Part thirty seven

65 5 1
                                    

Typing~~~~📱

*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*

'''(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)

   🌼 *Saboda* *duniya* 🌃

Writing by......
<<<<≤<≤<<<<<<<<<<<<
*Annafie*💗

07051376476

Nafeesa A Guga @ wattpad

*bismillahir rahman  rahim*
Page 70 ⏩ 71

  🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
Yau ne tafiyar Ammar  sai khadija taji kar yatafi gabadaya suku ku takejin ta kuma karfe goma jirginsu zai daga...
     Zaune take baking gado tayi tagumi fa hannu biyu tana tunani.. Harbata san lokacin fa Ammar ya fito daga wanka ba.. Karasawa yy inda take ya cire tagumin ya dago ya kalle sa sai kuma tayi kasa fa kanta.. Ya sunkuwa yana kallon fuskar ta yace "what's wrong with you" girgiza masa jai tayi baby tare fa tace komai ba.. Ya mike tsaye tare fa kamo hannun ta "kinga tashi kiyi wanka tym Na kurewa.. " baby musu ya mike ta shiga toilet  ya bita da kallo snn ya cigaba da shiryawa... Sanda ta fito har ya gama shirin sa... Ta nufi mirror lotion kadai ta shafa snn ta fesa body spray shi da kansa ya dauko mata kayan da zata saka.. Har ta gama shiryawa komai cikin sanyi take yinsa.. Ya kama hannun ta zuwa nan parlorn su ga breakfast nan an jera masu a dining.. Can ya nufa da ita   ya tilasta mata taci abincin turawa kawai takeyi  shima yanayi yana kallon ta da murmushi a fuskar wanda yanayi ne dan kawai karya karyar da zuciyar ta amma shima ji yake kamar kar ya tafi ya barta... 
Hannun ta ya kama suka nufi kasa a main parlor  suka iske sauran yan gidan har da aunty fati itama taxo  duk wanda kaga fuskar sa kasan yana cikin damuwa.. Ammar yaje ya rungume mummy kafin ya gaisar da ita da larabci ta amsa tana shafa kansa haka ya gaisa da kowa dake parlorn... Daganan kuma aka kwashi kayansa aka fita dasu suma duk suka fita.. Da motoci da yawa za'a tafi rakiyar su...
Mota daya Ammar da khadija suka shiga.. Jikin khadija a sanyaye... Suna back seat da ita dashi Hannun sa tasa ya kamo nata Tare da sakala fingers dinsa cikin nata.. Ta kwantar da kanta saman kafadar sa... Dayan hannunsa ya saka ta bayan ta tare da zagayo ta zuwa cikin ta hakan ya bata damar kwaciya saman chest dinsa.. Ya daura kansa saman nata still yana wasa da hannuwansu yace "this your mood make me feel discourage pls KO kwantar da hankalin ki mana babu abinda zai faru da ikon Allah.. " lumshe idanun ta tayi ba tare da tace komai ya zagaye ta da duka hannayensa snn yace "pls kimana Addua yanayin ki yana discouraging dina.. Haba kamar ba khadijar dana sani ba..." Shiru tayi tanajin babu dadi A haka har suka isa airport din.. Duk suka firfito.. families nan dayawa wadan da sukayo rakiya kowa ransa babu dadi.. Ammar ya nufi inda dan dazon sojojin suke kowa ya gansa saiya kame tare da sara masa.. Sunyi kusan minti biyar suna tattauna wasu abubuwan kafin kowa ya juyo domin yayi sallama da iyalansa....
  Ammar ya nufi wajen mummy da idanun ta ya cika da kwalla ta rungume sa "Allah ya tsaremin kai ya dawomin da kai lpy" can kasan makoshi ya amsa da "amin"... Su Aunty fati ma da waleed, sameera da rahma rungume sa sukayi suna masa fatan Alkhairi.....
Juyowa yayi ha khadija da take ta danne kukan da ke cinta.. Gab ya matso kusa da ita dan har tanajin saukar numfashin sa murya can kasa yace "I'll miss you badly".. Kasa tayi da kanta tana jin ba dadi cikin rawar murya tace "I pray god should give you power over them, may Allah protect you, as you leave peacefully and healthy may he bring you back.. that way.. Sai kuma tayi kasa da kanta tana jin kuka da kyar da iya dagowa tace.. "And.. Lastly I wish you a very wonderful journe... Bata karasa ba ta juya zata tafi saboda kukan da yaci karfin ta  yayi saurin rikota yare da janyo ta jikin sa.. Ta fashe da kuka.. Ya rungume ta sosae a jikin sa tana jin bugun zuciyar sa kamar yanda shima yake jin tata... Sun dade a haka kafin ta  rage kukan nata suna a haka har tayi shiru ta koma sauke ajiyar zuciya shima ita din yake saukewa tare da kai... Bakin sa daedae saitin kunnen ta yace... "I love you".. Runtse ido tayi tanajin kalmar har cikin kanta... Ya raba ta da jikinsa jin an fara kiransu hannu yasa ya share mata hawayen tare da kissing dinta a goshi.. Sann yace "ki kulamin da kanki." Ta gyada masa kai ya kama ta ya kaita hannun mummy snn yace "I'll be going" mummy ta saka masa albarka sann ya daga masu hannu  ya suma suna daga masa khadija kau kasa daga kai tayi.. Sai da aka dan jima snn ta dago suka hada ido dashi lokacin gab da zai shiga jirgin wani murmushi ya sakar mata yana daga mata hannu itama ta mayar masa da martani.. Idon ta a kansa har ya shige......
      ⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐
Khadija na jikin mummy har suka koma a dakin mummy ta kwanta tana ta tunani taji kamar ta bisa zuciyar ta duk ba dadi... Da kyar ta tashi tayi shirin makaranta suka tafi ... Ranar duk wanda yaganta sae yasan ba normal take ba ko abinci bata sosae..bunu bunu Ammar sae ya fada mata arai... Bata gane tayi kewar sa ba sai da taxo kwanciya taga ba ammar babu alamar sa. Taita juye juye take ta kamo pillow ta rungume amma duk da haka bataji kamar Ammar ba.. Ta runtse idanu tana hango kyakkyawar fuskar sa ya zuba mata sexy eyes dinsa  ... Tashi tayi zaune ta rike pillow tace a ranta tana tunanin ko yana ina jiran ynx kome yake yi ko sun hadu da yan ta addan  haka xuciya ta taita kawo mata tunanu barka tai masu kyau da marasa kyau... Ganin baccin bata ba mai yi wuwa bane yasa ta tashi tashiga toilet domin yin abinda zai amfane ta...
Alwala tayo tafara nafila... Snn ta fara rokon Allah akan ya kare mata mijin ta aduk inda ta dade har bacci ya dauke ta a inda take bata tashi ba sai asuba....
⭐⭐⭐⭐⭐⭐
Khadija bata san ta damu da Ammar ba sai ynx da babushi kullum cikin tunanin sa take.. Idan tana tuno rayuwar su sai tai ta murmushi  barin ma idan ta hango sa yana kyakkyawan  murmushin sa mai tsada wanda ba kowane ke iya ganinsa ba har rayuwar su ta kankakara tana tunowa .. Idan kuma ta tunawa cewa suna can tare da yan ta'adda duk sai zuciyar ta ta karaya sai ta zauna ta sha kuka snn tayi adduar Allah ya dawo da shi lpy yasa suci nasara akansu.... mummy kanta ta tausaya mata duk da itama kullum tana cikin kewar sa amma tasan mata daban ce.. Hakan yasa kullum take Kara janta a jikinta dan ta mantar da ita duk wata damuwa kowa a gidan cikin janta da jiki yake domin kau inhar zata zauna ita kadae to Ammar ne yake fado mata... Kuma jantan da suke yy tasiri sosae domin kau suna mantar da ita damuwa .. Sai taxo kwanciya ne komai yake dawo mata...
       ......................
Bangaren karatu kam ta dage  sosae dan tasan idan ammar ya dawo zaiji dadi idan yaga ta maida hankali dama gata ba daga baya ba wajen kwakwalwa....... Idan kau ta dawo gida koda yaushe tana tare da mummy dan bata barinta ita kadae har kitchen suke shiga tare da mummy tana kara nuna mata nau'o'in abinci kala kala    .. Su waleed suyi ta tsokanar ta wai tana kewar mijin ta mummy ce ke kare mata.. Kuma gaskiya suka fada dan kuwa yana can kasan xuciyar ta.. Ita har mmki ma take bata taba rike kowa haka ba a rai sai iyayenta...
Mummy ba kunya ta rinka siyo kayan gyaran jiki tanawa khadija gyaran gashi da sauran su.. Ai kuwa tuni ta kara murjewa tayi kyau    ita kanta har mmkin kanta take idan ta kalli kanta.. Tasan cewa fatar ta tana da laushi sosae amma duk da haka wnn gyaran yakara ta ta kara wani taushi ga santsi snn ga wani irin kamshi da take ko zaunawa tayi waje ta tashi sai kaji yana kamshi su Rahma suyi ta tsokanar ta....
Sati biyu na cika da tafiyar Ammar khadija ke tsammanin dawowar sa danni take kamar yayi shekara biyu gaba daya ta kosa taga kyakkyawar fuskar sa tare jin swt voice dinsa da tayi missn kullum cikin gyaran daki take  duk da ba nan take kwana ba dan tuni mummy tace ta koma kwana da sameera.. 
Shiru ammar bai dawo ba nan ta fara tunanin sati uku tana nan tana lissafi ammar har lokacin shiru.. Wann lokacin kuma zuciyar ta tafara karaya har Ammar yayi wata Amma bai dawo ba sosae ta damu dan hankalin ta ya tashi sosae wani lokacin sai ta je tasha kukan ta...

   Ranar tana zaune a dakin sameera gaban mirror tana duba dogon gashin ta da aka gyara mata sai sheki yake ga kamshi mai dadi ta yake fitar wa...
Toilet ta shiga tayi wanka bayan ta fito ta tayar da sallahr isha'i tana idarwa ta isha gaban mirror tana kallon kanta ganin yanda ta wani murje ta kara kyau duk da ita fara ce tasan ta kara haske.. Lotion ta fara shafawa tajin yanda fatar ta ta kara wani laushi da santsi...... Sameera ce ta shigo tace "Auntyn mu ki fito muyi" khadija ta lumshe idanun ta masu yalwar eyelashes tace "ohk ganin" kallon ta sameera tayi tace "wow wai kinga yanda kika kara wani kyau gsky idan yaya ya dawo zaice mun iya raino" murmushi khadija tayi wanda duka dimple dinta suka lotsa idan da sabo ta saba da tsonar su... Sameera ta fita ita kuma ta ci gaba da shafar da kamar mai tausayin fatar jikin ta... Tana gamawa ta dauko wata yar karamar rigar bacci ta saka tare da feshe jikin ta da turaruka..  Snn ta zumbula hijab ta fita........
Tana kusa da mummy dan koda yaushe idan zasu ci abinci mummy bata barin kowa kusa da ita sai khadija... suna cikin ci suka ga an bude kofar wasu daga cikin hadiman gidan ne suka fara shigowa da jakuna.. Da sauri duk suka mike waleed yace "Alhmdllh the prince is back" cikin tsantsan farin ciki ya fadi hakan.. Tuni gaban khadija ya fadi.. Tuni hancin ta yajiyo kamshin turaren sa... Bata gama tunanin da take ba taji sallamar sa cikin swt voice dinsa wacce tayi mugun missn kafin kyakkyawar fuskar sa mai cike da annuri  ta bayyana  yana sanye cikin uniform dinsa wanda suka kara fito a ainahin kyawunsa da jarumkarsa ya wani kara kyau da sauri su sameera suka ruga suka rungume sa cikin tsantsar farin cikin ganin sa.. Shima din rungume su yayi.. A lokacin ya dago ya kalli khadija da kyawawan idanun sa.. Idanun su suka sarke cikin na juna wani murmushi ya sakar mata tare da lumshe lumsassun idanun sa ya kara budesu a kanta...

  More comments more typing... ✍️

*#VOTE*
*#SHARE*
*#COMMENTS*

✨✨✨
*NAFEESA A GUGA*
😍😍😍😍😍😍😍😍

SABODA DUNIYA Where stories live. Discover now