Typing~~~~📱
*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
'''(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)
🌼 *Saboda* *duniya* 🌃
Writing by......
<<<<≤<≤<<<<<<<<<<<<
*Annafie*💗07051376476
Nafeesa A Guga @ wattpad
*bismillahir rahman rahim*
Page 5️⃣- 6️⃣
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼Muhammad sambo shine mahaifin khadija mutum ne wanda yasan darajar mutane tun yana dan karami mahaifinsa ya rasu sae mahaifiyar sa Hadiza wacce suke kira da hajjo.. Su uku mahaifin su malam sambo yabar mata usman sae Muhammad sae autar su Amina.. Hajjo ita taci gaba da kulawa dasu bayan rasuwar mahaifin su ta jajirce wajen basu tarbiyya da ilimi duk da basu da wani karfi har suka taso suna kaunar junan su sosae usman kasuwan ci ya saka a gaba dan bayan ya gama karatunsa bai samu aiki ba yayinda shikuma Muhammad yana gamawa ya fito da aikinsa a hannu amma duk da haka sae ya hada da kasuwanci balaifi sun samu rufin asiri daedae gwargwado domin kau Allah ya buda masu kuma komai suna tafiya dashi ta tsarin addinin musulinci...
Hajjo bata yarda amina tayi wani zurfin karatu ba dan ita a cewarta aure shine yafi dacewa da ya mace idan duk da ba hakan su Usman suka so ba amma babu yanda suka iya dama cikin abokanan Usman akwai wani Alhaji Isma'il da yake neman ta Usman yana jin haka ya gabatar da kansa akayi sa'a suka daedae ta kuma hajjo taya yaba da halinsa Alhaji usman dan jihar adamawa ne yana da arziki sosae.... Batare da bata lokacin ba aka fara shirye shiryen biki cikin yan watan ni aka daura aure ya wuce da matar sa adamawa ganin hajjo bata da ya mace kusa da itane yasa usman yanke hukuncin yin aure dan hajjo tasamu mai debe mata kewa dan yaga tana kewar amina kuma dagashi har Muhammad basu fiye xama gida ba barin ma Muhammad sbd yanayin aikin sa ... Jin shawarar da ya yanke yasa hajjo ta cika da murna.. Tuni usman ya samu mata aka daura aure..... Sunan ta Hafsa ba laifi hafsa tana dan taimakawa hajjo amma bada son ranta ba dan babu yanda xatayi ne dan daga hajjar har usman babu mai daukar warji a cikin su kuma tana son mijin ta bata son abinda zae raba su dan takula zae iyayin komai akan mahaifiyar sa..... Muhammad da usman suna tasamun budi babu laifi.. Dan shekarar hafsa daya da zuwa suka je makka gaba dayan su harda Amina...
Basu dade da dawowa ba Amina ta samu ciki tana gab da haihuwa ta dawo gida wanka.. Haka ma hafsa a lokacin taje wanka gida
Wata rana Muhammad da hajja sun fita domin ya nuna mata gidajen da ya siya da kuma kuma irn abubuwan cigaban da yasa mu.. Akan hanyar sa ta dawowane wata tashige masu gaba suka banke ta da mota... A rude suka bude suka yo kanta hajjo harda su kuka Muhammad duk yabi ya rude dan har cikin ransa yana jin kuka hajjo....
Yarunyar bata farfado ba sae washe gari hajjo ta gani kusa da ita tana gyangyadi ganin ta tashi zaune yasa hajjo wartsakewa tana washe baki kafin ta fara magana da karfi Muhammad ductor (doctor) kuxo ta farfardo... Da kamar jira suke saega su Muhammad sun shigo da nurse kallon kallo aka tsaya yi da ita dasu sannu suka rinka yi mata amma batace dasu komai ba.. Muhammad ne yayi tunanin ce mata "how are you feeling" a hankali tace masa "fine" doctor ne yace a basa guri yan gwaje gwaje yy mata kafin ya fito snn yace Muhammad ya sa mesa a office domin ayi discharging dinta...
Bayan an sallamesu suka shigo mota Muhammad ya ce "ynx muje gida kiyi wanka" ki dan huta daga nan sae mu kaiki gida ko" cikin harshen turanci yake maganar itama cikin harshen turancin tace "ai bn san inane gidan mu ba" batare da ya kalleta ba yace "yasu nan unguwar ku" tace bata sani ba" yace "wane gari kk" nanma tace bata sani ba
Dan juyo wa yy yana kallon ta da mmki kafin ya dauke idonsa a kanta yaciga ba tuki hajjo ta tambaye sa meke faruwa yace idan munje gida xan maki bayani.... Bayan sun isa hajjo yahada mata ruwan wanka bayan ta shiga ne Muhammad yy mata bayanin abinda take fada masa hajjo tacika da mmki..
Sai da suka gama cin abinci snn Muhammad ya ce mata ina iyayenki " nan ma tace bata sani ba.. Nan masuka cika da mmki
Amina ce tace to ya sunan ki... Shiru tayi kafin tace "am ummulkursum Abdullahi" nan ma suka kara shiga mmki "Muhammad yace "kuma bakisan kowa naki ba" tace "eh".. Duk wata tambaya da suka mata game da ita tace masu bata sani ba saedae sunan ta da tafada masu dukkan su sun shiga mmki... Dan kallon su tayi kafin a hankali tace "I want pray" da mmki suke kallon ta haka ma hajjo da aka fassara mata da kyar da iya cewa Amina ta kaita tayi sallah suka bita da kallo hajjo tace ga dae yarinya har yarinya amma ace batason kowa ba anya wnn ba jifa a ka mata ba. Danni bama tamun kama da yan kasar nan... Shide Muhammad shiru yana jinjina lamarin a ransa....
Hafsa ma tayi mmki gashi ko sallahr ta a natse take yi... Usman ma da ya dawo yasha mmki.. Can yace hajjo baki tunanin jifa akayi ma yarinyar nan, hajjo tace nima haka nake gani amma ni wlh ta kwanta min a rai jinake dama diya ta ce...
Kwanan kursum biyu amma har yau babu abinda tace ta sani game da ita saedae a dan zaman da sukayi da ita sun gane tana da saukin kai da riko da addini babu wanda bata shiga ransa ba a gidan nan musamman ma Amina dasuka zama kawaye haka hajjo ma jin ta take kamar yar cikin da duk da idan sun hadu zaman kurame suke amma hajjo ta dage saeta koya mata hausa......
Ana cikin haka Amina ta haifo kyakkyawan danta murna wajen hajja kamar me haka ma kursum ko daushe tana makale da yaron da taji yafara kuka xata rude ranar suna yaro yaci sunan sa Abubakar sadiq.. A ranar kuma aka Kira hafsa ta haihu amma dan babu Dukkan su sun shiga damuwa kuma sun tausayawa hafsa Usman ma yashiga damuwa...
Bayan wata daya hafsa ta dawo tunda ta kyalla idanu taga kursum hankalin ta ya tashi ganin yanda kowa ke nan da nan da ita ko magana bata so usman yana mata dan gaba daya duk ta rude da ita musamman ma ta taji Muhammad zaiyi aure bare ma tasaka rae cewa mijnta baxae aure ta ba sbd ga Muhammad kodaya bata kaunar ta.... Kulsum ta kula cikin gidan nan ita ce kadae bata sake mata ynx kam ta fara iya hausa duk da bata iya mayarwa dan hajjo ta dage sae an koya mata hausa... Amina ma bata koma ba sbd jira take sae anyi bikin Muhammad dan bafi sati biyu ba.. Shirye shirye ake sosae na bikin dan ynx kam su kudi alhmdllh bayan
Bayan amaryar mahammad abida ta tare a sabon gidan da Muhammad ya gina... Itama sae ta tsinci kanta da tsanar kursum ganin yanda suka saba sosae da Muhammad dama gashi hafsa ta zaiyane mata komai game da tarihin kursum Ai sae abida tafi tsanar ta ma akan hafsa dan tafi sabawa da Muhammad akan usman saedae abinda bata sani ba shine tun ranar da Muhammad yaga kulsum yake sonta...
Ranar da Amina xata koma kulsum tasha kuka barin ma da taga xata rabu da sadiq dan yaron ya shiga ranta saeda hajjo tayi da gske snn ta kwantar da hankalin ta.. Kursum tasaba da kowa nake sun zama sune kowa nata kuma kowa kaunar ta ya ke saidae takula matan su usman basa kaunar ta hakan yasa itama bata shiga sabgarsu babu abinda kursum bata iyaba na rayuwa amma har yau ta kasa tuna kowa nata... Takan je wa Amina hutu amma gidajen su usman indae batare dasu ba bata zuwa dan duk tsanar da sukai mata basa nuna mata gabansu... Shekarar Abida daya ta haifo kyakkyawan danta.. Wanda ranar suna yaci sunan sa auwal.. Murna wajen kursum ba'a magana dan Allah yayi ta da son yara.. Shikam Muhammad tunda auwal ya fara wayau yake kawo mata shi yaran ma har ya santa dan abida bata damu kula da yaro ba kullum yana wajen kursum hakan na bakanta ran abida.. Haka kuma wata shakuwa ce ke shiga tsakanin ta da Muhammad a hankali a hankali har soyayya ta shiga tsakanin su hajjo na kula dasu kuma hakan ya mata dadi... Hankalin su hafsa da abida ya tashi sosae ganin yanda maxajen su suka daje wajen sobon gida na kece raini kuma anata ta gyara gidan hajjo dan ynx kam kudi ke shigo masu... Muhammad yasamu hajjo da maganar yana son auren kulsum tace ita babu rwan ta indae ta amince shiknn saedae yarike amana....
Cikin yan kwanaki aka saka ranar auren su.... Abida har karamin hauka saeda tayi dan saeda su hajjo suka taka mata birki da yan uwan ta snn ta barsu suka huta...
Bayan biki wata soyayya ce mai karfi tasake shiga tsakanin su saedae kodaya bata jin dadin zama da abida ynx kam hafsa suna dan shiri dan tunda taji Muhammad ne xai aure ta ta kwantar da hankalin ta,.
Kulsum ce ta yaye auwal dan wata shakuwace tsaka nin su hakan kau yana bakanta ran abida amma babu yanda ta iya dan koshi Auwal din yafi yarda da kulsum a kanta...
Hafsa ta sake samun ciki ta har ta samu mujaheed.. A lokacin ne Muhammad yasake xuwa kasa mai tsarki tare da dukakkan matansa. ..
Shekarar Auwal hudu abida ta sake haihuwar saddiqa .. Saedae ko daya bata bari kulsum ta dauke ta sae ma gori da take mata akan itama ta haifi nata.. Abin yana ma kulsum ciwo dan Allah yayi ta da son yara... A wnn lokacin ne ogan Alh. Muhammad ya neme ya auri diyar sa jamila sbd mutuwar sonsa da take babu yanda ya iya face ya amince bai samu matsala da kulsum ba sai abida itama saedai tayi burgar ta ta gama...
Bayan ya auro jamila abida taso ta rinka juya ta sae taga tama take ta ita kuma jamila gani take abida ba abin kishin ta bace sai kursum dan takula yafi sonta nesa ba kusa ba.. Hakan yasa suka dauki tsanar duniya suka daura wa kursum.. Shekarar jamila daya ta haifi Raliya.. Gori sae ya koma kan kursum wai babu asali kuma gata juya abin na damun ta amma babu yanda ta iya ita baxata ga inda take ba ya akai kowa keda asali ita babu hajjo ce ke taka masu burki sai shi Muhammad din da Amina.. Hafsa kam babu ruwanta ynx yaran ta biyu mujaheed da faruq..
Bayan Abida tayi saddiqa sae tayi mufeedajamila kuma tayi salima.. Kulsum kau shiru gashi suyi ta saka yaran suna mata rashin kunya idan kacire Auwal kuma shi ba zama yake ba sbd karatu.. Hajjo ma rashin haihuwar kulsum na damun ta wata sa'in har gidan take xuwa ta xauna saboda abinda su jamila ke mata amma da tatafi sae a daura daga inda aka tsaya,.. Tare jamila da abida suka sake samun ciki gori kam sae ya karu suka hade mata kai.. Wata hudu Aneesa tabama farida....lokacin kuma Amina ta haifi husna..
Kwatsam rana daya saega kulsum da ciki Murna wajen Muhammad da hajjo ba'a magana su abida kam bakin ciki kamar me ganin yanda kowa ke farin ciki da wnn cikin sae kaffa kaffa ake da ita gata kam kamar me hajjo kullum tana gidan bakin ciki kamar ya kashe sauran matan gidan da cikin ta ya cika watan haihuwa hajjo ta dauke zuwa gidan ta bahakan Muhammad yaso ba amma ya iya kullum yana kan hanyar gidan su jamila kamar suci xuciya ganin irn gatan da ake bata.. Ranar wata juma'a kulsum ta haifi kyakkyawar diyar ta ruwa biyu dan babu wanda bata kama dashi cikin iyayenta hajjo ba'a taba haihuwar da tayi Murna ba irn wann ranar suna aka mata ta kwara wato khadija.... Ko a sunan ta bakaramar rawa aka taka ba Amina ma ji take kamar ta amshe yarjnyar sbd kyawun ta da shiga rai....
Tundaga nan babu wanda ya sake haihuwa Auwal lokacin yana gida kullum khadija na hannunsa yana mata wasa yakance ke shine kika dade baki xo ba ko kika sa muka shiga damuwa da ummi ko idan kin girma saena xane ki... Yarinyar ta shiga ransa sosae yana kaunar ta kamar me haka ma Abban su tunda su jamila suka lura da haka suka dauki tsanar duniya suka daura mata gashi kowa a dangi yana son ta haka nan hajjo xata dauko kafa taxo wai taxo ganin takwarar ta.. Wann abin na masu ciwo har yaran Hafsa da amina suna sunfi sonta akan yaran su.. Duk da abba na kokari wajen danne soyayyar ta amma saeda suka fahimta.. Sun dauki karan tsana sun daura wa kursum da diyarta...haka ma yaran su haka khadija ta taso cikin tsana wajen yan uwanta da iyayensu da farida da yaya Auwal kadae suke kaunar ta itama farida dan dae ajinsu daya a makaranta ne suka saba sakamakon Aneesa da ta B su suna A... Akullum cikin gori take wae ummin ta bata da asali tun bata fahimta harta fara gane.. Ranar ta tambayi umminta tace "ummi wae bakida asali wae baki da iyaye... Ranar kursum tayi kuka kamar me tace "khadija nima bn sani ba" kursum na fuskantar cin fuska sosae ba ga kishiyoyin ta ba ga yarasu ba Auwal ne kadae da farida suke girmama ta... Hakan da khadija ta lurane yasa itama ta dena ganin girman duk wanda baya girmama mahaifiyar ta kullum sae anyi tsiya da ita ba'a abun mutum ya dake ta ba ya hadu da fushin Abba ko hajjo dan hajjo har gida sae taxo ta ci mutuncin mutum akan khadija....
A haka suke rayuwa har har khadija tacika shikara 11... Bata raga wa kowa a gidan amma wata sa'in idan yan miskilancin ta suna kai ko kallo baka ishe ta ba ... Duk cikin gidan tafisu kyau ga kokari boko da islamiya dan malamai na alfahari da ita bata taba wuce 1st position ba hakan yana kara bakanta ran yan gidan.....
Kwatsam wata rana sae kursum ta tashi da ciwon hauka abu kamar wasa ya tsanan ta aka baxama neman magani amma ina har kusan wata daya abu yaki ci yaki cinyewa abba yashiga tashi hankali sosae shida su hajjo. Amina da usman kai har hafsa ta tausaya mata khadija kam ai ba'a magana.. Sai abu ya kara xama abin gori cikin gidan dan Ya Auwal ne kawae da farida suka shiga damuwa ... Wasa wasa har ta kusa shekara a haka a lokacin duk wani masoyin ta sae ya tausaya mata...
Rana da khadija baxata taba mantawa ba ranar da aka tafi da umminta wajen wani mai magani Abba yana da aikin gaggawa Hafsa ce ta tafi da ita da driver babu kukan da khadija batayi ba akan xata je amma hajjo ta hana sbd batada lpy a lokacin... Bayan tafiyar su da yan awanni.. Aka kira cewa motar su tayi hatsari mai firgitar wa dan babu wanda ya rayu ko gawar wani ba'a gane wa...
Wnn family din sun shiga tashin hankali hajjo ta rasa surukai biyu a lokaci guda idan kaga usman da Muhammad saeka tausaya masu dan rasa mata bakaramin tashin hankali bane 😭 mujaheed da faruk sun shiga tashin hankali.. Khadija kam tayi suma yafi nawa ko su abida saida suka tausaya mata....
Daga nan rikon mujaheed da faruq ya koma hannu hajjo khadija kam takan dan zauna amma ba sosae ba dan abba yace baya so ya rabata da yan uwan ta...
Khadija bata jin dadin xama cikinsu ko kadan dan basa damuwa da cewa umminta bata duniya suke mata gori kuma su zageta.. Tana jin ciwo amma ya ta iya dan ma basa mata sbd hajjo bata raga masu... Itama hakan ba raga masu take ba saedae wani lokacin suna cin sa'ar ya Auwal da farida yaran kau ba raga masu take ba duk da sun girme ta... Wani lokacin kuma tabama bnx ajiyar su kulawa kam tana samun ta wajen Abba da ya Auwal da hajjo dan basa son ganin fushin ta ko kadan sae yaran (momy) Amina ya sadiq da husna haka ma faruq da mujaheed suna sonta.... Yan gidan su ne kadae matsalar ta dan ynx tsanar duniya sun daura mata ga bakin ciki dasuke mata ita kam hakan baya damun ta... A ynx tana suna 100l ne ita da Aneesa da farida tana karantar law... Wnn knnMore comment more typing
*#vote*
*#share*
*#comment*✨✨✨
*Nafeesa A Guga*
YOU ARE READING
SABODA DUNIYA
RomanceLabarin yana dauke da abubuwan bn mmki.. Labarine akan wadanda duniya ta rufe masu ido sun manta Allah ne mai komai snn yana dauke da salon soyayya mai bn sha'awa.. Zai fadakar kuma ya nishadantar daku