Typing~~~~📱
*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
'''(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)
🌼 *Saboda* *duniya* 🌃
Writing by......
<<<<≤<≤<<<<<<<<<<<<
*Annafie*💗07051376476
Nafeesa A Guga @ wattpad
*bismillahir rahman rahim*
Page 40⏩41🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
Fadawa jikinsa tayi tare da fashewa da kuka.. Kamal kau duk ya gama rudewa shima ji yake kamar ya fashe da kukan yama rasa inda xae shiga. Mikewa yy ya fice da sauri..
Fuskar sarki dauke da kayataccen murmushi ya fito daga mota burinsa kawae yaga mafi soyuwar jarumin dan nasa snn yana mmkin abinda ya hanasu zuwa airport tarosa... Kirari aka fara yi masa jinjina kae kawae yake yana tunanin ta inda zae hango Ammar nafi yawa daga ciki sun fahimce sa dan indae Ammar yana gari maimartaba ya dawo daga tafiya shine gaba wajen dauko da .. Ana cikin haka sae ga Kamal a rude kowa binsa yake da kallon mmki suna kallon bayan sa.. Zubewa yy gaban maimartaba duk ya hada zu fa da kyar ya iya tattaro maganar bakin sa yace "Allah ya taimaki sarki yareema.. yareema. Maganar ta makale masa sae kuma ya fashe da kuka "Abie Ammarrr" tuni hankali Abie ya tashi cikin dakiya ya mikar da kamal suka nufi part din yareema..
Har lakacin khadija na nan yanda take ganin su ne yasa ta mike ta ja gefe but still crying... Hankali tashe yake kallon dan nasa ganin yanda aka zuba masa ruwa amma ko gizau baiyi ba jikinsa kansa rawa ya fara Baba Rashid yy patting shoulder dinsa "sarki calm down bari nasa a kai sa asibit" yana gani aka dauki dan nasa aka wuce dashi cikin hospital din dake cikin masarautar guri maimartaba ya samu ya zauna trying to calm his self...
maimartaba ne yake ta safa da marwa a bakin dakin da aka kwantar da Ammar wanda kwararrun likitoci suka duku fa akan sa kuma har ynx bai fardoba saedae an tabbatar da yana da rai da ka gansa kasan yana cikin damuwa khadija na zaune duk ta fita hayyacin ta haka kamal ma yana zaune sae kace ba likita ba ya kasa tabuka komai ... Dada ce taxo bayin ta na biye da ita fuskar da damuwa amma zuciyar ta fess bataki ba ya mutu ya ynx kausar na gefenta sae kukan take itama.. Tayi wa sarki sannu da zuwa dan sae ynx suka hadu jinjina mata kai yy ba tare da yace komai ba... Suna nan zaune har 10 amma ba wani lvr kowane likita ya fito saedae kaga yana hada gumi kuma da an tambaye su sae suce akan aiki suke hakan yana kara tsinka xuciyar maimartaba...
11 sha daya saura wani likita ya fito kamal yy saurin tarar sa "Dr wae har ynx babubabu wani improvement" yana cire hand gloves dinsa yace "be patience Dr kamal yareema yana nan da ransa kuma mun samu kansa ynx haka ya farfado saedae har ynx muna kan aiki ne kuma muna so musama masa hutu... Yana fadin haka ya wuce dakin na'urori.. Ajiyar zuciya kamal ya sauke ko ba komai ya samu relief shi kansa sarki kallo daya zaka masa kasan yadanji saukin damuwar sa duk da bai nuna ba Amma kallo daya zaka masa kasan yana cikin damuwa.. Khadija kam babu wani abu da taji burinta kawae ta gansa...
Wayar sarki ce tayi ringing ciro wa yy yana kallon screen din ganin mummy ce yasa gabansa yy wata irin faduwa domin kau yasan tabbas an samu munafikin da ya fada mata zaunawa yy dan tun daxu a tsaye yake ya daga wayar ya kara a kunne tare da sallama.. Ko sallamar bata amsa ba cikin tashin hankali tace "Abu Ammar what's wrong with my son" shiru Abie yy dan bae mezece mata ba kawae sae yaji ta fashe da "pls abu Ammar duk to me wae da gaske ne yana nan rai hannun Allah" a hankali yace "Farha" tace "na'am" yace "kin dai cewa Allah ke bada lpy da rashin ta ko" tace "eh" yace "kin san ciwo na kan kowa ko kuma kowaye kai Allah zai iya jarabtar ka dashi ko" tace "eh" "to danki adduar ki yake bukata wnn kukan bashi da amfani ummu Ammar" mummy ta share hawaye tace "to amma nide gobe zan taho ko a taho dashi nan" girgiza kai yy "no farha ki barshi a nan snn kiyi zamanki ynx nan Dr ke fada mun sun samo kansa kuma ya farfado hutu suke so ya samu kuma inshallah zae samu lpy he only need your prayer" nan yaita kwantar mata da hankali har ta hakura tace "ina matar sa duban sa ya kai inda khadija take har ynx bata bar zubar da hawaye ba sakawa yy a kira masa ita kanta kasa taxo inda yake tare da durkusawa ta gaishe sa ya Mika mata wayar yy kwatar mata da hankali mom din tayi kafin suyi sallama ta mika masa wayar shima kwantar mata da hankali ya shiga yi..
Batare da kowa ya sani ba Dada ta sulale daga wajen.. Can wani waje suka kebe ita da sarkin fada daka gansu kasan suna cikin tsantsan farin ciki Dada tace "dole ne nayi wa malam kyauta mai tsoka dan tunda nake ba'a taba mun aiki mai dadi kamar wnn ba naji dadin aikin nan.. Sarkin fada yake "hakane Allah ya taimake ki malam yana bukatar kyauta mai tsoka sae wani hanzari ba gudu ba inkin kula har ynx kan iyayen nasa yana kan sa dubi fa yanda suka tashi hankalin su" shiru Dada tayi sae kuma tace "dole ne su fita harkar sa suma manta suna da wani da Aliyu bama su kadae ba kowama inaso ya manta da wani yareema kar ya shiga sabgar sa yanda zamu samu damar yin aikin mu a sauka ke fatan dai likitan da zaiyi aikin ya zama ready... "Wnn duk ba matsala bane ranki ya dade" dariya tayi tana ganin bakin cikin ta yaxo karshe...Ynx hankalin kowa ya kwanta dan Ammar ya farfado kuma har ya samu bacci sae dae har ynx babu wanda yake shiga ganin sa sae kamal shima dan yana likita ne kuma ya fara dawowa cikin hayyacin sa... Har asuba Ammar bai farka ba..
Da asuba su Dada suka saci hanya suka fita... Kyautar mai tsoka tayi wa bokan nata da take kira da malam dan taji dadin aikin da yy mata ta kara da fadin "malam inaso a kawar da idon kowa daga gare sa harda iyayensa inaso a manta da bashi da wata lpy kowa ya fita harkar shi...
Malam yace "An gama inde wnn ne saedae ba kowane zae fita harkar sa ba".. Tayi "saurin cewa malam Allah yasa banda mahaifan sa dan idan har suka tsaya akan komai nasa aikin mu baxae yiwu ba... malam yace "bnd su suma za'a rufe bakin su akan dan su" ... Ajiyar zuviya gaba dayan su suka sauke godiya tayi masa tare da kara masa wata kyautar suka baro gurin cike da farin cikin da basu taba jin irn sa ba...
kamal ne ya fito daga office din doctor jiki duk a sanyaye ya nufi dakin da Ammar yake anan ya samu khadija sarki da baba Rashid jiri har wani har lokacin Ammar bacci yake dibarsa yake a ya zauna tare da Mika ma sarki result din hannun sa jikin sarki yy sanyi ganin yanayin kamal... Da kyar ya kai duban sa ga takar dar ya dade yana kallon ta kafin ya dago yana kallon Ammar kafin ya kalli kamal.. Kafin yy magana kamal yace "nima abinda na gani kenan wae jijiyoyin jikin sa sunyi sanyi komai nasa a slow yake aiki ynx ba komai zai iya yi da kansa ba saedae a masa kuma har ynx basu san dalilin cutar ba babu abinda ya nuna ka cutar saedae zasu dora sa akan magani.... kallon sa kawae suke kowa da wani irin shock khadija kanta har wani juyawa yake tama kasa kukan saedae ta kalli Ammar ta kalli kamal sarki kasa magana yy dagashi har Baba Rashid sai kawae ya fice.... Baba rashid yabi bayan sa sae ita da kamal ne kawae aka bari a dakin.. Du kar da kanta tayi kuka ma yaki zuwa ta.. Duban ta kamal yy yace "ya kamata duk abinda ya samu Ammar mu dauke sa a matsayin kaddara Allah ne ya daura masa kuma shi zai yaye masa a yanxu ne Ammar zai gane yana da masoya babu wanda yafi bukata a ynx sama da ke saboda ke matarsa ce mahaifiyar sa bata kusa dashi ke xaki zame masa uwa kuma mata snn kawa ina rokonki kar rabu da Ammar dan wnn cuta ta same sa nima inshallahu zan tsaya tsayin daka wajen maganinsa kafin muga abinda abie zai yake dan nasan kila fita za'ayi dashi..snn ku dage wajen yi masa Addua dan ita yafi bukata a ynx... Gyada masa kai tayi tana hawaye....
. wajen 10 yan gidan su khadija suka zo kaf dinsu babu wanda aka bari kuma har lokacin Ammar bai farka ba Khadija da kamal sae Dada suka samu dan tun lokacin da Abie ya tafi har yau bai sake dawowa ba.. Khadija taji dadin ganin su sun dade suna kafin su fara shirin tafiya momy Amina ta jata gefe dan itama taxo... Tace "khadija ki kula da mijin ki kar gujesa dan Allah ya daura masa wata cuta kar ki kaji dashi duk runtsi sae kiga ta dalilin haka kin shiga aljanna ki rike sa Amana" sae a lokacin kuka yaxo ma khadija ta fada jikin momy tanayi kamar ranta zae fita da kyar ta samu ta lallashe ta abba ma da ya Auwal suka karayi mata wata nasihar snn suka tafi dawowa tayi tana share kwalla a ranta tana tunanin dalilin da ya hana sarki dawowa tun dazu....
Dakin ta shiga kamal kuma ya fito zuwa wajen sarki dan yy masa bayani akan maganin da suke son daura Ammar dama already Dada ta fita tun kafin yan gidan su khadija su fito... Toilet ta shiga ta wanke fuskar ta fitowan da zatayi sukayi ido hudu da Ammar shima ya xuba mata kyawawan idanunsa masu haske...
More comments more typing... ✍️
*#VOTE*
*#SHARE*
*#COMMENTS*✨✨✨
*NAFEESA A GUGA*
😍😍😍😍😍😍😍😍
YOU ARE READING
SABODA DUNIYA
RomanceLabarin yana dauke da abubuwan bn mmki.. Labarine akan wadanda duniya ta rufe masu ido sun manta Allah ne mai komai snn yana dauke da salon soyayya mai bn sha'awa.. Zai fadakar kuma ya nishadantar daku