Typing~~~~📱
*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
'''(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)
🌼 *Saboda* *duniya* 🌃
Writing by......
<<<<≤<≤<<<<<<<<<<<<
*Annafie*💗07051376476
Nafeesa A Guga @ wattpad
*bismillahir rahman rahim*
Page 11-12
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼Farida taja khadija xuwa daki yayinda suka ma can suka cigaba da tattauna yanda bikin zai kasance.... Baba Rashid yace a hada auren dana su farida a lokacin aka Kira big dady yaxo aka tsaida maganar aure wata biyu karsheb first semister dinsu tinda abin duk na gida ne.....
Tundaga ranar hankalin khadija a tashe yake kullum cikin kuka ita damuwar shin metayi wa yan uwan ta ne sukai mata wnn tsanar me ta tare masu ynx shknn sun raba ta da usman knn har ga Allah tana kaunar sa, ynx kowaye wanda zata aura koya halinsa yake... Kullum cikin kuka take ga habaici da matan ubanta ke sakar mata ita kadae tasan take ji amma bata kula su ynx basu bane a gaban ta.... Ko a sch bata sakin jikin ta har su mufeeda idan sun xo duk abinda zasu fada bata kula su..... Abba ne ke lallashin yana bata baki akan ta kwantar da hankalin ta da yaya Auwal Sae fadila da farida da suke kokarin kwantar mata da hankali hakama husna kullum saeta kira waya....
Abba yabama Aneesa lokaci ta fito da miji inba haka ba zae xaba mata da kansa...
Hajjo da kanta taxo ta dauki khadija ta maida ta gidan ta dan tace hankalinta zaifi kwanciya acan... Kuma Alhmdllh hankalin ta nadan kwaciya dan can babu me takura mata kowa yana son saka ta farin ciki barin ma faruk da kullum yake nishadantare da ita Abba, yaya Auwal da farida ma kullum suna kan hanyar gidan fadila ma na kwantar mata da hankali.. Ita sae take gani ma ganar auren kamar da wasa ne dan tunda aka saka ranar auren sau daya baba Rashid ya kara zuwa.... Hakan kam yana damun su Abba gani suke kamar abin baxai yiyu ba suna dae shiri ne amma gani suke kamar abin baxai yiyu ba... Ana yin hutu amma tace su shirya ita da farida suje hutu can gidan su husna wajen momy.. Ai kam sunji dadin haka
Ranar da suka je husna tayi farin cikin ganin su dama duk kadae ci ya isheta ga daumuwa.. Ynx kam khadija batada wani damuwa dan gani take ita kamar bnda ita su farida kam harwata yar rama sukai itakam har wani dan cika take ga momy na masu gyara saeta kara wani haske ta kara murjewa idan su husna na damuwa sae ta tasa su taita masu dariya usman kau ta cire shi a babin rayuwar ta gani take kamar ci gaba zatayi da karatun ta....
Ana sauran sati biyu biki suka dawo a gidan hajjo suka sauka su umma na duk sun dawo nan dan gidan hajjo babban gida ne kowa yanada daki a gidan.... Sun dawo da kwana biyu matar big dady ta kawo lefen da aka hada na mujaheed wato na farida knn komai masha Allah kowa yana ta yabawa... ... Washe gari kuma aka kawo na yaya Auwal shima ya birge sosae domin umma da Abba sun fitar dashi kunya komai masha Allah... Na khadija ne kawae ba'a kawo ba su mama sae yada mata habaici suke.. Ita dae bata damu ba ita hakan ma dadi yake mata dan bason aure take ba. Su husna kam kullum cikin damuwa suke... Wasa wasa aure fa yana ta matsowa Amma babu wani abu daga can dangin mijin khadija....
Gida ya cika da yan uwa da abokanan arziki domin kowa yaxo domin taya murna hajji zata aurar da jikokin ta har biyar...
Har ranar daurin aure basuji komai game da wadan da zasu auri khadija abin yana cin ransu Abba amma sun danne summa cire auren khadija... Ana idar da sallar juma'a aka daura auren ya ya auwal da husna, ya mujaheed da farida... Sae guda ta kaure a cikin gida dan ana ji daga masallacin khadija naji babu ita tayi hamdala.
Can kau a masallaci Ana gama daura na mujaheed Abba an tabo sa daga baya yana juyawa sae yaga baba rashid cikin shiga ta kamala har zaiyi magana Baba rashid ya daka tar dashi da fadin "zomuje sirikin khadija yana son ganawa da mahaifin surukar sa" cikin mamaki Abba ya mike tare da yima big dady da wani aminin sa bismilla.... Cikin mmki suka biyansa a part din big dady suka je dan babu mutane a can baba rashid yace " inaso a Kira hajjo" yafada yana kara waya a kunnesa shiru yayi kafin yace "to kun kusa... Allah ya kawo ku lpy"
Hajjo ce tashigo da sallama tana mmkin wann kiran da aka mata tana ganin baba rashid ta waro idanu zatayi magana wayar baba rashid tayi Kara tashi tsaye yy kafin yace "ina xuwa" snn ya fice suka bisa da kallon mamaki
can kau waje kowa sae kallon motocin da suka zo yake kowa na mmki ganin kamar tawagar sarkin masarautar *GADANGA*....
A hankali mutanen ciki suka fara fitowa manya manyan mutane na masu shiga ta alfarma da fadawa....nan suka fara baxa manyan riguna a saida sarki ya gama fitowa sann suka mude kyakkawar fuskar kamilin sarkin ta bayyana nan da nan guri ya natsu kowa ya tsaya ganin ikon Allah yan uwa sae mmki suke su yaya Auwal ma sakin baki sukai suna tunanin abinda ya kawo sarki gidan su.... Gurin yayi shiru babu abinda kk ji sae kirarin da ake ma sarki...
Baba rashid ne yaxo nan da nan su aka fara masa kirari... "Barka da zuwa amin tacce sarki yana farina cikin ganin.... A cikin takun sarauta suka fara karasawa cikin gidan su yaya Auwal ma da su sadiq, mujaheed, da faruk suka bi ayari dan kansu duk ya gama daure wa....
Suna shiga part din big dady su Abba suka mike cikin mamaki da fargaba.. Sae kirari ake masa tare da baxa masa riguna ya xauna... Babu shiri su abba suka zube suna kwasar gaisuwa sarki ya girgiza kai baba rashid ne yace ku samu guri ku xauna zama sukayi jikin su na rawa... Wani aminin sarki ne ya fara magana, sarki ne da kansa yaxo domin nema ma dansa yariman masarautar GADANGA auren yarku khadija... Kasa magana sukayi baba daya mmki da fargaba ya cika su... Sarki ne ya fara magana cikin muryar sa mai taushi wacce ta jiku da sarauta yace "ina fatan zaka amince da yarka ta zama surukata domin inaso a daura auren ta da dana ynx ba sae anjima ba kuma dan domin shine Wanda Baba rashid ya roki alfarmar auren ta kuma kula bashi Baba rashid Amintacce na ne kuma nine na turosa dominwya nema wa dana auren Yarka... Ynx haka muna tare da sadaki da komai...
Gaba daya su Abba suman zaune sukayi gani suke abin kamar a mafarki wae yau shine gashi ga sarkin babbar masarauta kuma shine mahaifin mijin da mafi soyuwar yarsa zata aura.... Wani ba fade ne ya katse tunanin su da fadin "sarki yana buka tar da ku tashi mu shiga masallaci a daura aure...
Baba rashid ne yace "muje ko sarki ya mike suma suka mike jiki a sanyaya....
Kamar da wasa yan cikin gida da yan waje wadan da suka zo daurin aure suka ji ana sake wani daurin auren wakilin amarya dana ango.. Gurin yayi tsit kowa yana jira yaji auren wa za'a daura da har sarki zai halarta a wannan rana kowa ya zaku yaji haka maka cikin gida kowa ya kasa kunne..... Nima na kasa kunne
Kamar saukar aradu suka ji daurin auren..... *ALIYU ABDUR-RAHMAN GHADDAFI DA KHADIJA MUHAMMAD SAMBO* a bisa sadaki sisin gold......
A tare Aneesa, Husna, farida da fadila da sauran mutanen dake wajen suka furta *PRINCE AMMAR*...?
Khadija kam ji tayi gaba daya ji da ganin ta ya dauke....
More comments more typing.. ✍️
*#VOTE*
*#SHARE*
*#COMMENTS*✨✨✨
*NAFEESA A GUGA*
😍😍😍😍😍😍😍😍
YOU ARE READING
SABODA DUNIYA
RomanceLabarin yana dauke da abubuwan bn mmki.. Labarine akan wadanda duniya ta rufe masu ido sun manta Allah ne mai komai snn yana dauke da salon soyayya mai bn sha'awa.. Zai fadakar kuma ya nishadantar daku