da kallo cikin tausayawa kafin ya girgiza kai ya shige daki..
.... Wajen karfe 8;40 Abba ya shirya zuwa gidab hajjo.. Tunda yafada mata ta kasa kwantar da hankalin ta. Tace "sae taje ta dubo sa babu yanda ya iya haka ta shirya suka tafi..
   Koda suka je mutumin ya farfado har yaya Auwal ya taimaka masa yy wanka ynx ma abinci yake basa... Abba ya dan rissina ya gaishe sa mutumin ya amsa yana dan murmushi.. Abba yace ya jikin" yace "da sauki Alhmdllh sannu da dawai niya" murmushi Abba kawae yy kafin ya xauna .. Hajjo tace "sunnu kaji ya jikin ka" "da sauki ma ai ngd sosae.. " abba bai wani jima ba ya tafi wajen aiki" yaya Auwal ma ya tafi gida domin yy wanka ya kawo su umma su duba sa,. Sae hajjo ce ta tsaya dashi .. Ba'a jima ba sae ga yaya Auwal da mama da umma sai Aneesa suka gaishe sa basu dade ba suka tafi.. Lokacin jikinsa yy sauki hajjo sae Lvr take basa harda yanda Abba ya bige kursum shide jinta kawae yake yana murmushi a ransa kam yana tausawa wnn baiwar Allah da diyarta....
can kau gida hantsi nayi khadija ta  shiga kitchen ta fara masa girki wanda tasan zaiji dadin sa a matsayin sa na mara lpy... Mama ce ta shigo tana kallon ta "ke kuma yau da abinci xaki sch din" dan girgixa kai tayi tana saka flacks din a basket snn tace "aa mama xan kaiwa patience din da abba ya bige ne.. Umma da tashigo parlorn ynx tace "kaji mun wani shishshigi ke meye naki"
Mama ce tace "ya baxata shige masa ba kin manta cewa uwarta ma ahaka aka tsince ta hhhh" "eh hakane kuma" khadija dae batace  komai ba ta dauki basket din tare da dauko sch back dinta snn ta fice...
Driver ne ya kaita har asibitin acan ta iske hajjo da ya Auwal.. Gaishe su tayi snn ta durkusa ta gaisar da patient din ya amsa mata cikin sakin fuska hajjo tace wnn itace khadijar wacce taci sunana... Ya kara fadada murmushin sa yace khadija matso kusa dani.... Kanta kasa ta matsa inda yake yace "ykk ya gida" tace "lpy qlw ya jikin" "da sauki.."
Flakes din abincin ta bude zuba masa ta mika masa ya karba tare da yi mata murmushi snn ya fara ci.. A hankali a hankali yake janta da fira.. Wajen 3:30 ya Auwal ya kaita makaranta... Sann ya maida hajjo gida..
Bayan khadija ta taso daga lectures ita da farida tace drivern ya wuce dasu  asibiti  hakan kau akayi.. basu koma gida ba sae dare...
Washe gari aka basu sallama suka wuce dashi can gidan Abba aka bashi daki...
Kulawa sosae yake samu acan duk da wasu daga cikin yan gidan suna nuna kyamar sa.. Khadija kam mutumin yana birgeta gashi da kwarjini koda yaushe tana inda yake bata damu da tsegumin da yan gidan ke mata ba... Ita ynx matsalar ta usman ne kwata kwata yadena kiran ta a yan kwanakin nan ko ta kira sa baya picking a hankalin ta ya tashi tana adduar Allah yasa lpy.. Gashi hajjo ta taso ta gaba akan tafito da mijin aure kuma bata da wani zabi da yawuce usman din domin har ga Allah tana son sa datsewar karatun tane bata so amma ya ta iya tunda hajjo ta kasa ta tsare tace sae anyi kuma tana da tabbacin zaibarta tacigaba da karatu....
Satin baba Rashid (patience)  abba ya koma ga iyalansa khadija tayi kewar sa sosae dan mutumin a kwai shiga rai da kwar jini....
*******   ******* ******
Shiru khadija tayi tana sauraren hajjo da ta zage sae fada take mata akan ta fito da miji dan dole tare dasu farida za'a hada auren su.. Big dady ne (baban su mujaheed)  yace "hajjo da kin barta duka nawa take ne khadija xata gama karuntun ta da kananun shekarun ta  dukaduka nawa take tunda mijin baizo ba abar... Da sauri hajjo ta katse sa rufe mun baki shekara shataran ne yarinya baka san wadan nan matan uban nata baki cikin samun miji suke mata ba so kake suce tayi kwantae tarasa  mashishini to baxan lamin ta ba nasan bawae samarin ne bata dasu ba itace bata son su sau nawa ina jin hirar su da farida ... Ya Auwal ne yace "hajjo ki kara bata lokaci kila bata samu wanda ya mata bane ko kuma tafi ra'ayin karatun.... " "zaka min shiru koko kar ta samu wanda yy mata din kuma aure dai dana su farida za'a hada na baki kwana ukku ki samo wanda yy maki.. " tana gama fadar haka tashige dakin ta... Khadija ta tashi tana kuka tashige wani daki itama..
Yaya auwal ne da faruk suka bi bayan ta.. Yaya Auwal ya janyo ta jikinsa "kiyi hkr sis ki daure ki yi abinda hajjo tace nasan ba hakura zatayi ba kindae san halinta faruk yace "ina wnn mai sunan dady danaji su farida suna tsokanar ki naga alamar kina sonsa ko" ta gyada masa "eh amma kwana biyu fa yabar kirana" yaya Auwal ya shafi kanta karki damu "common habibtie ki masa usuri ynx dae ki tura masa text akan yaxo ya sameki ko gobe ne sai kasanar dashi kafin lokaci ya kure maki because I knw she mean what she said"... "Kai wlh she mean it dan duk abin da tsohuwar nan ta fada saeta ai katashi" cewar faruk yana dariya.. Suma dariya sukayi  tare da kwantar mata da hankali....... Ranar da daddare ta tura masa text akan yaxo ya same ta gidan hajjo...
... Washe misalin karfe 4 text ya shigo wayar khadija tana dubawa ga mmkin ta sai taga usman ne  Ta karan ta "gani naxo ina waje" murmushi tayi wanda har saeda faruk dasuke tare ya harbo jirgin ta yana dubawa idon sa ya sauka a kan text din ya fashe da dariya tura baki tayi kafin ta kira farida taji ko ta kusa karaso wa yayin da faruk ya tashi yana fadin "bari kiga ni xan farawa hajjo albishir yana gama fadin haka ya shige dakin hajjo.... Ita kuma ta da hijab ta fice tana hararan dakin da yashiga snn ta fice...
A mota ta samesa ta ta dan sauke glass cikin sanyin murya ta masa sallama snn tace "ka shigo ciki mana" yadan girgixa mata kai no baxan shiga ba" ta dan marairaice murya "why... ya kamata kashigo kasha ruwa kuma bayan nan a kwai maganar da nake so muyi" "no ki shigo mota muyi maganar kawae ba sae na shiga ba" "to shikenan bari na kawo maka abin sha" ta fada tare da juyawa zata shiga gida.   Yayi saurin dakatar da ita ta hayar kiran sunan ta... Ta juyo.. Yace "shigo motar muyi magana" babu musu ta dawo ta shiga.   Yace "ina jinki shiru tayi tana wasa da yatsun hannun ta kanta kasa sun dade a haka kafin ta fara sanar dashi  shiru yy har tagama fadar abinda xata fada baice komai ba.. Jin yy shiru yasa ta dago kanta suka hada ido tayi kasa da kanta kafin tace "naji kayi shiru" ya sauke numfashi snn yace "banki taki ba amma ynx ba wann ba meyasa kika boye min ke wacece tuntuni" cikin rashin fahimta tace "kamar ya" yace "humm sae ynx nagane dalilin ki na kinyarda na gabatar da kaina a gidan ku, ashe dama baki da cikakken asali, ashe dama ko lpyr kirki baki da ita kuma kinsani kika fadamin" "a rude tace "kamar ya usman me kk fadi ne haka" ya katse ta "me yasa kike yaudara ta ne meyasa baxaki fada mun ke wacece ba kika ja nafada soyayyar ki wlh nayi dana sani dana yarda na kamu da soyayyar ki..... Cikin masifa  tace "mind ur tongue usman nataba cewa kashigo cikin rayuwa ta have i invite to come into my lpy or did i beg for your love.  Shin dan ba'asan asalin mahafiya ta ba laifi na ne naga ko cikin shege ce ni bani da laifi... Tana gama fadin haka ta fito daga motar shima ya fito... Lallai yau na yarda da abinda ake fada mun cewar bakida cikakken hankali daga fadin gsky sae hawa sama dama ance mun hauka a jinin ku.... Wani lafiyayyen Mari yaji ansakar masa yasa maganar sa ta tsaya.. Farida ce da kara sowar ta knn ta sauke masa shi.... Cikin fushi ta fara magana da ina kallon ka mai hankali ashe kai din mahaukacin jahili ne to kasani kaima ba fin tq kayi ba da yasa Allah ya yika cikin dangi pls kafin ja wulakanta wani ka tsaya kayi tunani kaima a koda yaushe rayuwa zata iya juya mata kunsan me Allah yake nufi da ita ne amma ka tsaya nan gaba sae kayi dana sanin abinda kayi wa yar uwa ta.... Tana gama fadin haka ta ja hannun khadija suka shiga ciki....
Khadija kuka take kamar ranta zae fita ta tabba ta wani ciki nata ne yaje hada mata wnn kullin.... Hajjo na ganin ta hankalin ta ya tashi.. Ta fara tambayar ba'asi da kyar ta samu suka fada  mata... Ai kam tayo waje ko xata gansa sae taga ya tafi ta dawo cikin gida sae masifa take tace ma faruk ya xo ya kaisu gidan abba yau saita cima matan sa mutun ci dan tasan idan ba su bane to yaran su ne...
Zyciyar faruk na kuna ya dauko key din motar sa  yarasa meyasa yan uwanta suka tsane ta haka dan tsabar rashin imani har aure suke son hanata yi....
Can kau gidan abba baba Rashid ne ya kawo masa ziyara Abba ya ji dadi sosae sun dade suna hira kafin baba Rashid yace "a gasky naji dadin karam cin ka Alhaji kai din mutunin kirki ne kaida xuri'ar ka idan babu damuwa ina neman wata alfarma a gare ka" Abba yace "baby damuwa ina sauraren ka duk abinda kk so indae har baifi karfina ba xan baka" baba Rashid ya jinjina kai kafin yace "idan babu damuwa inason kabama yaro na auren daya daga cikin yaran ka mata dan ina so mu kulla zumunci mai karfi da kai" kamar saukar aradu haka abba yaji batun ya dago yana kallon baba Rashid jiyayi ya masa kwarjini baxai iya ce masa aa ba can ya kakalo murmushi kafin yace "babu damuwa danma wnn ai ba matsala ga Aneesa nan sae na basa ai dani da kai duk daya.... Murmushi jin dadi yy kafin yace ngd Allah yayi albarka.... Abba ya dauki waya ya kira Auwal yana dagawa yace "kace inason ganin kowa dake cikin gidan nan".  . babu jimawa sae gasu duka sun shigo  kowa ya samu guri ya zauna suka gaisar da baba Rashid ya amsa cikin farin ciki....
Duban su Abba yy kafin ya fara sanar dasu duk abinda suka yanke tsakanin su da baba Rashid.    Hankali tashe umma ta mike tsaye haba Alhaji kamar ba kaine ka haife ta ba da zaka dauke ta kaba ma wanda ba ka san kowa nasa ba haba Alhaji.... Cikin fushi Abba yace baki da hankali ne kin kau san abinda bakin ki yake furtawa kuwa Abida. ... "Dama ina take da hankalin ai wadanan matan naka babu abinda suka saka gaba sae aikin shedan..   Muryar hajjo ta katse su... Hankalin Abba da yaya Auwal a tashe suke tambayar meke faruwa ganin yanda khadija ke kuka kamar ranta zai fita farida na taya ta Abba yane "hajjo meyafaru""yo meyema bai faru ba sae ta fara kuka "ynx dan Allah me wnn jikar tawa tayi wa matan ka da yan uwan ta dan nasan tabbas cikin sune wnn wane irn bakin ciki ne suke mata ace aure ma baxasu bari tayi ba nan ta kwashe duk abinda ya faru ra fada masa.    Shiru Abba yy yana kallon matan sa zuciyar sa na kuna baya son abinda zai batawa khadija rai ko kadan kodan maraicinta baxa su tausaya mata ba yaya Auwal yana can kusa da khadija yana lallashin ta.... Abba yace "mai nayi maku haka dan ba khadija kukayi mawa ba ni kukayi mawa... Hajjo ta goge hawaye "dama nasan baxasu taba kaunar ta ba sun fiso taita zaman gida to ta Allah ba taku ba.... Baba Rashid ne yace hajiya abi komai a sannu dan Allah ni idan babu damuwa Alhaji inaso kabani auren mai sunan hajjo tunda ita waccan mahaifiyar ta bata so... Shiru Abba yy yana kallon baba Rashid ko kitawa babu kamar yanda kowa ya zura Masa idanu... Gaban Abba sae faduwa yake ji yake anya idan yayi haka yama khadija adalci baya son abinda zai batawa khadija rai ko kadan baya so ya kuntata mata.... Baba Rashid yace "kamar da wuya ko baxaka iya daukar diyarka kabama talaka ba ko wanda baka san sa ba ko" umma tace "Alhaji maizae hana ka amince khadija da Aneesa ai duk yaranka ne saedae idan sonkai xaka nuna"... Abba ya sauke numfashi kafin yace "ni bani da matsala indae diya ta ce na amince nabama danka aurenta indae har mahaifiya ta ta amince itama khadijar ta amince . bani da matsala.. Da sauri hajjo tace "kaji ni da ja'iri ni na san alkhairin take tare da ita da baxan amince ba  na amince Allah ya tabbatar da alkhairi.... Ta juya ga khadija da tayi sunan xaune ta dafa kafadar ta tace "ta kwara nasan ke mai biyayya ce kuma nasan baxaki watsa min kasa a ido ba nida mahaifin ki inaso ki yarda da wnn auren dan baki san alkhairin dake tattare dashiba.... Khadija ta lumshe idanun ta gabanta na faduwa baxata iya musa da Abban ta ba tasan idan tace aa baxai ji dadi ba snn baxata iya cewa baba Rashid cewa bata  son  dansa ba.   Ya bude idanun ta dasuka jike da hawaye  Haba Abba kana da ikon bada aure na ga kowaye ma bare dan Baba wlh na amince Allah yasa hakan shine mafi alkhairi.... Hajji bata san lokacin da ta rungume ta nasan ke ya' ce kin haifu Allah yayi maki albarka.. Khadija ta fashe da kuka. Baba Rashid yace "Allah ya maki albarka" umma taja hannun Aneesa tana mita "ai dama da ita yadace bada ke ba dan ke da asalinki da kmi" Auwal ya bita da kallo cikin takaicin  abinda suke yi mama ma tabe baki tayi ta fice..

More comment more typing.... ✍️

*#Vote*
*#Share*
*#Comment*

✨✨✨
*Nafeesa A Guga*

SABODA DUNIYA Where stories live. Discover now