Part twenty four

45 4 0
                                    

Typing~~~~📱

*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*

'''(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)

   🌼 *Saboda* *duniya* 🌃

Writing by......
<<<<≤<≤<<<<<<<<<<<<
*Annafie*💗

07051376476

Nafeesa A Guga @ wattpad

*bismillahir rahman  rahim*

Page 46⏩47
  🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

Sosae khadija take gudu tana karanta duk adduar da tazo bakin ta ta kariya daga dukkan wani mai sharri yayinda hawaye ke zuba a idanun ta kamar me tausayin Ammar da iyayensa kawae take snn tana tunanin wace irin rayuwa zasu yi Wajen la'asar suka shigo cikin garin kano juyowa tayi ta kalli Ammar taga bacci yake ta sauke ajiyar zuciya snn taci gaba da tafiya shiru a ranta tana tunanin ina zata dosa tasan ko hauka take baxata zauna a kano ba saboda babban gari ne a kwae manya manya da ammar baxae wahala ganewa ba tunanin inda zasu bi kawae take kuma bata so su hadu da sojoji ko yan sanda  dan sau hudu tana haduwa da wasu to sae dae kun san yanda Nigeriar take... Shiru tayi tana nazari zaman babban gari ma kwata kwata bae kama ce su ba zagaye garin kano kawae take tana tunane tunane  Filing station ⛽️ ta shiga tayi refiling snn ta wuce wani eatery tayi ordering take away da drinks incase koda zasu bukata dan har lokacin Ammar bai tashi ba tunanin tane ya bata kila kamal ne ya masa allurar bacci cigaba tayi da tafiya har kabuga wata hanya da tayi yamma ta dauka wacce ta wuce janguza barrack daganan ta miki hanyar tana kallon garuruwan dake hanyar  tana son tsayawa amma saetaga duk bayyi mata ba  a haka har ta shigo cikin katsina state a wani gari dayi karamar hukumar malumfashi tsayawa tayi tana kallon hanyoyin tana tunanin wacce zatabi hanyar da tayi kudu ta nufa ... Anan ta wuce fstc dayi
Tafiya take sosae Hanyar kankara ta dosa batare da tasan ina zata nufa ba pass seven ta iso cikin garin kankara dan gudu take yi sosae zagaya garin ta rinka yi kafin ta samu wani gefe tayi parking daga cikin class din take ta kallon mutane kowa na hidimar gabansa tunanin yanda zata fara rayuwa a gurin take a ranta tace ko ta kara gaba... Sae kuma tayi saurin girgixa kai dan dare yy" ji tayi ana mata knocking glass gaban tane ya fadi ta fara addu'a a bakin ta ta zuje glass din sukayi ido hudu da wani dattijo da mmki yake kallon ta yace "yarinya me kikeyi a nan wajen kina mace kuma gashi dare yy" cikin sanyi tace "ina wuni baba" yace lpy qlw me kike yi anan dare yana yi fa" a hankali tace "ni bakuwa ce wajen kwana nake nema" shiru yy yana kallon ta ganin irn kallon da yake mata ne yasa tace "ina neman muhallin zama ne kamar gida ko na haya haka" "kina nufin baki son kowa ba anan" ta gyada masa kai yy shiru can yace "to ko zamu je gidana ki kwana" tayi saurin girgiza masa kai "aa baba dai za'a samu ynx inaso sae in kama ynx na basa kudin... Yace "yarinya gidaje suna wahalar samu anan barin ma da dare neman dillalen ma aiki ne Amma idan kin matsa inada numbern wani sae a kira sa tayi saurin gyada masa kai dan bata so su tare a gidan wani dan tasan zasu takura.. Waya ya dauko ya kira wani sun dan dade suna waya snn ya juyo yana duban ta yace "to kinji ba wasu manyan gidaje saedae kananu wadan da akwae mutane a ciki shiru tayi can tace to baba hakan yy... Ya gyada mata kai still looking at her dan daga ganin ta yasan badaga karamin gida taxo ba snn ga dankaririyar mota wacce yake tunanin duk cikin garin kankara da kewaye babu mai kamar ta... Yace "yarinya kiji tsoran Allah nasan kina da iyaye me zaisa ki baro su abinda naga mafi yawancin mata nayi sae su baro iyayen su su shiga duniya kan wani silly abu ki bata rayuwar ki dan Allah idan har kin baro gidan iyayenki ne don ki shiga duniya in baki shawara mana dan zaki saka rayuwar ki a hadari ki rage darajar ki" wani murmushin tayi wanda yafi kuka ciwo tana hawaye lokaci guda kuma taji kaunar mutumin tace "baba ba duniya zan shiga ba hasalima da aure na" ya waro idanu "to me ya fito dake kuma ina mijin naki" tace "ina tare dashi yana bayan mota ne bacci yake" da mmki yace "bacci" tace "eh bashi da lpy ne" gyada kai yy snn yace "to bari na kirasa ynx zaki gansa... Waya yay masa akan cewa yaxo snn ya kashe wayar yana kallon ta she look very innocent but shifa har ynx baiyi yarda tare da mijin tq suke ba duk da yaji yarinyar ta shiga ransa... Ba'a wani jima ba mai bada hayar gidan yaxo a motar sa gaisawa sukayi da Alh marwan ya nuna masa khadija Mal. Jagaba kaga mai neman gidan nan kallon ta jagab yy da kyau dan kallo daya yy mata yasan daga gidan kudi tq fito yace "hajiya nasan xaki fi bukatar babban gida sae dae babu kuma wlh sai ki iya zagaye garin nan baki samu ba.."ba damuwa nawane ake biya a wata uku" yace "dubu tamanin ne" hand back dinta ta janyo kasancewar a kwai kudi ta kirga dubu 80 ta basa ya kirga yasa aljihu tace "dame dame za'a bugata dan ynx nake son tarewa yace "to ba katifa" alh marwan yace "a kwae sabuwar katifar na nasayo jiya bari na baku" khadija tace nagode... Gidansa ya shiga yasa aka fito da wata katuwar katifa mai kyau saman mitar jagaba aka daura suka shiga suka fara tafiya khadija na binsu a baya tafiyar babu nisa har suka isa baki wani gate jagaba ya fita ya bude khadija ta shiga da motar sukuma suka shigo da katifar khadija ta bude ta fito tana bin gidan da kallo
Dakuna shidane kowane gefe uku suna kallon juna a kwae hasken wutar lantarki a koina gidan shiru da alama ba kowa dan kowace kofa a rufe take bnda guda daya  wata kofa jagaba ya bude suka shiga da katifar suka fito jagaba yace "saura tabulaye idan kina da bukata ina saidawa ynx sae na dauko maki" tace "eh" snn ta dubi Alh marwan tace "baba kudin katifar" girgixa mata kai yy snn yace "kar ki damu yata ki barsu kawae fatana dae ki zauna da kowa lpy kuma ki kila dan kinga gidan mutane nw bake kadae bace gyada masa kai tayi" jagaba ya shigo rike da cottons ya mika mata ta basa kudin snn suka nufi inda dakin yake ya bude suka shiga ya kunna haske.. Taita bin dakin da kallo daki daya ne mai dauke da corridor sae toilet da sif din bango da mirro shima na bango ga fan da bulb duk sunayi snn painting lafiyayyen ne kasa kuma tiles ne sae wasu fararen kugeru na roba guda uku .. Ta dunga bin dakin da kallo Allah sarki rayuwa wae yau sune zasuyi rayuwa a nan ita bama kanta take ji ba Ammar take ji shida bangon dakin sa ma kanshi abin kallo ne lallai idan kana cikin daula yakamata ka rinka tunawa dana kasa da kai... Jigine mata katifar sukayi.. Tace "dan Allah kutaimaka min na sakko dashi da mmki duka suke kallon ta jagaba yace "wa?" Danshi baisan ba ita kadae bace Alh marwan ne yace "baya iya tafiya ne" ta gyada masa kai" jinjina kai yy snn yace muje" tayi gaba suka bi bayan ta sae da ta dauko wheel chair dinsa snn ta bude idanu Ammar biyu ynx kam suka sakko dashi suka daura sa a wheel chair din tayi masu godiya snn suka suka nufi waje jagaba yace "kai kaga mutane kamar sun hada iri da larabawa dubesu fa basuyi kalan wahala ba wlh kome ya fito dasu" shide Alhaji marwan baice komae ba...
    Ita da kanta ta turasa har zuwa dakin shi kansa bin dakin yake da kallo a hankali a hankali ta dunga shigo da kayan su tana ajewa a coridor sae da tagama tass snn ta rufe kofar bayan ta gyara parkin din motar... Duk da ko ina a share yake bata yarda su zauna a kasa ba.. Cikin kayan su ta dauko morning fresh ta shiga toilet ta wanke sa tass snn ta juna ruwan zafi a heater kafin yy zafi ta share ko insa harda wardrobe din dake jinkin bangon dakin gida biyu snn ta juye ruwan zafin ta dubi Ammar da idon sa yake a lumshe tace "yallabai wanka" kallon ta yy sae kuma ya lumshe idanu hakan yasa ta fara kokarin cire masa kayan sa kanta a kasa dagashi sae singlet da boxers ta turasa zuwa toilet din ita kuma ta fito ta sanya cuttons  na windo dana kofa snn da saka kayansu na sakawa da kayan tea dinsu a cikin wadrope Sae a lokacin ma ta kula jakar da kamal ya saka masu kudin ita a wardrobe ta saka ta snn ta fito masu da silipas irinsu gas heater da yan kayan girkin da ta dako ta age su a corridor... Ta shimfida bedsheet da jera pillo da blanket ta fesa turaren kamshi nan da nan dakin ya dauki kamshi.. Ta juna ruwan wanka ta ita ma snn tayi masa knocking kafin ta tura ta shiga ta yafa masa towel snn ta turo shi shida kansa ya shafa maisa ta dauko masa kayan bacci ta taimaka masa ya saka bayan ta feshe sa da turare  snn ya dauko abincin da tayi masu ordering kadan yaci duk tafiyar da Suka sha babu yanda batayi ba da ya gara amma yaki sae tabasa drink babu laifi yasha ta basa ruwa yasha snn tace kayi alwala ya lumshe mata idanu ta juyar dashi gabas ya fara sallah ya yanda yake  Ita kuma ta juye ruwan ta ta ta kai toilet snn taxo tasaka towel ta maida hijab dinta snn ta shige toilet har ta fito bai gama rama sallar ba a tsana ke ta shirya cikin kayan baccin ta snn ta maida hijab snn itama ta tayar da sallah duka kasaru tayi tana idarwa ta fara addu'o'i ta dade tanayi kafin ta dukar da kanta dan har wani sara mata yake tunda take bata taba jin wahala irin ta yau ba ko dogo driving bata taba ba sai sau daya shima da zasu bauchi ne wajen momy Amina ita da faruk yabata tayi... Tanasan da a gida ne tayi irin wnn wahalar har ciwo sae tayi... Dagowa tayi suka hada ido da Ammar ta kakalo murmushi tace "bari na kwantar da kai nasan ka gaji tsare ta da ido yy itama kallon sa ta tsayi dan tasan da yana so zai lumshe mata idanunsa a hakali tace "ko kana bukatar wani abu" kallon abincin yy snn  ya kalle ta ta kalli direction din abincin dauko wa tayi ta saka spoon ta debo ta kai bakin sa ji bude bakin yy ta marairaice "me kk so pls" ya kalli abincin ya kalleta tace "na ci kk nufi" ya lumshe mata idanun sa tayi murmushi tare da langwabar da kai "nifa bana jin yunwa" ya tsare ta da kyawawan idanunsa tayi kasa da kanta dan baxata iya jurar kallon sa ba a hankali ta fara cin abincin duk yunwar da take ji bata jin dadin abincin turawa kawae take dan da ta dago zasu hada ido saeda ta cinye kadan ta sha drink da ruwa snn mike ta dauke take away din ta kai corridor sauran drink din kuma ta aje gefen katifa dawo gaban sa tace "na hada maka tea" kallon ta yy sae kuma ya juya kwayar idon sa zuwa wani direction din tayu murmushi snn tace "ok zaka kwanta ai" ya lumshe mata idanunsa hannu sa ta kama ta rike sa sosae tana jin yanda jikin sa ke rawa yana dafe shoulder dinta har ta karasa dashi saman katifa ta kwantar dashi tare da rufa masa blanket tace sleep tight" ya lumshe mata idanu tayi tayi murmushi tayi snn ta mikedan karamin Quran dinta dake cikin jaka tauko ta fara karantawa cikin muryar ta me dadi Ammar ya lumshe idanunsa sa tayi awa daya snn ta tashi shafa'i da wuri tayi ta dade tana addua snn ta tashi ta juyo tana kallon sa idanun sa a lumshe tunanin yanda zata kwanta wae yau itace zata katifa daya dashi gashi babu wani blanket din bare ta shimfida a kasa rokon Allah take Allah yasa yy bacci da ba gane masa kk ba idan ya lumshe idanu tana kokarin cire hijab dinta taji shigowar motoci kida sae tashi yake gaban tane yy wani irn faduwa can kuma tafara jin hayaniyar mutane kamar muryar mata tayi karfin halin fita corridor ta daga labulen motoci biyu ne suka shigo kuma tanajin karar wasu a waje matane suka dunga shigo cikin wata irn shiga da ka gansu kasan daga club suke ko wace ta cakare  kusan su bakwae sae maxa biyu da suka fito daga cikin motocin biyu wata a cikin yan matan tace "jar uba Kyauta kinga wata matsiyaciyar mota " juyawa wacce aka kira da kyauta tayi ta kashe wani ture kaga tsiya ta wani idanu "kutt wayyo gsky duk wacce ta kamo wnn ta kamo nera ai tunda nake ban taba ganin kalar motar ba tunda nabar kano rabona da irin su gsku dagani mai motar nan millonear ne" shewa duk sukayi ko wacce ta nufi dakin ta a tsorace khadija ta dawo tana tunanin wnn wane irin gidane da sauri ta cire hijab dinta ta daga blanket ta shiga sosae da matsa jikin Ammar dan har zasu iya shakar numfashin juna runtse idanu tayi jikin ta na rawa tana karanto addua a haka har bacci ya dauke ta.. Ammar ya bude ido yana kallon kyakkyawar fuskar ta ya dade yana kallon ta kafin ya maida nasa idon ya lumshe..  
  More comments more typing... ✍️
*#VOTE*
*#SHARE*
*#COMMENTS*

✨✨✨
*NAFEESA A GUGA*
😍😍😍😍😍😍😍😍

SABODA DUNIYA Where stories live. Discover now