Typing~~~~📱
*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
'''(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)
🌼 *Saboda* *duniya* 🌃
Writing by......
<<<<≤<≤<<<<<<<<<<<<
*Annafie*💗07051376476
Nafeesa A Guga @ wattpad
*bismillahir rahman rahim*
Page 7️⃣ - 8️⃣
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼Yau ya Auwal da kansa ya dauko su khadija, farida da aneesa makaranta., sae driver ya dauko sauran.... Kar sha biyu suna cikin gidan...
Khadija na xuwa daki tayi wanka ta shirya.
Ya Auwal na dawowa daga masallcin juma'a ya dauke su ita da farida xuwa gidan hajjo sauran kau ba son zuwa suke ba dan bawani shiri suke da hajjo ba....
Motar su na gama parking... A hatabar gidan hajjo yays sadiq ya danno hancin motar sa....
Ai da gudu su khadija suka fita husna ma na ganin su ta fito ta rungume su cikin murna yayinda ya Auwal da yaya sadiq sukaje suma suna gaisawa.. Momy (Amina) tafito tana fadin ni babu mai tani ko ta yan uwan ku kuke ko...
Ai da sauri suka saki husna sukayi kanta suka rungume... Daga nan suka rungume yaya sadiq ...
Hajjo tayi farin cikin ganin su sae murna take yi....
Mujaheed da faruq ne suka shigo... Cikin murna faruq yace "wow yau gidan muna da manyan baki knn" "da sauri khadija tace "kaide bari gamu nan munsha hanya". Hararan ta yy kafin ya dungure mata kai "see you dake nake ne nida momy da ya sadiq nake amma ku bnd ku" Khadija ta marairaice fuska tare da dafe goshi "hajjo kingan sa ko zae saka min ciwon kai" Hajjo tace "kai fita ido na saeka saka mata ciwon kai ko wae faruk baxaka bar takurawa hadiza ba ko" khadija ta hade fuska "kai hajjo ni kibar cemun hadiza wnn ai saeku amma ni khadija nake" Hajjo ta mata dakkuwa "ungo nan naga suna na aka saka maki kuma haka na iya yau ga ja'ira" khadija ta tura baki tana kukunai momy ce da tashigo parlorn tace "maike faruwa ne" "faruk yace "gara kiyi shiru kinsan ba'a shiga tsakanin hadiza babba da hadiza karama"khadija ta harare sa yayinda momy tace gidan ku faruk kyalesa kinji diyata" dariya faruk yayi kafin yace " wae gayu madam babu wani khadija hadiza dae" kukan shagwaba ta fara... Yaya sadiq ne dake kusa da ita ya fara lallashinta "srry kinji zanyi maganin sa" dariya kowa yake mata a wajen.... Husna tace "hadiza nayi mssn dinki" ya sadiq ya bige mata baki.. Momy ce tace to ya isa ku tashi muci abinci....
bayan isha'i suka shirya domin xuwa sha ice cream suka shiga mota babba wacce xata ishe su iya su yaran yaya auwal ya sadiq faruk khadija, farida sae husna ya mujaheed ne kawae babu dan shi cewa yayi baxae xo ba. Khadija ta tabe baki kafin tace "ke wlh farida wnn saurayin naki wani lokacin halinsa sai shi wani lokacin saukin kai wani lokacin jin kai" "farida tace ina ruwanki" yaje yayi ai gwarashi ke da kullum sbd ke sai an tsaida mu a titi fa.... Khadija ta tabe baki keni rabani da wadan nan mutanen....
Bayan sun dawo basu wani dade ba ya Auwal ya kwashi iyalansa da suka zo sae husna xuwa gidan Abba.... Sanda sunka shiga main parlor dukkan ilahirin gidan na nan umma(abida) da mama(jamila) kowa sae bin yaransa da harara kasa kasa yake khadija na lura da su amma ta nuna kamar bata gansu ba ta nufi Abba ta fada jikinsa "Abba na munda wo" husna ma ta gaisar dashi ya shafi kanta kafin yace ya hanya lpy qlw tace "alhmdllh Abba mun same ku lpy" lpy qlw ya mominki" " tana gaishe ka Abba" "ok kici abinci ni bari naje na kwanta don nagaji" kowa yayi masa saida safe.... Suka zauna a parlorn husna ta gaisar da su umma da mama dakyar suka amsa mata
Mama ce tace ke husna baki gaishe da yayunki kamar ba yan uwanki ba gaba daya kin mai diyar nan ita kadae ce yar uwar ki wacce ko asali bata dashi.... Husna najin ta ta nuna kamar ma bata jin ta mufeeda ce tace "mu awa daxata dauke mu yan uwan ta tunda an jika an bata........ " "keee zan tattaka ki anan tasjiki bar wajen nan banxa fitsararra" "babu inda xata wato kafifita bare akan yaruwarka ko"umma tafada cikin masifa.... Ahankali yace "umma khadijar ce bare ynx yakike tunanin Abba xaiji idan yaji abinda kk fada akan diyar sa.... " "dallah can rufemun baki wanda baya son abinda uwar sa keso idan ba bare bace to mece ce... Ga hauka ga rashin asal... "Ai baikasa jin abinda take fada ba ya fice daga parlorn.. Farida ma ficewa tayi... Yayin da sauran suka raka su da harara salima ce tace "nu har bnsan kalar yaya da farida da ba agidan nan da asalin su da komai amma.... " "dan uwarki a rubata maki asalin a goshi" husna tafada cikin harxuka... Mama tace "ai fa mara kunya taxo a gaba na kike zagina.... " husna ta tabe baki kafin taja hannun khadija su wuce daki...
Mufeeda taja tsaki "wann karon fa baxan dauki iskancin yarinyar nan ba baxae yu taxo gidan ubanu tana mana abinda taga dama ba ehe... "
Washe gari sunday su khadija basu da lectures dan haka yau sukasha baccin su basu tashi ba sae 11.. Lokacin harsu abba, mama, umma, da ya auwal sun tafi gidan hajjo domin tarbar baki aka saka ranar auren Raliya da saddiqa" domin shi Abba babu ruwansa akan sae mace tayi karatu sann tayi aure a duk lokacin data samu miji xae aurar da ita taci gaba acan.. Ita hajjo ai har su khadija cewa take sufito da maxajen aure....
Saida sukayi wanka snn suka fito saddiqa, mufeeda da Aneesa farida kam har tayi break ta koma bacci dan mama bata fita ba saida ta hada mata break dan tana mugun ji da autar ta ta...
Suka je dining din husna tace "ina break din" saddiqa tace wa kuka aje ya muku... Khadija tace "kinga husna muje kitchen naga dae muna da hannu" suna fadin haka suka nufi kitchen suka dafa indomie suka ci kayan....
da yamma suka shirya su uku xuwa gidan su fadila sunyi kyau abinsu idan kagansu sai ka kara kallon su gashi har wani kama suke ...
Fadila harda tsallen murnar ganin husna " suka rungume juna fadila tace "shine tun jiya baku xo ba ko" "ai da kinxo kin dauke me" cewar khadija...
Sun dade a gidan ganin hadari ya taso yasa suka fara shirin tafiya babu yanda fadila bata yi ba akan su bari driver dinsu ya dawo ya maidasu amma suka ka ki wae basa so ruwa ya same su a nan.. Har bakin titi ta rako su suna neman abin hawa amma basu samu ba duk sun gaji da jira dan unguwar su fadila ana wahalar abin hawa... Ga hadari ya taso.. Motoci sae tsayawa suke su masu lift amma sunki hawaw... Fadila tace dan Allah kuxo mu koma kar ruwan nan ya same mu a nan .. Khadija ta harareta.. Kafin ta dauke sunan har aka fara yayyafi khadija kamar zatayi kuka wata motace har ta gibtasu ta dawo.. Farida ce tace to gade wani nan salan kuma kuce baxaku shiga ba fadila tace "wlh frnd Kikace baxaki shigaba saedae kuxo mu koma kokuma nayi tafiya ta...
Daidae su yy parking tare da zuge glass din black beuty ne... Dan murmushi yy kafin yace "ya kuke tsaye a nan mata daku ga ruwa kushigo na rage maku hanya.. "Aa mun gode kabar... Da sauri husna ta rufe bakin khadija snn tace "aikam da mun gode" murshi yayi kafin ya kalli khadija da ta wani hade rai tana hararan Husna "to kushigo kar ruwa ya sakko" farida ta bude gaba tashige ganin khadija na niyar bata masu lokaci husna ma shiga tayi yayin da fadila ta juya tana dagawa khadija hannu kinga frnd na wuce
Khadija ji take kamar ta nutse ga matashin ya tsare ta da ido babu yanda ta iya dole ta bude inda husna take ta shiga... Husna tace da kar ki shigo... Ya fada motar bayan farida ta fada masu unguwar... A hankali yake dan jansu da fira husna da farida ne kawae suke kulasa amma bnd khadija ya dan juyo yana kallon ta snn yace madam kinyi shiru kona maki laifi ne.. Murguda masa baki tayi kafin ta dauke kai yy murmushi snn yacema farida "wnn yar uwar taki dae akwai fitina" farida tace kadan kagani" khadija najin su batace komai ba... Suna iso wa gidan khadija tabude xata fita yayi saurin dakatar da ita haba madam yaxaki fice babu ko sallama ga ruwa ana tayi ai kin bari ya dan tsagaita... "To nagode sai anjima" tafada tana kokarin fita yace "to bani numbern ki mana" tace "bnd waya" da sauri Husna tace "bari xan baka" hararanta khadija tayi kafin ta bude ta fita ta ruga sbd ruwan...
Godiya suka masa bayan ya karbi numbern khadija suka fice suka ruga cikin gida...A parlor suka iske su yaya Auwal dasu su ya sadiq dasu ya mujaheed da faruk.. Su umma kam har ynx basu dawo ba
Khadija nashigo ya Auwal ya mike daga ina kuke haka ana ta kiran numbernku ba kwa picking ina sauran suke ... Ya jero mata tambayoyin.. Su farida ne suka shigo ya sadiq ya watsa masu harara daga ina kuke haka.. Lahh yaya daga gidan su fadila muke fa" farida ta fada "kin ci gidan ku da fadilar shine kuka tsaya har ruwa ya sakko kuma ana kiran ku ba kwa picking" cewar ya sadiq .. Shiru sukayi sae fada suke masu yaya sadiq da ya Auwal sae faruk dake xugi. Mujaheed dae baice kala ba.. Saeda sukayi fadan mai isarsu snn suka korasu daki dakin khadija suka tafi suna dan dariya .. Husna tace masifaffu kawae shiyasa yaya mujaheed yaje birgeni babu ruwansa da wnn fada .. Khadija ta kwalalo idanu waya fada maki ai gara kowa da shi nasan nan da ajima zai kira farida shi komai akanta yake saukewa...a haka ake Soyayyar husna tace tab... Ai kam kamar jira yake sae ga wayar farida ta fara kara suna dubawa suka shine duk ta wani damu khadija ta tabe baki wlh da nice baxan yarda da ba ai naga kokarin ku ji fa yanda yaya Auwal ya gama zazzage mu kuma wae anjima ko kunya baiji zai kira ki" husna tace "to ina ruwanki" khadija ta tabe baki ... Kafin ta shige toilet farida kam nacan gefe tana waya da ya mujaheed sai questioning dinta yake"....Kusan karfe goma kira yashigo wayar khadija ita harma ta fara bacci... Ganin number ce taki daga wa taci gaba da baccin ta har ta tsinke... Aka sake kira anan ma taki dauka haushi ya ishi husna da take waya da ya Auwal.. Ta tashe ta tare da ga wayar da saka mata a kunne "babu de kyau wulakanci ci kika son wake kiranki...
Tsaki khadija tayi kafin tayi sallama... Daga can bangaren aka amsa shiru ne ya biyo baya kafin can yace "natashe ki ko" "uhm" shine abinda tafada "ok srry kawae dama nakira ne naji muryar ki hope kin gane mai magana "aa" tafada a takaice" yace "am sunana usman nine wanda sis dinki taba ma numbern ki bayan kince cemun baki da waya" sae ynx khadija gane ko wane shiru tayi batace komai ba can yace "ynx ki kwanta kiyi bacci xamuyi magana gobe inshallah"...
Bayan ya kashe ta juyo tana hararan husna da itama take kallon ta...
Husna tace "madam lpy " lpyr ce ta kawo haka wato shine kika bada number ta ko maimakon kibasa wrong" husna tayi dariya "akan me xan basa wrong common Allah gayen ya hadu kawae ki amince masa" tsaki khadija tayi kafin ta juya tana fadin aisaiki min dole... Dariya husna tayi tana fadin "madam ai nama riga ja basa hajjo kawae zan samu da maganar nasan xata yi farin ciki...Washe gari su husna suka koma sbd makaranta haka khadija taci gaba da rayuwa a cikin gidan da dadi babu dadi maganganun da suke jifar ta dashi ne mata ciwo da mahaifiyar ta dasuke muxantawa sae kace tana duniya wani lokacin idan abin ya isheta sai ta tafi gidan hajjo dan tafi jin dadi can ga faruk ma susha barkwancin su dan sunfi sabawa akan mujaheed sbd Abban tane yasa take zama gida.... Sai kuma idan sunyi fada da hajjo...
Ynx kam soyayya suke da usman dan duk cikin samarin ta suke binta shi kadae ya kwanta mata kuma yana da saukin kai da barkwanci.... Suna yin hutun second semister dinsu akayi bikin Saddiqa da Raliya.... Yayin da aka saka ranar mufeeda snn salima da ya sadiq ... Ynx kam soyayyar usman da khadija sae abinda yayi gaba dan harma ya fara magana akan zae turo iyayen sa sbd asan da zaman sa ita ce ma ke dan dakatar dashi dan bata so tayi aure ynx kuma tasan hajjo da yaxo zata ce ya turo kawae.. Shikam baya so ya rasa ta har suka shiga 200 level.. Alokacin akayi bikin mufeeda da salima da yaya sadiq...
Ynx kullum sae hajjo tace mata itama ta fito da shi ita da Aneesa dan ynx kam tasan da soyayyar Ya mujaheed da ta farida sai yaya Auwal da husna... Shikam abba baya son suyi aure ynx amma babu yanda ya iya dan idan yace wa hajjo basu isa ba taxace su tun suna shekara sha biyu aka masu aure bare yan shekara 18 takwas sha tara... A haka dae har suka shiga level 3 ynx kam har an fara maganar auren fadila da husna yaya Auwal da yaya mujaheed...
Wata rana Abba yana kan hanyar sa ta dawo ya banke wani mutum... Hankalin tashe Abba ya fito mutane suka taimaka masa yasakashi a mota suka nufi asibiti... emergency aka tafi dashi... Hankali tashe ya kira Auwal ya sanar masa akan yasame sa a asibiti tare dayi masa kwatanceen asibitin....More comment more typing.... ✍️
*#vote*
*#share*
*#comment*✨✨✨
*Nafeesa A Guga*
YOU ARE READING
SABODA DUNIYA
RomanceLabarin yana dauke da abubuwan bn mmki.. Labarine akan wadanda duniya ta rufe masu ido sun manta Allah ne mai komai snn yana dauke da salon soyayya mai bn sha'awa.. Zai fadakar kuma ya nishadantar daku