Typing~~~~📱
*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
'''(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)
🌼 *Saboda* *duniya* 🌃
Writing by......
<<<<≤<≤<<<<<<<<<<<<
*Annafie*💗07051376476
Nafeesa A Guga @ wattpad
*bismillahir rahman rahim*
Page 38⏩39
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼Tana isa bakin kofar bedroom dinta yy saurin rikota kawae sae ta fashe masa da kuka .. Rungume ta yy ya fara parting bayan ta tare da daura kansa saman ta yana jin yanda hawayen ta ke falling a chest dinsa runtse idanu yy he knows she's hurt sun dade a haka kafin yaji ta sassauta kuka dagota yy yana kallon ta tayi kasa da kanta tana kokarin kwacewa amma yaki bata damar ya hakan still his eyes on her abinda bai taba ba ita kanta khadijar ta kasa natsuwa duk ta gama tsarguwa cikin swt voice dinsa yace "Hanan" dagowa tayi jikin ta na rawa ta kasa kallon sa sae kuma ta fara kokarin yin kuka.. Kama hannunta yy suka shiga bedroom dinta ya zaunar da ita saman gado shima ya zauna tayi wiping tears din ta yace "is ok" ta gyada masa kai... Shiru yy triying to find something to say because bai wani saba tsayawa bada baki ba.. Can yace "hakan baxae sake faruwa ba she's wrong and i'll correct her" nan ma ta gyada masa kai shiru yy can kuma yace "gobe colleagues dina zasu zo gaishe ki so you have to prepared.." Dan kallon sa tayi sae kuma tayi murmushi tace "Allah ya kaimu" a hankali ya furta Ameen" shiru kowa yy.. Wayar Khadija ce tayi ringing tana kusa shi daukowa yy ya mika mata cwt mummy ke yawo akan screen din wayar kallon sa tayi dan mom din sa ce kasancewar kullum sae sunyi waya kaf lvrn khadija mom ta sani hakan yasa ynx ta zame mata tamkar mahaifiya.. Daga wa tayi da murna suka gaisa da mom din Mom tace ina Aliyun kallon sa tayi sai kuma taji kunya a hankali tace gashinan mom" shikam mmki yake har yaushe sukayi sabo da mom dinsa and he is so happy da yaga yanda ta mayar da ita tamkar mon dinsa . miko masa wayar tayi ya karba suka gaisa da mom din cikin harshe larabci daganan take tambayar sa ya yaushe zasu taho yace "next week inshallah" daganan tayi masu fatan Alkhairi.. Sukayi sallama Amsar wayar tayi snn tace "nide kar ta kara zuwa nan koda tace baxata kara tsokana ta ba" kallo ta yy kafin yace "who" ta turo baki "that kausar or what ever" yace "why" daure fuska tayi tace "I just don't want to see her she should let us pls warn her" maganar taxo bakin ta batare da ta shirya ba dariya ta basa amma ya danne tare da zuba mata manyan idanun sa dauke kai tayi tare da juya masa baya snn ta kwanta.. Mikewa yy ya nufi kofa with his smiling face just trying not to laugh because he always get funny whenever she started her childish wani abun kuma idan tayi kamar babba... Down stairs ya sakko daedae lokacin kamal ya shigo kallo yabi Ammar dashi sae kuma yy dariya yana nuna sa Ammar ya daure fuska kafin ya nemi waje ya zauna inda yake kamal ya nufa shima ya zauna tare da dafa shoulder dinsa har lokacin yana dariya.. Hararan sa Ammar yy kafin ya dauke shiru kamal yy ya bi Ammar da kallo sae kuma ya fara wata dariyar cikin harzuka Ammar yace "kaga malam fita ka ban waje ko Nina fita" yana fadin haka ya fara kokarin tashi da sauri kamal ya riko sa "srry srry haba frnd nine fa" shiru ammar yy yana kallon wani direction din.. Kamal yace "gani nayi ka sakko kana wani smiling abinda bn taba gani ba gaba man tun fa da akayi auren nan gaba daya ka canxa ko ka kara wani fresh ko nemana ma bakayi" "kaine dae kayi wuyar gani" cewar Ammar kamal yace "to xan zo ne nai ta xama bayan ynx kanada iyali" tabe baki Ammar yy snn ya cigaba da danna wayar hannunsa .. Kamal dana yasan ba lallai ya samu amsa ba dan yafi kowa sanin halin abokin nasa.. Tsaki yy tare da fizge wayar dalla mallam sae kae ta wani danna waya ka share mutum am fada maka wae kowa ne irn ka. Ka takura kan ka kaki magana lips Ammar ya lasa ya kishin gida da kujera tare da lumshe idanunsa.. Kamal ya bisa da idanu a ransa yana jinjina halin abokin nasa yace "to ina Amaryar" sama ya nuna ma batare da yace komai ba kafin yace wani abu saegata tana sakkowa hijabi ta har kasa..
Gaisar da kamal tayi tana murmushi ya amsa yana tsokanar ta ta mike ta nufi kitchen "bari na girka maku abu mara nauyi kusa a cikin ku" "aa ki girka mai nauyi kinsan cikin gwauro da yunwa dariya kawae tayi ta shige kitchen..
Faten dankali da wake tayi with fish yaji vegetables sae kamshi yake sae coffee ... Kamal sae santi yake ita kam dariya ya bata. Yace "Wato princess nima aure zan zo nayi gsky duk da dai ban girma ba koda yake abokina ma yy shiyasa gashi nan sae kyau yake ya barmu da bin saura kina ji nide kisan yanda zaki dani madam dan gsky nima aure nake so Ammar kawae abie zamu samu ko nima kace ya samomin.. Kauda kai Ammar yy dan baya so yy dariya a gaban khadija.. Kamal ya tabe baki tare da kurgan coffee "kaidae ka sani baxan iya kunshe magana a cikina ba...
Washe gari juma'a kafin a taso daga sallahr juma'a su khadija sun gama sun gama hada komae na tarar baki da fadila taxo duk ita ta yasa komai ita da wasu hadima daga nan suka kara gyara gidan ko ina ya dau kamshi..
Tare da bakin Ammar... Lokacin khadija na kitchen taji shigowar su kasa fitowa tayi dan baxata iya ratsa su ta wuce ba ko hijab babu a jikin ta tana ji Ammar ya wuce sama ba jimawa ya dawo kitchen din ya shigo yana kallon ta "oh kina nan Amma shine kika bari natafi nemanki ko" kamar xatayi kuka tace "to banda Hijab ba a haka xan fita... Binta yy da kallo ganin yanda kyakkyawar surarta ta bayyana yace "Am coming" ya fice... Da kin yaji ya dauko mata wata Alkyaba mai kyau kamal dae sae binsa yake da kallo yana murmushi.. Da kansa ya sanya mata Alkyabbar shi kansa tayi masa kyau dan saeda ta da asalin kyawunta.. Hannun ta ya kama tayi kasa da kanta suka fita zuwa parlour...
A yanda suka juyo kallo daya zaka masu sae ka kara sunyi bala'in dacewa colleagues nasu suka rinka kashe masu hotuna kamal sae tafi yake cikin farin cikin ganin yanda abokin nasa ya dace da mace.. Duk wnn abun kaseem na zaune a inda yake yana kallon khadija da tayi balain tafiya da imaninsa ..har cikin ransa yana bakin cikin yanda kowa ke taya su murna...
Kowa sae yaba ta yake musamman ma da sukaji girkin ta hakan ya kara rudar da kaseem.... Samuel da yasha manyan kaya kamar ba haushe bayan khadija ta tafi yace "Oga wnn mata nata idan yana da karami ina so indae yy beautiful kamar ta and she can cook delicious lyk this one... Dariya duk sukayi kamal yace "ba karami she's the last born" Samuel yace "pls oga ka rinka duramin wnn delicious a leda kafin nima na samu nawa matan hausawa.... Dariya duk sukayi... Da zasu tafi kowa sae da yabada kyauta ta bn mmki abama khadija...
A parlor suka iske khadija da fadila suna gyara parlorn bayan sun dawo daga rakiyar su .. Kamal yace "oh dama muna da bakuwa shine ta kune a daki dariya kawae sukayi suka idasa gyara wajen ... Da fadila zata koma kamal ne ya mayar da ita....
. 🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
Saturday...
Sama khadija ta wuce ganin har 12 Ammar baiyi breakfast bedroom dinsa ta tura a hankali ta shiga shiru dakin sae kamshi yake babu abinda kk ji sae karar AC.. Bin ko ina tayi da kallo Amma bata gansa ba da mmki ta fito domin kau bata ji fitar sa ba coridor doors din tabi da kallo wata kofa ta nufa wanda take kyauta ta zaton reading room ne a hankali ta tura tashiga tana bin hadadden reading room din da kallo ka pics din yan gidan nan ta ko ina wani katon hoton mom ta kura wa kallo trying to recall something dauke idanun tayi tacigaba da bin ko'ina da kallo can idanun ta ya sauka a kansa ya juya baya gashin kansa na baya yawani kwanta luf luf sae sheki yake a hankali ta juya zata fita taji muryar sa yace "zonan" dakatawa tayi dakatawa tayi tana waro idanu dan batayi tsammanin ya kanta ba and his voice sounds abnormal a hankali tajuya zuwa inda yake tace "gani" wasu book ne a gaban sa da system yana operating still not looking at her yace "me kike nema anan"... Duk ta tsorata da yanayin yanda taji muryar sa hat jikin ta ya fara rawa she's eager to leave tace "I just come to check on you na..naga bakayi breakfast ba".. Shiru yy kafin ya dago ya kalle ta saida ta ja baya ganin yanda fararen idanunsa suka rikida zuwa jaa tayi saurin runtse dan ta tsorata sosae sae kuma ta fashe da kuka dafe kai yy sae kuma ya tashi ya kamo hannunta cikin calm voice dinsa yace "srry kuka me kk" tace "me same ka" kasa yyy da kansa sae kuma yace "do not worried kai na ne kawae ke ciwo" shiru tayi tare da duban sa he look sick da sauri tace "pls kayi break sai kasha magani" gyada mata kai yy snn ya kama hannun ta suka fita zuwa bedroom dinsa ita kuma ta sakko ta hada masa tea ta debar masa arish... Duk son sa da tea sai taga kadan yasha tace "ka kara" girgiza mata kai yy dan wani irn zafi yake ji a cikin cikinsa zuwa makoshin sa shi abu mai sanyi ma yake sha'awar sha sae dae yasan is not good to his health cikin karfi hali ya tashi ya dauko drugs ta dauko masa bottle water yasha ya kwanta saman Royal bed dinsa.. Ya rufa da blanket dan wani irin zazzabi yake ji yace "ki kashan AC din" tashi tayi ta kashe masa tace "ko a kira kamal ne girgixa mata kai yy "no xanyi bacci" shiru tayi tana kallon sa tanaji har bacci ya dauke sa tanajin yanda yake struggling da numfashin sa. Hawaye ne ya zubo idon ta ta tashi ta fita ta kara gyara dining din snn ta shiga domin daura masa abinci mafi sauki.. Lokaci lokaci takan dan leko sa takaga yana bacci har ta gama ta taho zata kawo masa tana budewa taji kakarin aman sa a toilet da sauri ta aje ta nufi toilet. Kamar zae amayar da yan hanjin cikin sa gashi sae rawar sanyi yake ya rude ta kama sa jikinsa ya day zafi sosae ya wanke bakinsa snn ya fice cikin karfin hali gyara toilet din tayi snn ta fito zaune ta gansa saman sofa ya jiginar da kansa yana sauke numfashi kamar zatayi kuka tace "sannu" ya gyada mata kai kafin yace "bani abu mai sanyi cikina zafi" girgiza masa kai tayi "no baka da lafiya fa bari dae ba hada maka ruwan wanka" daga haka ta shiga toilet din.. Da kyar da samu ya rage kayan jikin sa sanye ta iske sa bathrope sae rawar sanyi yake bayan ta hada masa ruwa mai xafi cikin dakiya ya mike ya shiga toilet din ta bisa da kallo hawaye na fita a idon ta closet dinsa taje ta dauko masa wasu kaya masu dan kauri ta aje Masa tareda feshe su da turare.. Wayar sa ta dauko luckyly ta samu ba security ta sunan da taga anyi saving da tight frnd ta kira bugu biyu kamal ya dauka har xai fara tsokanar sa yaji khadija ce yace "madam ince dae lpy" tace "ka ganshi nan bashi da lpy ko break beyi ba" ta kare maganar wiping her tear yace "gani nan xuwa" aje wayar tayi tare da fashews da kuka... Turo kofar akayi Kamal ya shigo daedae lokacin da Ammar ya fito tashi tayi ta fice a dakin baya ta nunawa kamal abincin sa ta nufi dakin ta tana kuka.. Tana jin yanda gaba daya masarautar ta rude ana murna dan yau maimartaba zae dawo daga misra gashi kamal yace karta fadawa kowa....
Da kyar kamal ya tilasta masa yasa wani abu acikin sa snn ya saka masa karin ruwa koda khadija ta dawo har yy bacci kamal yace bari yaje kar ta fadawa kowa don baya son hayaniya ta gyda masa tana binsa da kallo......
Hudu da rabi Ammar ya farka ba laifi ya dan samu sauki sae dae jikin sa duk ba kwari dauriya ce kawae irn tasa. Ya rama duk sallonsa kadan yaci cikin abincin khadija ta kawo masa khadija ta jinjina masa sosae kallo daya zakayi masa kasan yana jin jiki dan har ya wani zabje....
Suna zaune a parlor su duka ukun magrib kowa yy shiru dawowar mai martaba kawae suke jira Ammar shi kadae yasan yanda yake ji a cikin jikin sa shi kansa yadan daurewa kawae yake har ya kosa Abbie dinsa ya dawo ko ya ji dumin mahaifin nasa suna cikin haka sukaji shigowar tawagar motocin sa khadija ta mike ta nufi sama sukuma suka mike zasu fita... Har ta kai tsakkiyar stairs taji faduwar mutum.. Cak... Ta tsaya jikin ta na rawa tama kasa juyawa a kyar ta aro courage tajuya dae dae lokacin da Kamal yace "Ammarrrrrr" kasa motsi tayi ganin yanda kamal ke jijjigasa kamar gawa.... Wani irn kuka khadija ta saki ta ruga kan Ammar tana bubbugasa "yareemaaaa" amma ina baya ko numfashi....
More comments more typing... ✍️
*#VOTE*
*#SHARE*
*#COMMENTS*✨✨✨
*NAFEESA A GUGA*
😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍
YOU ARE READING
SABODA DUNIYA
RomanceLabarin yana dauke da abubuwan bn mmki.. Labarine akan wadanda duniya ta rufe masu ido sun manta Allah ne mai komai snn yana dauke da salon soyayya mai bn sha'awa.. Zai fadakar kuma ya nishadantar daku