Typing~~~~📱
*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
'''(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)
🌼 *Saboda* *duniya* 🌃
Writing by......
<<<<≤<≤<<<<<<<<<<<<
*Annafie*💗07051376476
Nafeesa A Guga @ wattpad
*bismillahir rahman rahim*
Page 15⏪16
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
Suku ku khadija ta tashi jikinta duk a sanyaye idan ta tuna yau zata bar gida duk da yan gidan ba wani shiri suke ba amma xatayi kewar su musamman ma Abban ta hajjo farida da ya ya Auwal gashi kuma xata je inda aka fi karfin ta inda bata san kowa babban takaicin ta ma shine batasan inda cigaban karatunta ya kwana ba....
Gidan har ynx da mutane kowa yana so yabama idonsa abinci akan auren khadija da yarima... Dan wasu har ynx basu gama yarda cewa jinin sarauta zae auri khadija ba musamman ma yan gida da zuciyar su fal take da bakin ciki..... Aneesa kam har yau kuka take tana danasanin kin bin umarnin Abban ta ba... Umma ce tace "ke ki kwantar da hankalin ki hauka sarki yake da zae aurawa mara asali dansa kuma mafi soyuwa a wajen sa jinin sarauta gaba da baya ai yafi karfin ta nesa ba kusa wlh ... Ita dae Aneesa bata tanka ta ba....
Karfe 4:32 tawagar gidan sarki suka shigo cikin anguwar da tarin motoci nagani na fada wata daga cikin hadimai ce ta shiga cikin gidan inda duk jama'ar dake wajen suka bita da kallo dan daga gani daga masarauta take... Tace Hajiya Amina nake nema.. Kafin suyi magana momy ta fito daga bedroom din hajjo tace "gani sannu da zuwa" hadimar ta gyada kai kafin tace "muna neman iso yan uwan yarima suna son shigowa" momy tace "marhabun barkan ku da zuwa bismillah" khadija dake ciki su fadila suna ta fama da ita akan taci abinci gaban ta yy wata muguwar faduwa.. Can kau fitar matar bada jimawa ba saega hadimae sun fara shigo da akwatuna masu kyau sae da aka shigoda har guda ashirin da hudu... Wata kyakkyawar yarinya ce kimanin shekaru sha shida ta shigo tana rike da hannu wani yaro da shekara biyar dukkansu sun sha kayana alfarma kowa dake parlorn ya bita da kallo fuskarta dauke da murmushi tace "ina amaryar tamu take" fadila da tafito ynx tace "shigo gata nan" Rahma ta nufi inda fadila take da murnar ta suka shiga bedroom din... Anan suka iske khadija ta tasa abinci gaba idanun ta cike da hawaye. Rahma na ganin ta ruga tare da rungume ta "barkan ki da zuwa cikin zuri'ar mu" ajiyar xuciya ta khadija ta sauke tana kallon kyakkyawar yarinyar... Rahma ta sake ta tana murmushi kafin tace "oh baki sanni ba ko am am Rahma the last born dinsu mijin ki" murmushi khadija ta kalalo Rahma tace "Autyn mu kina da kyau sosae gsky zaku dace da yaya Ammar" yarinyar ta birge khadija sosae diyar sarki ce amma babu ruwanta da girman kai khadija tace "ai duk kyauna ban kaiki ba" waro idanu Rahma tayi xatayi magana momy da hajjo suka shigo wata kyawar mata da xata girki ya sadiq da yar budurwa da zatayi sa'ar Aneesa na biye dasu suna cikin shiga ta alfarma fuskar su dauke da walwala suna ganin khadija suka kara fadada murmushin su Aunty fati ta xauna kusada khadija da sauri khadija ta fara kokarin zamewa kasa Aunty fati tayi saurin rike ta "no yi zaman ki kanwar mu.. Masha Allah" khadija ta gaisar da ita kanta a kasa" Aunty fati ta amsa tana shafa kanta kafin tace "kina nan auta tacikaki da surutu ko" murmushi kawae khadija tayi tana mamakin saukin kai irn na mutanen" yayinda Rahma ta tura baki "kai aunty gaisawa fa kawae mukayi.... Sameera ce tace "ai ansan halinki da surutun ne" dariya tayi kafin tace "to nida baki na... Ita dae khadija najin su sae taji sun birgeta babu ruwansu amma ita ba wann ba shin shi uban gayyar shima haka yake ko akasin haka....?
Anan suka ci abinci mai rada lpy tare da tursasa khadija taci babu yanda ta iya haka ta rinka tsakura tana ci badan tana jin dadinsa ba gaba daya kunyar Aunty fati take ji... Yayinda su kuma kowa yake kokarin nuna kulawar sa a gareta har dan karamin yaron aunty fati Shaheed wanda suka shigo tareda Rahma ya lafe a jikin ta..... Su mama da yaransu sae rawar kafa suke suna murnar karfi da yaji wacce bata kai har zuci ba dan wani tukikin bakin ciki suke ji a ransu....
Khadija cike take da kewar su farida dasu ya Auwal amma duk yau bataga kowa a cikin su ba sae ya Auwal shima tunda ya shigo yau da safe ya tilasta mata yi breakfast bata kara ganin sa ba duk da tasan yana cikin gidan yazama busy ne kawae...
Su ya Auwal ai kofa amaren su basu je ba tun safe suna gida hidima ta masu yawa ynx haka suna tare da iyalan sarki...
Har kusan bayan mangariba suna gidan inda hadimai suke tayi wa khadija wanka turaruka kala kala.. Duk wanda yaga lefen da akama khadija sae ya rike baki domin kau babu ce kawae ba'a saka ba gwala gwalai kam sunfi a kirga ga keys din mota har uku... Sae saka albarka akeyi yayinda xuciyar su mama kamar ta fito da bakin ciki kuma duk da wnn basu gama yarda cewa dan sarki ne ya auri khadija ba..
Anayin isha'i aka shirya khadija cikin kaya na sarauta sunyi mugun amsarta kamar itama jinin sarauta ce.... Khadija sae kokarin maida hawayenta take ganin abun kamar a mafarki wae zata bar Abban ta, hajjo da ya Auwal duk a yau... Part din Abba aka kaita inda a nan ta iske duk ilarin family din su idanun tane ya cika da hawaye. A hankali momy ta fara mata nasiha kamar mahaifiyar ta babu abinda take sai kuka daga nan hajjo da su yaya Auwal suka mata tasu mai shiga jiki snn big dady ma ya mata mai ratsa zuciya... Abban ta kam yy shiru kansa a kasa shi kadae yasan yanda yakeji a game da khadija, duk sanda ya kalleta a gidan yakan ji farin ciki yakan tuna matar sa, yau gashi xata tafi ta barsa itama ko wane irn zama zatayi acan Allah masani...idanun sa sun cika da hawaye da kyar ya iya bude baki Muyarsa na rawa yace "mamana Allah ya baku zaman lpy kibi mijin ki sau dakafa kizama mai hakuri snn kiyi koyi da dabi'un mahaifiyar ki Allah ya maki Albarka " abinda ya iya fada knn da sauri khadija ta dago tana duban sa jin yanayin muryar sa.. Cikin kuka tace "Abba na" kasa dagowa yy ya kalleta zuwa tayi ta rungume sa tare da fadawa jikinsa tana wani kuka... Kowa a gurin saeda ya tausaya masu idan kacire su mama da suka tabe baki.... Da kyar aka raba ta fada jikinsa.. Yana ji yana gani a ka fita da ita sae kuka take har aka shiga da ita cikin jerin motocin momy na zauna gefen ta yaya Auwal kansa saida ya xubda kwalla hakama hajjo da faruk....
Sunyi tafiya mai nisa kafin su isa cikin masarautar wacce ake ta shagali ana busa algaitu murnar xuwan amaryar yarima Nan ma sauda sukayi yar tafiya kafin motocin su isa part din yarima wanda kallo daya zakaiwa part din kasan an xuba dukiya dan tunkafin kashiga ma kasan cikin ya gaji da haduwa ...
Ai kam basu tabbatar da hakan ba saema da suka shiga ciki komai mai kyaune ka wani cool kamshi da ya hadu da sanyin A. C A sama dakin khadija yake dan haka aunty fati ta wuce dasu can nan ma bakarama dukiya aka zuba a ciki ba yan kawo amarya sun ba ma idon su abinci. Dan dama gidan sarauta da ban yake sae su mallaki abinda masu mulki basu mallaka ba... Yan kawo amarya basu wani jima suka tafi... Khadija kamar ta bisu haka take ji fuskar ta na rufe har lokacin da aunty fati ta kama hannun ta suka nufi part din Dada bayi na take masu baya...
A bedroom dinta suka iske ta kishingide cikin kayan alfarma kursum na gefen ta ga suna shan kayan marmari ga bayi nan a gefen su kowa da aikin da take.... Kursum na ganin su tawani hade rai yayinda Dada ta sallami bayin dake wajen sukayi godiya suna russunawa kafin su gaisar da su aunty fati snn su fice..... Aunty fati ce ta gaisar da Dada kafin Rahma kanka khadija a kasa ta gaisar da ita kursum ta bita da wata irn harara yayinda Dada ta amsa fuska ba yabo ba fallasa... Shiru tayi kafin tace "barkanki da shigowa masarauta mai tarin daula.. Gaki dae kinsha kayan sarauta kamar da gaske jinin sarauta bana talaka ba saedae ba jinin bace zadae a kiraki da matar dan sarki dukda baki can can ci ki zama matar sa ba dan babu jinin sarauta babu na talaka.... Talaka sae takala basarake sae basaraki.. Murmushin karfin hali aunty fati tayi kafin tace "umma kin manta duka Allah ne yayisu... " murmushin kasaita Dada tayi kafin tace "shi yayisu kuma shiya banbanta yayomun a masu mulki su kuma talakawa dan sahun jiwa dana rakumi ba daya ba kuma iya jarumtar rago a wajen karo da dan a kuwa yake ko dan uwansa rago amma bai isa ya tunkari zaki ba. ...
Shiru aunty fati tayi kafin tace "to umma muzamu wuce godiya muke mun barki lpy.... " tana fadin haka ta kamo hannun khadija da zuciyar ta tagama tsitsitsinkewa da kalaman Dada.... Har suka fito maganganun Dada suna yawo a tsakkiyar kanta to wacece wnn din ko mahaifiyar sa ce... ta sauke numfashi lallai kam ba'a rabu da bukar ba an haifi Abubakar... Knn kowane gida suna da nasu amanun dama ita tarigada tasan rijiya ba gurin wasan makaho bane......
More comments more typing...✍️
*#VOTE*
*#SHARE*
*#COMMENTS*✨✨✨
*NAFEESA A GUGA*
😍😍😍😍😍😍😍
YOU ARE READING
SABODA DUNIYA
RomanceLabarin yana dauke da abubuwan bn mmki.. Labarine akan wadanda duniya ta rufe masu ido sun manta Allah ne mai komai snn yana dauke da salon soyayya mai bn sha'awa.. Zai fadakar kuma ya nishadantar daku