Part twenty two

46 5 0
                                    

Typing~~~~📱

*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*

'''(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)

   🌼 *Saboda* *duniya* 🌃

Writing by......
<<<<≤<≤<<<<<<<<<<<<
*Annafie*💗

07051376476

Nafeesa A Guga @ wattpad

*bismillahir rahman  rahim*
Page 42⏩43
  🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

Kakalo murmushi tayi kafin ta karasa inda yake duk da idon ta cike yake da hawaye tace "sannu ya jikin" har lokacin kallon ta yake baidae ce komai ba ... Kamal ne ya shigo dakin fuskar sa da damuwa karasowa yy ganin  Ammar ya tashi yace "Ammar" duban sa Ammar yy ba tare da yace komai ba kamal yace "are  you feeling pain anywhere" dauke kai Ammar yy ba tare da yace komai ba Khadija tace "bari na hada masa ruwan wanka" daga haka ta nufi toilet shi kuma ya fara taimaka masa ya tashi zaune runtse idanu kawae Ammar yy yana jin zafi a jikin sa ya taimaka masa ya rage kayan jikin sa.. Khadija ta fito tace "nagama bari naje na sama masa abinda zaeci daga nan kaga sae na hado da kayayyakin da zamu bukata...  Kamal ya gyada mata kai daganan ya dauki waya yy wa sarkin mota magana aka cewa zai maida khadija ta dauko wasu kayan amfani... Daga nan kuma ya fara kokarin sakko da Ammar tana nan tsaye da tana kallon su da taimakon kamal yake takawa Ammar duk da haka jikin sa rawa yake yana cizar lips dinsa na kasa kai da ka gani kasan yana jin azaba.. Ficewa tayi.. Sarkin motane ya mayar da ita part din yareema.. Abu mai sauki kuma wanda zaiyi wa mara lafiya dadi ci ta dafa masa sai ta zuba ruwan zafi a flacks  ta saka a basket snn ta dauki kayan tea dan tasan zasu iya bukata a kowane lokacin.. Bedroom din Ammar ta shiga sae da ta gama bin ko ina da kallo duk da baya nan har ynx akwai kamshin sa a dakin closet ta tude ta fitar masa da kaya marasa nauyi da na ciki tunda bata san iya kwana kin da zasu dauka acan ba. Snn ta daukar masa creams dinsa body sprays da perfumes duk ta saka a jaka.. Itama taje ta dauko nata duk abinda tasan zata bukata... Ta hada komai tafito dasu sarkin mota na ganin ta yaxo ya kwashe ya saka a mota.
Koda ta koma ta samu har Ammar yy wankan sarkin mota ya aje kayan yana ma Ammar sannu.. Shide baice komai ba sae binsa yy da idanu har ya fice da taimakon kamal ya saka kayan ita kuma tana duke tana hada masa tea. Kamal ya gyara masa zama snn yace zo ki basa tea din.. Matsowa tayi jiki a sanyaye ta xauna jefen sa ta fara basa tea din kamal na zaune gefen su shima yana kallon sa cikin tausayawa.. Can yace "khadija da takun kowa da zae shigo domin duba Ammar kar ki yarda da kowa  snn kar ki yarda wani yace zai taimaka maki akan abubuwan da suka shafi mijin ki ko girki karki yarda wani yasa maki hannu kuma ya zamana koda yaushe kina tare dashi karki barsa shi kadae ko daedae da minti daya ne domin hakan zae sa a aikata masa abinda baki tunani ya kasance koda xaki bar dakin nan ni ina nan bayan ni karki yarda kowa yy wani abu da ya shafe sa duk da nasan shima baxai yarda ba amma bai da lafiya ynx za'a iya fin karfin sa pls khadija ki rike amana bashi da kowa sama dake a ynx za'a iya yin komai domin a salwantar da rayuwar sa..." Shiru khadija tayi saedai dukkanin hankalin sa na garesa hawaye kawae take yi cike da tausayin Ammar.. Aje cup din tea din tayi ta dauko abincin shide Ammar baice komai ba.. Khadija tace "har ynx Abie shiru bai dawo ba" Kamal ya furzar da iska mai zafi sann yace "dazu daga gurin sa nake naje akan maganar lafiyar Ammar amma abun da naji babu dadin ji hakan ya tabbatar min da an shiga tsakanin abie da dansa because he never show I don't care to his beloved son sai nan lokacin da yake tsananin bukatar taimakon sa" dukkanin sa kallon sa suke har Ammar. Kamal yace "cigaba da basa Abincin" zata basa ya dauke kai still looking at kamal Kamal yace "kaci mana Ammar" Ammar ya dauke kai snn ya kara kallon Kamal.. Kamal yace "ko na kira maka mummy" Ammar ya lumshe idanunsa snn ya bude.. Waya kamal ya ciro yy dialing numbern mummy yasa a H-free bugu biyu ta dauka lumshe idanu Ammar yy jin muryar mahaifiyar tasa suka gaisa da Kamal snn yace "mummy ya maganar lafiyar Ammar naji har ynx baki ce komai ba" tace "me maimartaba yace a kai" cikin sanyin murya kamal yace "cewa yy baxa'a fita dashi ba tunda ni likita ne mene amfanin karatuna ai nima zan iya kula dashi kuma mummy ba fill dina bane bakuma asan dalilin cutar ba and mum this is a very serious issue that  we have to show consine mummy yakamata muyi wani abu Ammar yana bukatar taimako yana wani nasa a kusa dashi tun daxu da Abie yabar nan har ynx bai dawo ba shine nace ko mutaho nan... " da sauri mummy tace "ku taho kuyi me kamal mene Amfanin matar sa ita baxata iya kulawa dashi ba dole saemu snn duk wani treatment da za'a masa anan nan ma za'a iya masa idan kai ba fill dinka bane ai akwae likitoci dayawa anan zan baka shawara ka bi abinda mahaifin sa yace don yafi kar ka kara kirana akan wnn dalilin and kar wani ya kira yan uwansa ya fada masu karda hankalinsu ya tashi kai da ita khadija baxaku iya kulawa dashi bane" yace "zamu iya mummy" tace good Allah ya kara lpy" a sanyaye yace "Ameen" trying hard to stop his tear direction din Ammar ya kalla yaga ya jingina da pillow idanun sa a lumshe hawaye na zubowa.. Shima goge nasa hawayen yy snn ya dauko drugs dinsa yana basa babu musu ya karba kamal ya gyara masa kwanciyar sa snn ya dubi khadija da ta dukar da kanta tana kuka kasa kasa..
  Yace muje waje khadija daga haka ya fice a sanyaye ta tashi tabi bayan sa zaune ta samesa saman resting chair dake baki ward din tsaye tayi ta kasa cewa komai duban ta yy snn yace "have a seat" zaunawa tayi kanta a kasa shiru yy na wasu yan lokaci kafin yace "kinga abinda nake fada maki ko" ta gyada masa kai yace " lallai idan kana da rai zaka sha kallo ki dubi irin soyayya dake tsakanin Ammar da mahaifan sa amma an raba shi dasu a lokacin da yake bukatar su tabbas akwae wani abu a kasa sae dae mu dage da adduar snn kuma musanya idanu akan shige da fice kowa dan dama kadan ake jira a salwantar da rayuwar sa inshallahu nan bada jimawa ba zan fitar dashi kasar India domin zaman sa anan hadari ne yana fadin haka ya mike khadija tace wae duk saboda me suke masa haka.. Wani murmushi kamal yy snn yace "SABODA DUNIYA.. Ni xanje in duba masa wasu drugs kar kiyarda da kowa ko doctorn da ke dubasa Dr.Irfan ki saka idanu a kansa" tace "toh" daganan ta tashi ta koma dakin" Alwala ta dauro tayi sallah raka'a biyu snn ta daga hannuwan ta sama tana adduar "ya Allah kana ganin bawanka bashi da wani gata da ya wuce kai ya Allah kabasa lafiya karaba sa da duk wasu makiya... Haka taita adduar tana kuka tana mika ma Allah kukan ta tayi 30 talatin a haka ta juyo sukayi ido hudu da Ammar....
Sosae khadija da kamal suka dage wajen kulawa da Ammar komai da taimakonsu yake da ko tsayuwar minti daya baya iya ye tuni jikin sa zaifara rawa zama ma sae ya jinjina da wani abun kamal ya dage sosae wajen basa magunguna yayinda khadija ta dage da addu'o'i  ba dare ba rana har yau Abie bai sake takowa xuwa inda suke ba hakama ma mommy bata sake kira ba  dada kam kullum sae taxo duba sa da tawagar ta ko daya hakalin khadija bai kwanta da ita ba... Snn babbar damuwa khadija bai wuce yanda har yan gidan su Abba da ya Auwal da sauran su sunsan halinda take ciki babu wanda ya kara kiranta yaji ya jikin mijin ta yau kwana uku knn da kwanciyar sa wayar ta ta dauko ta kira Abban ta yana dauka suka gaisa ya tambaye ta ya mai jikin sai ta fashe masa da kuka yace " subahanallah meyafaru" tace "bayan babu wanda ya kirani yaji ya jikin sa kowa ya share ni" yace "to mekike so mu maki bayan munxo mun dubasa kuma nasan yana samun kulawa" tace "to  Abba babuai kulawa dashi fa sae mu nida kamal har sarki bai zuwa inda yake" yace "to mu idan munxo me zamuyi masa?" Shiru tayi tana sauraren sa da mmki. Ya cigaba "so kike mu saka sa gaba mui ta kallo shima sarkin idan yaxo mai zae masa sa kinda gaki me kuma yake bugata kar ki kara kirana da irn wnn maganar nama fada maki daga haka ya kashe wayar bin wayar tayi da kallo da mmki sae kuma maganganun kamal suka fado mata share hawayen ta tayi ta juya sukayi ido hudu da Ammar.. Kafin tace wani abu an bude kofar an shigo Dadace Ammar yy saurin rufe idon sa dan inba khadija da kamal ba babu wanda ya bude ido a gaban sa Khadija ta kakalai murmushi Dada tashigo cikin shigar ta ta alfarma sae kamshi take bayin ta a waje suka tsaya dan kamal ya hana kuma ta barsu ne gudun karda a kawo wani zargi.. Khadija ta gaisar da ita Dada ta zauna batare da ta amsa ba tace "ya mai jikin" Khadija tace "da sauki" jinjina kai tayi snn tace "wani shirye shiryen kamal ya yanke akan sa" batare da ta kawo wani abu ba tace "yace za'a tafi dashi India" da sauri Dada ta kalle ta sae kuma ta dake tace "yaushe" ganin yanayin ta saeda gaban khadija ya fadi kafin tace wani abu aka bude aka shigo Kamal ne ganin haka yasa Dada ta mike tace "to Allah ya kara lpy kamal khadija bari naje na baro kausar itama ba lpy" tana fadin haka ta fice.. Binta da kallo kamal yy dan yaga kamar she's lose of control. Karasa shigowa Kamal yy yana kallon khadija snn yace "me yasa naga yanayin umma a haka" khadija ta fada masa yanda sukayi... Kamal ya dafe kai tare da zaunawa yana karanto salati tace meyafar Dr" kamal yace "kin rusa mana komai wann reaction din nata dana gani ya nuna min akwae wani abu a kasa a kwae abinda take shiryawa ynx tafiyar mu ta rushe bani da wata idea nasan da Ammar ne da ynx ya sama mana mafita karasawa yy gaban gadon Ammar wa riko hannun sa  hawaye a idanun sa yace "frnd I've no idea to save you bnsan me umma ke shiryawa ba wnn karon Allah kadae yasan shirin da tayi akanka pls frnd ka tashi ka bamu solution I don't wanna lose you pls Ammar ka tashi sae kuma ya fashe da kuka Ammar ya lumshe idanu hawaye suna gangarowa khadija ma kanta kukan take... Kamal ya tashi jiki a sanyaye ya dubi khadija kinga ki kwantar da hankalin ki ynx bari naje na nuna wa Dr irfan wadan nan drugs din wani doctor ne ya rubutamin su.... Yana fadin haka ya wuce office din Dr irfan.. Yaxo zae tura knn yaji magana kasa kasa kamar ta mace kasa kunne ya karayi jin muryar Dada ya waro idanu yaji tana cewa  "irfan wnn wace irn bnxar magana ce yaxa'ae musaka aiki ka kawo mana cikas tun jiya fa muka baka alurar nan amma ka kasa aiwatar mana da aiki kasan shekara nawa na dauka ina jiran wnn damar.. Dr irfan yace "ki kwantar da hakalinki ranki ya dade matsala daya ce shine yanda Dr kamal ya dauki serious action akansa ne amma inshallah daren yau zanyi komai gobe da safe sae dae kuji lvrin mutuwar sa dan nagama shirya komae.. Kamal ya waro idanu cikin tashin hankali muryar sarkin fada yaji yace "kar ka bata mana aiki dan kaga so suke si fita dashi kasar India" a mugun fusace Dada tace "ina rayen zasu fita dashi wata kasa ai sae dae idan bana numfashi na dade ina jiran wnn dama bn samu ba sae wnn lokacin wlh kaji na ratse sae naga bayan Ammar a wnn lokacin shi kuma kamal idan yasan wata ai baisan wata ba sanda naje wajen malam hakalin na baikawo min wani kamal ba iyayen sa kawae nake tunani ynx kuma tunda nasamu wnn damar ko za'ayi yaki a cikin kingdom din nan sae na cika burina.. Dr irfan yace kar ki damu na gama shirya komai a yau din nan.. Sarki fada yace "kar ki damu Rankiyadade sarautar GADANGA ta jinin ki ce babu wanda zai karbi sarauta nan wanda ba jinin ki ba saedae idan bana raye.. Da sauri kamal da yagama jikewa da zufa ya juya yana kokarin jan kafafun sa da suka masa nauyi wani irin jiri na kwasar sa. Da sauri ya labe jin an bude kofa an fito sune suka fito runtse idanu yy yana dauke numfashi dan kar su gansa....
More comments more typing... ✍️
*#VOTE*
*#SHARE*
*#COMMENTS*

✨✨✨
*NAFEESA A GUGA*
😍😍😍😍😍😍😍😍

SABODA DUNIYA Where stories live. Discover now