Part thirty four

44 5 0
                                    

Typing~~~~📱

*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*

'''(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)

   🌼 *Saboda* *duniya* 🌃

Writing by......
<<<<≤<≤<<<<<<<<<<<<
*Annafie*💗

07051376476

Nafeesa A Guga @ wattpad

*bismillahir rahman  rahim*
Page 66 ⏩ 67

  🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
Fitowar sa daga wanka knn  sanye cikin white bathrobe dinsa hannun sa rike da dan karamin towel yana goge ruwa kallo daya yy mata ya nufi mirror yana shafa mai har yagama ya fess body spray.. Duk tana kallon sa... Tace "meyasa me ka" kallon ta yy ya sakar mata dan murmushi bayan ya saka singlet da boxex  yace "bakomai" sann ya nufi closet dinsa ya dauko wata rigar bacci .. Matsowa tayi inda yake ta karbi rigar yana kallon ta ta mirror  ta taimaka masa yasaka duk yana kallon ta  ta dauko turare ta fesa masa.. Yy murmushi tare da cewa "thanks wife" dan lumshe idanu tayi ta bude a kansa snn tace "baxadae ka fadamun abinda ke damun kaba ko..... Hannun ta ya kama yajata zuwa saman sofa ya zauna tare da janyo ta ya daurata saman jikin sa  yace "wani abu kika gani ne".... Lafewa tayi a jikinsa a hankali tace "I know there must be something wrong dan tunda ka shigo na kula da yanayin ka"... Rumgune ta yy tare da daura kansa saman nata ya furzar da iska yana lumshe sexy eyes dinsa...... Ya dade a haka kamar baxaice komai ba sae kuma ya fara magana murya can kasa.... "Yau bayan mun fita da waleed yake cemun besan meyasa umman sa take son raba kyakkyawar alakar dake tsakanin mu ba bacin Allah yayimu yan uwa kuma jini daya besan meyasa take kin yaran mummy ba bayan ita mummyn bata kinsu... Ya nuna min damuwar sa sosae snn kuma ya nuna min bayaso ranar da zata zo ace burin umman su ya cika sun juya mana baya saboda duniya da abinda ke cikin ta... Ya kalli khadija shin meyasa take mana haka ne meyasa take son raba tsakanin mu bayan Allah ne ya hada mu kuma shi ya dasa mana kaunar junan mu maganganun sa sun tsaya mun a rai dan nasan inhar ta samu dama sai ta raba tsakanin mu bama su kadae ba harta iyayena sae ta raba ni dasu tinda har ta dauko hanya ni kuma da na rasa su a rayuwa ta na gwammace na rasa komai nawa na domin su din jinina ne mecece duniya da har take tunanin rabani dasu..."
  A yanda yake maganar kasan yana cikin damuwa da bacin rai idanun sa sun sauya kala.. Tuni taji kwalla ta kawo idanun ta.. Dole ya shiga damuwa domin kau a raba ka da wadanda kake kauna babban tashin hankali ne kuma daga gani wnn familyn suna kaunar junan su yanda idan ba daya dole si shiga tashin hankali.. Tunano nata yan uwan tayi wadan da kwata kwata basa kaunar ta.. Da sauri ta kawar da tunanin ta goge hawayen ta .. Ta saka hannuwan ta ta tallafo fuskar sa tana kallon sa... Snn tace "kana ganin akwai wanda ya isa ya maka abinda Allah bai maka ba" girgiza mata kai tace "to meyasa zaka damu kan ka Allah yace kome yasame mu mu mika masa kuka mu kuma shi zai share mana hawayen mu duk abinda kaga yasamu bawa mukaddarine daga Allah  dan haka ka kwantar da kanka ka inshallah babu wanda zai rabaka da yan uwanka kaji" dan murmushi Ammar yy yana jin sanyi a ransa taciga ... "Addu'a zamuyi snn itama munema mata shiriya da fatan kuma Allah ya shiryaemu gaba daya  pls forget about that kaji"..... Ya hade goshin sa da nata a hankali yace "na manta and thank you for reminding me that Allah is the best" murmushi tayi tana kokarin sauka daga jikin sa ya kalleta "oh zaki fara ko" ta marairaice abinci fa zamu je kaci.. Dan kada kai yy kafin yace "ok lets go".. Kama hannun ta yy suka nufi inda abincin yake ta zuba masa ta tura masa yace "kefa"
Tace "am ok naci nawa".. Dan dage kafada yy snn ya fara cin abinsa... Ita kuma ta bisa da kallo ganin yanda yakecin abincin a natse gwanin bansha'awa.. Dagowa yy suka hada idanu  tayi saurin dauke kanta yy murmushi snn yace dama kin dago dan naga abinda kk yi.. Dagowa tayi tana tsuke fuska me kuma nayi ya harareta snn yace "da wani kanki tun ba haihuwa" kara hade fuska tayi kamar zatayi masifa sai kuma ta bude manyan idanun ta tare da fashewa da dariya kallon ta  ta yy ganin yanda take nunasa ne ya fara kallon jikin sa ta dan tsagaita snn tace "wlh kaima haka kanka yake da kana yaro wai ka ganka kuwa" sakin bakin yy yana kallon ta ganin harda wani rantsewa. Sai kuma ya dage gira yana kallonta "nidin kuma harda rantsuwa" "oh kana mmki ne bari ka gani" ta fada tana mikewa ta nufi inda hotunan suke ya bita da kallo harta dauko ta dawo.....
Sakin baki yy yana kallon pics din yace "ke where did you get them from" dage kafada tayi tana murmushi "tace kaima kanka ai tuna haihuwar ne" yana murmushi yana kallon pic dinsa wasu gwanin ban dariya wani harda napkin babu kaya jikin sa... Yace "lallai ma mummy wato saeda ta nuna maki knn dama ta dade da daukar wnn promise din" khadija ta dauko wanda yake daga shi sai napkin tana dariya sosae tace "wae dube ka kamar ba kai ba daga kai sai napkin" dariya take sosae shikam ya bita da itanu ganin yanda tayi kyau da dariyar kamar karta dena.. Yace " dasuki ma tunda matata ta gani what's there abinda yafi napkin ma zata gani.. " cak ta tsaya da dariyar tana kallon sa.  Shikuma ya kashe mata ido daya .. Mikewa tayi ba tare da tace komai ba ta nufi toilet ya bita dakallo har ta shige snn yace "Hanan rigima"..  da dade bata fito ba dan wanka ta tsaya yi ta fito sanye da bathrope ko kallon direction din da yake zaune yana danna system dinsa batayi ba ta nufi mirror tayi shafa taxo ta shirya cikin kayan bacci taje ta kwanta saman bed tare da rufa da blanket..
     Ko minti biyu batayi da kwaciya ba ya mike yashi toilet brush yayo snn ya fito ya kashe wutar yabar mara haske snn ya shiga bargon shima tare da rungume ta ta bayan ta  ... A kunne ya rada mata "am very lucky to have you as wife"... idanun ta a lumshe ta saki murmushin da bata shirya ba she don't know how she's feeling but happy... A haka bacci ya dauke su.. Nikam nace asbu ta gari...
      Washe gari sae ga aunty fati da murnar ta dan tunda suka gane cewa ga abinda yasamu danuwan nasu iyayensu sunyi biris ganin mummy bata da niyar cemata komai yasa tayi fushi ta dena zuwa gidan ko waya amma kullum tana masu adduar dashi da iyayen nata.. Shaheed na ganin khadija ya ganeta aikam ya makale mata itakam sai kara ririta shi take.. Sun dade kafin mijin ta yaxo ya dauketa dan akwai inda zasu...  Da yamma suka fita zagaya cikin gari ita da su sameera ya khadija ta sha kallo sann sunje sunyi Siyayya kayan sakawa takalma kayan shaga kai harda na kan ciye ciye irin su chocolate khadija saida ta kwaso.. Da suka dawo Ammar yaga kayan ciye ciyen da ta kwaso yace "sae kace baby" murguda masa baki tayi tace "ina ruwanka" murmushi kawae yy yace "fitina"..
    Haka rayuwar su tacigaba da tafiya khadija ta saba da yan gidan kamar me wanda yan uwan ta na jini ma basu saba haka ba snn a rayuwa mahaifi shine daya amma iyaye yawa garesu domin kau khadija ta rasa mahaifiya amma mummy ta zame mata tamkar ita dan duk abinda take nema samu take suma basa suruka da juna... Ta bangaren Ammar kau suna nan yanda suke babu abinda ya canxa ... Shi wani lokacin idan tana wani abun har mamaki take basa yar karama da ita sae hankali wani amma idanba tayitana wata yarintar zaka nage yarinya ce lokacin kuma ta birkice takoma fitinan na da tsiwa sae kuma shegen tsoro cike da ciki... .. Amma kuma sun saba sosae dan inhar ta dade bata gansa ba sai ta shiga damuwa.. Kuma ko bacci zatayi ta fi jin dadi a jikin sa tana shakar kamshin sa amna bata nuna masa hakan...

   Shigowar sa knn ya tarar da ita tana sallah  tsaye yayi jikin kofa yana kallonta.. Yana inda yake harta sallame ta fara azkar harta gama bai motsa daga inda yaje ba jin an shigo kuma ba a karaso ba Ta juya.. Tsaye ta gansa jikin door yana kallon ta.. Sannu da zuwa tayi masa.. Bai amsa ba saema lumshe idanun da yy Wanda hakan na kara masa kyau.. Ya dade a haka kafin murya can kasa yace "yaushe kika gama" ba tare da ta fahimci inda ya dosa ba tace "what?"  Still idanunsa a lumshe yace "period" gabanta ne ya fadi dan tun shekaran jiya da daddare tayi wanka a boye take sallah dan kar ya gane sai gashi yau ya kamata dumu dumu... Da sauri ta juya masa baya tana tura baki.. Barin bakin kofar yayi  ya nufi toilet snn ya shiga tana ganin haka ta fice a dakin...
   A ranar khadija duk a tsorace take ko ganin sa tayi sai gaban ta ya fadi shikam yana lura da ita share ta kwae yy yai ta hidimar sa.. Da zasu kwanta ta ma kasa sakin jikin ta tayi saida taga ba ta ita yake ba snn ta saki jikin ta.. Washe gari ma share ta yayi  ya shirya cikin uniform dinsa wanda ke nuna shi jami'in kasa da kasa ne  sunyi matukar yi masa kyau khadija sai kallon sa take sae ta nuto da ranar da ta fara ganin sa.. Matsowa yayi daf da ita tare da hura mata iskar bakin sa.. Wata kunya taji ta lullubeta ya saki murmushi snn yace "I'll be going"  bata bude idanun ta ba tace "a dawo lpy".. Kadan kadan kadan take kallon sa har ya fice.. ..

     khadija ce ta fito daga wanka sanye da dan towel pink dan karami wanda iyakar sa rabin cintar ta  Ammar kam ya fita sallahr isha'i  gaban mirror taje tayo shafa ta gyara gashin kanta tare da feshe jikin ta da body spray.. Tana gama wa ta mike domin ta dauko kayan bacci taji an bude kofar an shigo... Ammar ne wanda lokaci guda idanun sa suka sauka a kanta ya fara kallon ta tundaga toes dinta fararen cinyoyinta da kirginta da yake cike zuwa kyakkyawar fuskar ta wanda ita ma din shi take kallo.. Ganin irin kallon da yake mata ne yaka tayi saurin nufar closet dinta yace "wait" cak ta tsaya fuska a tsorace.. Tako wa ya fara yi zuwa inda take ta fara ja da baya yana biyota har ta isa jikin bango jikin ta na rawa ta fara girgiza masa kai.. Gab ya matso kusa da ita kamar zai shige jikin ta ta hada goshi sa da nata haka ma hancin su lips dinsu ne kawae basu hadu ba.. Yana kallon cikin idonta a idanun sa suka fara sauya ka kafin ya lumshe ya daura soft lips dinsa saman nata tare da kissing dinsu a hankali  sa cire ya kara kallonta idanun ta sun cika da hawaye tana girgixa masa kai  ya kara lumshe idanun sa tare da daura lips dinsa a nata yy kissing.. Ya bude idanun sa ya kalleta sae kuma ya kara hadewa yana tsotsa tare da rungumeta...
Wani irin feelings yake ji ta ko'in yayinda ita kam hankalinta yayi mugun tashi har lokacib lips dinsu na hade... Da sauri ta rike towel dinta jin yana kokarin zamewa sann ta cire  bakin ta a nasa tare da fashewa da kuka.. Hakan ya dawo da Ammar daga cikin hayyacin sa... Rabuwa da ita yy tare da fadawa saman gado yana sauke numfashi... Da sauri ta nufi closet ta dauko riga ta zura tareda saka hijab....
  Ya dade kwance saman gadon dafe da kansa kafin ya tashi zaune ya janyo system dinsa dake saman bedside drower ya fara danne danne.. Har lokacin bata matsa daga inda take ba dagowa wa yy ya kalleta fuskar ta a tsorace dariya taso subuce masa amma ya dake.. Ya mika mata hannu alamar taxo .. Kin motsi tayi ta xura masa idanun ta ya lumshe idanu "come pls".. A hankali ta karasa kusa dashi ta kamo hannun ta tare da zaunar da ita saman cinyar sa a tsorace ta fara kokarin tashi ya mayar da ita murya kasa kasa yace "relax mana babu abinda zan maki" danne dannen sa yayi snn ya juyo da system din yanda zata gani yace "choose the sch you want to study a duk cikin misra" on expected haka taji zance sa kallon sa tayi fuskar ta dauke da tsantsan tace "pls tell you're not joking" lumshe idanu yy kafin yace "sure.. Ki xaba gobe sai muje dake ayi duk abinda ya kamata.... Khadiha bata san lokacin da ta rungume sa ba saboda tsantsar farin ciki da alama harta manta da abinda ya faru tsakanin su.. Yace "ouwch karki ballani dubifa yanda kika matseni da nine da tuni an fara mun kuka... Cike da kunya ta sakesa tare da sauka daga saman jikin sa yace "madam sorry ta go ki zaba kwantawa tayi ba tare da ta kallesa tace "kasaka mun tasu Rahma ita nake so" murmushi kawae yy tare da cike mata makarantar su Rahma.. Yana gamawa ya shiga toilet yy wanka ya saka kayan bacci snn ya hawo gadon har tayi bacci ya janyo ta jikinsa tare da zare hijabin jikinta...
  More comments more typing... ✍️

*#VOTE*
*#SHARE*
*#COMMENTS*

✨✨✨
*NAFEESA A GUGA*
😍😍😍😍😍😍😍😍

SABODA DUNIYA Where stories live. Discover now