Thirty one

53 4 0
                                    

Typing~~~~📱

*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*

'''(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)

   🌼 *Saboda* *duniya* 🌃

Writing by......
<<<<≤<≤<<<<<<<<<<<<
*Annafie*💗

07051376476

Nafeesa A Guga @ wattpad

*bismillahir rahman  rahim*
Page 60 ⏩ 61

  🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
Tunda suka shigo unguwar Khadija take binda da kallo ko ina security light ne kuma da kaga unguwar kasan ta manyan mutane wadan da kudi ya ratsasu....
A bakin fitinennan gida mai taxi din ya tsaya wanda khadija kallo daya tayiwa gate din tasan za'a sha kallo   hannun ta taji Ammar ya kama ta juyo ta kallesa  yace "u're welcome to Egypt" lumshe idanu kawae tayi tanajin ranta yana mata wani sanyi without reason.. 
  Hannun sa daya yana rike da trolley dinsu dayan kuma yana rike da hannun sa  suka nufi gate... Trolley din ya aje ya fara knocking.. Kamar jira ake sai gashi an bude gate wani security ne kakkarfa ya bude.. Idanun sa na sauka akan yayi saurin Zubewa a kasa yana kwasar gaisuwa Ammar baice dashi komai baikuma amsa gaisuwar ba ya ja Hannun khadija suka shiga cikin gidan.. Tsayawa fadar yanda kyan yake bata lokaci ne  ga securities ta ko ina dan suna shigowa kowa hankalinsa yayi kansu suna ganin Ammar zasu zube suna kwasar gaisuwa  Shikam Ammar ko kallon su bayayi bare su sa ran zai amsa wasu suka zo suna take bayansu khadija duk saitaji wani daban ganin katti majiya karfi suke ta Zubewa wasu kuma na take bayansu duk da a cikin masarautar su ta Nigeria ma hakane  Amma wnn yasha banban  ta dubi Ammar taga shikam ko a jikinsa sai ma wani hade fuska da ya karayi ya fito kamar a asalin prince din da ta sansa.. Mota ce taga ta paker daga gefen su.. Batare da wani bata lokaci ba Ammar ya bude mata ta shiga shikuma ya zagaya aka bude ya shiga aka fara tafiya dasu Ammar ya jingina da seat tare da lumshe idanun sa har motar ta tsaya bai bude idanun sa Ya dade a haka kafin aka bude masa ya fita itama haka suka fito .. Bin katon gurin khadija tayi da kallo tana jinjina haduwar wajen Ammar ya zagayo ta inda take ta kallesa shima din ita yake kallo tayi kasa da kanta.. Cikin wata irin murya yace "I can't wait to see them mushiga ciki pls" Khadija taji duk tausayin sa ya kamata yayin da itama taji tausayin kanta shekara da shekaru rabonta da umminta amma har yau tana kewar ta kuma gata da yan uwa sae dai su basu kaunar ta.. Aamar taji ya kamo hannun ta ta dago suka kara hada idanu ya gyada mata "let's go" binsa tayi jiki a sanyaye sai da suka hau step hudu snn suka isa bakin kofar  ga mamakin ta sai taga yasa hannun sa wajen tum print kawai sae taga kofar ta bude kallon ta yy "get in"....
   Batare da tayi masa musu ba ta shiga kanta a kasa... Dukkan nin suna cikin babban parlorn mai cike da kayan alatu.. Waleed,  sameera, Rahma sai mummy jin an bude kofa yasa hankalinsu gaba daya yy gurin dan sun san idan aka cire su da suke nan daga Abie sae Ammar ne zasu iya bude kofar nan batare da knocking...
  Idonsu ne ya sauka a kan khadija dukkanin su da wani irin shock suke kallon ta .. Tayi kasa da kanta gabanta na faduwa aranta tace "yanxu kila haushi na suke ji na gudar masu da.. Bata karasa tunanin da take ba sae kawae gani tayi Rahma da sameera sun rugo sun sun rungume ta .. Yayin da waleed yake ta kallon kofa ko zaiga dan uwan nasa  Amma shiru ya juyo ga khadija suka hada idanu  cikin saarkakkiyar murya yace "where is... " kafin ya karasa idanun sa ya sauka akan Ammar da ya shigo ynx.. Yana ganin ya ruga ya rungume sa hakan ya janyo hankalin su Rahma   aikam suna ganin suka saki khadija sukayi kansa suka rungume sa tare da fashewa da kuka.. Khadija ta bisu da kallo gwanin ba sha'awa yanda suke nunawa juna su kauna yana burgeta yanda kasan gabadaya ciki daya suka fito... Ji tayi kamar ana kallon ta hakan yasa ta juyo idanun ta ya sauka a kan kyakkyawar fuskar mummy da ta mike tun shigowar su ta zuba masu idanu.. Gaban khadija ya fadi da ta tunawa wayar su ta karshe da ita yanda ta nuna I don't care da dan nata duk da yanda yake cike da bukatar ta... Ga mamakin ta sae taga idon mummy cike da kwalla . Khadija tayi kasa da kanta... "Khadija" taji murya mummy ta kirata cikin sanyi.. Dagowa khadija tayi sae dae takasa kallon mummy din a hankali tace "come to me dear" khadija ta kalleta mummy ta gyada mata kai.. A hankali khadija ta karasa inda mummy take. Tuni mummy ta rungume ta idanun ta na fitar da hawaye  yayin da khadija ta sauke ajiyar zuciya tana jin wani ta dadi a kasa zuciyar ta kuma tunanin ta ta mahaifiyar kawae take tana jin inama ace bata mutu ta barta ba...
  Ammar ya raba yan uwansa da jikin sa idanun sa na kan su mummy yana jin wani irin kewar ta rabun sa da ita tunda ya tabi Germany kusan wata nawa kenn saidai yana tsoro yanajin tsoro saboda yanda aka shiga tsakanin su.. Saman wata kujera yaje ya ya zauna yayi kasa da kansa  idanun sa sun kada sunyi sunyi jajir.. Da kallon tausayi suka bisa dashi dan su kansu sun rasa rasa dalilin da yasa mummy bata nuna wani damuwa akansa ba .. Tunda waleed ya dawo ya. Sanar masu abinda ke faruwa suka tashi hankalin su Amma mummy sae ta share ko da yaushe cikin yi mata maganar suke amma sae tayi bnxa dasu idan ma sun dame ta zata tashi ta basu waje sun shiga tashin hankali sosae ko abin kirki basa ci su sameera kullum kuka waleed ne mai dan dauriya...
   Mummy ta dago tana kallon Ammar har lokacin bata saki khadija ba ta dade tana kallon sa wani irin tausayinsa takeji ji take kamar taje ta rungume sa amma tana tsoro she don't  know what goes over her ta share dan ta ko maganar sa bata so ayi mata amma ynx tana ganin sa sosae a ranta but she know he is hurt and very angry with her  ta gujesa a lokacin da yake bukatar taimakonta lokacin da bashi da wanda yake bukata sama da ita sai kuma ynx da ya samu lafiyar sa snn tace zata nuna masa tasan he take it impossible ta runtse idanun ta tana jin zafi a ranta  ta kara bude idanun ta a kansa har lokacin kansa a kasa yake tasan zabi yake ji sosae a ransa .. A hankali tace "Ammar my son"  runtse idanu Ammar yy batare da ya dago ba.. Hankali mummy ya kara tashi da sauri tace "pls come to me" still bai taso ba  kuma bai tago ba.. Ta kara kankame khadija hawaye  na fita a idon ta tace "bana fatan ranar da zata zo ace na rabu da kai I don't know what goes over me akan duk abinda ya faru I know you must blame me maybe you're wondering ko nice ko bani bace.. Yes I am.. That your swthrt and i still the one you knw pls my son come to me plsss." taja pls din da cikin wata muryar kuka tana dora kanta saman kafadar khadija.. Tace "khadija nasan fushi yake dani ko kila ma yace baxai kara zuwa wajena ba ko kece kika matsa masa ko kokuma wajen yan uwansa yaxo domin nasan da wuya uwa tayi ma danta iri abinda nayi masa ba ya sake waiwayar ta..kaico na ni farha diyar Abdullah me yasame ni ne....
Runtse idanu Ammar yy yana jin wani zafi bakaramin taba ransa maganganun Mummy suke ba yasan ba laifin ta bane kuma bai taba rike ta ba snn kuma bakaramin dadi yaji ba jin yasame ta kamar mummy da yasani a baya.. Ya dago yaga yanda ta rungume khadija kamar zata shige jikin ta dakin yy shiru kowa hawaye yake.. A hankali ya tashi zuwa inda suke  da sauri yaje ya rungume su gaba dayan su yana runtse idanun sa idanun sa da suka koma kalar ja.. Cikin sarkakkiyar murya yace "I miss you swthrt"  wani murmushi da mummy bata shirya ba tayi tana jin wani dadi gsky tayi kuskure da tayi tunanin zai iya rike ta dubada irin kaunar da yake mata  ta lumshe idanu tana jin kaunar dan nata da wani irin farin cikin ganinsa kusan wata nawa rabon ta dashi..
  Ganin haka yasa su Rahma ma suka xo suka rungume su suna farin ciki.. Sun dade a haka kafin mummy tace "kai ku sake mu haka mana sai kun karya mu" dariya sukayi su duka suna sakin su mummy ta kama hannun Ammar da khadija tana hararan su sameera "ko gajiya basu sauke ba kun wani bi kun makalkale su" dariya sukayi gaba dayan su kowa na samun guri ya zauna.. Mummy tace "zama nace kuyi" suka mike da sauri ..
Mommy ta dubi sameera "ku tafi da Hanan tayi wanka" sameera ta kama hannun ta suka nufi dakin ta .. Ammar ya bisu da kallo har suka haye stairs .. Mummy take tabada abinda za'a dafa aka wuce da kayan su can dakin Ammar..
   Khadija ta dade tana wankan snn ta fito wankan har lokacin sameera na dakin  mirror khadija ta nufa ta yi shafa sameera ta dauko mata wata riga mai kyau mara nauyi ta saka tare da fadawa saman gadon Sameera tana sauke ajiyar  zuciya.. Dariya Sameera tayi "kun sha hanya fa" "kedae bari ai ba'a magana" cewar khadija mikewa sameera tayi kinga tashi muje kafin mummy ta saka a biyo mu"  Khadija ta mike suka fice..
Har lokacin su mummy suna nan parlor suna Ammar  ya daura kansa saman cinyar mummy ya wani lumshe idanu waleed kuma nadaga can zaune kujerar gefen su da alama lvr suke yi... Rahma kau tana can suna shirya dinner ita cook.... Mummy ta nunawa khadija  gefen ta "zo ki zauna nan mamana" a kunyace khadija tayi yanda mummy tace... Ammar kau har lokacin bai dako ba bai kuma bude idanu ba.. Mummy tace "kai tashi ka tafi kai wanka" Ammar ya bude lumsassun idanun sa.. Batare da yace komai ba kuma bai kalli kowa ba ya mike ya nufi stairs  part dinsa ya shiga.  Parlar ne mai dauke da dakuna  tsayawa fadin kyan gurin bata lokaci ne sae kamshi dake tashi ta ko ina an gyara sa tsab. Wani dadi yaji wato dae duk da abinda akayi wa mummy tana jin sa a kasan ranta kenn tunda hakan baisa ta dena sakawa a gyara masa dakin sa ba... Bedroom dinsa ya shige nan ma gyarare yake  fess ya fara rage shigar sa zuwa ta wanka snn ya shige toilet din....
  Har aka gama jera komai a dining Ammar bai sakko ba gaba dayan su suka nufi dining hannun khadija cikin na mummy har sukaje dining din suka zauna tana gefen ta. .. Mummy tayi serving dinta duk abinda aka dafa saeda ta zuba mata "ki cinye duka kinji"... Kan Khadija akasa duk sai taji kunyar mummy take ji bacin a waya sakin jiki take da ita .. Mummy ta dago tana kallon su sameera tace "kar wanda ya saka mata idanu ku barta taci abincin ta kar ki kula kowa kinji mamana" waleed yace "mu kuma akan me zata ji kunyar mu muda ba yau ta fara ganin mu ba kuma mu kannen ta ne ba surukarta ba" "yauwa yaya Waleed nima abinda na gani knn" cewae Rahama  mummy ta hararesu tace "na de fada muku ku kanne ne ni kuma uwa ce sae muga wanda za'a fi jin kunya a ciki" dariya sukayi gaba daya  snn suka fara cin abincin khadija ma ta saki jikin ta... Kamshin turaren sa ne yasa duk suka dago suna kallon sa  yana sakkowa daga step din.. Khadija ta bisa da kallo bakaramin kyau yy ba cikin light blue kayansa masu taushi.. Hada idanu sukayi ya kashe mata ido  tayi saurin yin kasa da kanta.. Ya karasi wajen tare da kissing din mummy snn ya zauna gefen ta shima tayi serving din sa ya fara ci yana kallon Khadija da ta fara wasa da spoon...
    Pls kuyi manage da wnn kwanan nan idona yana bani matsala amma da babu gwara ba dadi.. 
... More comments more typing... ✍️
*#VOTE*
*#SHARE*
*#COMMENTS*

✨✨✨
*NAFEESA A GUGA*
😍😍😍😍😍😍😍😍

SABODA DUNIYA Where stories live. Discover now