Typing~~~~📱
*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
'''(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)
🌼 *Saboda* *duniya* 🌃
Writing by......
<<<<≤<≤<<<<<<<<<<<<
*Annafie*💗07051376476
Nafeesa A Guga @ wattpad
*bismillahir rahman rahim*
Page 28⏩29
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼Tunda Ammar tafita Khadija ta aje abincin ta janyo bargo zata rufa Aunty fati tace "oh saboda ya fita ko to da kin kwanta zan kira sa" kamar zatayi kuka tace "aunty bafa bacci zanyi ba" "eh duk da haka ynx nan da kin kwanta zazzabi zae sake rufe ki" sameera ta saka mata pillows a bayan ta "aunty Hanan ki dan jigina basae kin kwanta ba zaki samu karfin jikin ki"...
Jin gina tayi tana ya mutsa fuska ji take kamar ta fashe da kuka... Tanajin su suna ta fira akan tafiyar tasu anan ne ma take jin jin wae maimartaba na misra.. Suma duka gobe zasu koma aunty fati acan take aure sameera da Rahma kuma acan suke karatu walid ma tare zasu tafi daga can zae wuce cairo dan acan yake masters dinsa.... Dan kallon su khadija tayi "wae kuna nufin duk tafiya zakuyi ku barni" dariya Walid yy "ke kadae kuma keda gaki ga oga" hararan sa tayi tana murguda masa baki can tace "nide zan biku idan ba haka ba nima na tafi gidan mu" waro idanu sameera tayi "ina zamuje da ke bayan ga ya Ammar" "Aunty fati tace "kwantar da hankalin ki kuma kuna nan xuwa kinga bai dade da dawo wa ba ga Abbie baya nan so kinga yakamata ya tsaya ko... " "amma xanyi kewar ku" cewar khadija dariya suka rinka yi mata aunty fati ce ke bata hakuri.. Haka suka rinka janta da fira da barkwanci har ta manta tana wani zazzabi.. Ranar kaf anan suka wuni Ammar kau tunda ya fita bai dawo ba.. Hakan Yamata dadi ynx dan rabon ta dasu tun ranar da Ammar ya dawo.. Ynx kam masha Allah kafar ce kadae ke mata ciwo...
Har su aunty fati suka tafi bai dawo ba suna tafiya itama ta wuce daki tana din gisa kafar ta tayi wanka snn ta kwanta.. Bata jima da kwanciya ba Ammar ya turo kofar dakin ganin ta kwance yasa ya ya karaso dakin zubama kyakkyawar fuskar ta manyan idanun sa ya hankali ya kai hannu goshin ta yaji babu zazzabin... Bude idanunta tayi tana kallon sa shi kuma ya dauke kai kamar ammasa dole yace "how you feeling" ta dan lumshe idanu a hankali "Alhmdllh" batare da ya kara cewa komai ba ya nufi hanyar fita tace "yaya gobe xamu je gidan".. Tsayawa yy na wasu yan seconds can kuma ya fice batare da yace komae ba.. ta bisa da kallo kamar wata doluwa. Can kuma ta murguda baki ta juya taciga da baccin ta...
Koda ta tashi da asuba ta samu sauki sae dae bata jin dadin jikin nata snn har ynx kafar da sauran ta... Yau ko tea din safe aunty fati ta aiko masa dashi babu aekin da tayi yau dakin ta kadae ta gyara... Ta kwanta wajen 9 ta tashi da hanzari ta shiga wanka ta fito ta fara shiri cikin marron less ya amshe ta sosae batayi wata wata kwalliya ba farar powder kawae ta shafa sae lipstick sae ta gyara girar ta hakan ya fito da tsantsar natural beuty din nata.. Mayafi ta dauka ta nufi parlor tayi breakfast snn ta dawo sama a corridor ta hadu dashi ya shirya cikin shiga ta alfarma kayan sunyi matukar yi masa kyau ita kanta saeda ta yaba da tsantsar kyawun sa a zuciyar ta.. Amma a fili sae cewa tayi "good morning" yace "same" a hankali tace dani za'a je "girgiza mata kai yy.. Ta langwabar da kai "why?.. Naji sauki fa" bai ce mata komai ba saeda ya gama saka wrist watch dinda ke hannun sa snn ya dago yace "you are going no were because you're still limping your leg" hawaye ta fara yi "dan Allah muje zanfa iya tafiya. Juyawa yy ya shige dakin sa.. Ta fashe da kuka ji take kamar tayi tsuntsuwa ta ganta tare da Abban ta. Tans ciki haka ya fito.. Zuba mata idanu yy baya son ya bata ma wani rae ko wani yy kuka ta sanadiyar sa.. Gashi yama kasa ce mata komai... Jin ya fito kuma bataji ya wuce ba ta dago tana duban sa .. Hakan yasa ya mika mata Alkyabbar hannunsa kamar mai rada yace "gashi ki saka am waiting in the down stairs be hurry" da murna ta karba ta shige bedroom din ta ya bita da kallo kafin ya sauka kasa.. Sae da ta kara shafa powder snn ta saka alkyabar ta fito" tun da ta fito yake kallon ta a sace ganin yanda kayan sukayi wani mugun amsar ta
Tana karasowa ya dauke idon sa akanta ya mike yayi gaba tabi bayan sa... Saida suka biya part din Dada tsakanin ta da khadija gaisuwa haka shima tunda ya gaisar da ita ya mike yayo waje batare da yabi takan tayin abincin da take masu ba da kausar da take ta cewa su jirata gaba yy khadija na binsa..
Moto cine masu yawa zasu tafi da su ga fadawa da sojoji su aunty fati duk sun shirya cikin shiga ta alfarma su walid sameera da Rahma.. Cikin mutunci duk suka gaisa suna tambayr ta ya jiki tace Alhmdllh kowa ya nufi motar da zae shiga. Ammar ya bude mata ta shiga.. Ya zagaya aka bude masa zae shiga knn Kausar tace "prince can I go the same with you" "No" yafada a takai ce snn ya shige... Jiki a sanyaye ta nufi wata motar...
Tunda suka shiga motar kallo daya yayiwa Khadija yasan karfin hali take... Har suka isa anguwar su khadija baice da ita kala ba. Haka itama....
Motar su nagama parkawa cikin murna khadija ta fara kokarin bude motar yy saurin riko hannun ta ta juyo tana duban sa ganin ko kallon ta beyi ba yasa tace "kabar ni naje mana" "haka zaki shiga ba tare da an mana iso ba" tura baki tayi to nida gidan mu dan kallon ta yy snn ya dauke kai itama dauke kan tayi tana kallon window kusan minti biyar ta hango su yaya Auwal suna fitowa nan ta cika da murna tana kokarin kwace hannun ta amma yaki saki tace "dan Allah ka barni" "sae kowa ya gama fita snn zamu fita" cewar Ammar.. Khadija ji take kamar ta makesa ta fita.. Suna nan har su aunty fati suka fito kausar sai kallon gidan take dan kallo daya zakayi wa gidan kasan maishi ya yayi nisa a kirasa da Talaka.. Khadija na gani har su aunty fati suka fara shiga gidan amma batayi ji yarima yace kala ba.. Juyowa tayi tana duban sa.. Gani tayi ya lumshe idanun sa kamar mai bacci.. Samun kanta tayi da kallon sa eyelashes din masu yawa kamar mace lips dinsa pink shar ga sajen sa mai laushi ya kwanta a saman kyakkyawar farar fuskar sa da ka gansa kaga balarabe duk da baikai su Rahma haske ma... "Kallon fa" muryar Ammar ta katse ta waro idanu tayi shima ya bude idanun sa ya xuba akanta ta turo baki sai kuma ta marairaice tace "dan Allah na fita" sakin hannun ta yy yana gyada mata kai da murna ta kai hannu zata bude yace "wait" ta juyo tana duban sa shima ita din yake kallo snn yace "kibi a hankali kinga dae kafar ki ba lafiya ne da ita ba ko" gyada masa kai tayi snn ta fice.. Shima aka bude masa ya fita.. Da murnar ta taje ta rungume yaya Auwal "yayana nayi mssn dinka" bayan ta ya fara bugawa yana murmushi hararanta faruk yy "wato ni baki sanni ba ko" hannun sa ta kamo "srry yaya na kasan nayi kewar ka" yaya Auwal yace "lil sis kinga bari naje mu gaisa da mijin ki" juyawa tayi inda Ammar yake tagansa tsaye tare dasu Mujaheed yana wani dan light murmushi dan tsayawa tayi tana kallon sa ganin yanda yy kyau da murmushin dan bata taba gani yy ba... Faruk yamata kas kas da finger dinsa daidae saitin idon ta snn yace "sis dan dagi mana" hararansa tayi snn tace "yaya Auwal ka gansa ko" "srry sis shiga ciki su farida ma da husna duk suna ciki da murna ta nufi entrance din cikin gidan bayi suka rufa mata baya wadan da bama tasan dasu aka xo ba sai ynx... Sukuma su faruk suka wuce domin gaisawa da da walid... A main ta iske su aunty fati an cika masu gaba da kayan motsa baki su sameera sun saki jiki sae fira suke da dasu husna kausar ce kawae tayi shiru sae danna wayar ta take ga hajjo sae nan da nan take dasu su mama dae yake kawae suke Aneesa kam tama kasa fitowa.. Da murna khadija ta rungume farida da husna da ka gansu kasan sunyi kewar junan su.. Aunty fati tace "kide bi a hankali kinsan ba lafiya ce dake ba... Murmushi khadija tayi "aunty ai naji sauki" sae da gaban mama ya fadi jin haka dan a tunanin ta ciki ne da ita.. Farida tace "sis make damun ki" dan ya mutsa fuska khadija tayi snn tace wlh jiyane na fadi shine nayi targade a kafa.. Yar boyayyar ajiyar zuciya mama ta sauke da kausar... Cikin girmamawa khadija ta gaisar dasu mama da umma suka amsa mata suna washe baki amma kasan zuciyar su bakin ciki ne. Dan basu alamar tana shan wahala ba sae ma kyau da haske da ta kara yanda kasan ita ma jinin sarautar ce ganin yanda kayan suka amshe.. Mama tace "wai ina surukin nawa ne naga bn taba ganin sa" kafin ta bada amsa Aneesa ta fito ita da mufeeda itama taxo.. Khadija tace suna can tare da ya Auwal..umma tace "kinga Aneesa zo ku kaimasa kayan motsa baki yaci wani abu kafin Abban naku su iso..." Aneesa tace "to" aunty fati tace "asist her Rahma" Rahma ta tashi suka nufi inda aka jera kayan tarbar nasu suka fara dauka suna fita dashi.. Aneesa na shiga parlour kamshin turaren ammar ya daki hancin ta saeda ta lumshe idanu snn ta bude ta dago ta sauke idanun ta akan Ammar.. Wanda saeda gaban ta yy wata mummunar faduwa tuni jikin ta ya fara rawa da kyar ta samu ta saeta kanta ta aje abincin da taxo dashi ta tabbatar wnn shine yarima Ammar dan shakka babu tunda ta taba ganin kamal da walid... A hankali tace "ina wuni" murya kamar anmasa dole yace "lfy qlw" dan kallon sa Aneesa ta karayi ganin koma kallonta baiyi ba... Gaisar dasu walid tayi snn ta fito gaban ta bugawa da gudu ta ruga daki ta fada saman gado.. Ganin yanda ta wuce su ne yasa a hankalin umma ya tashi tace "bari na danje ban daki" daga haka tabi bayan ta mama tashi tayi tabi bayan ta... Saman gado suka iske ta tana ta kuka da sauri umma ta janyo ta jikin ta "Aneesa lpy" cikin kuka tace "umma nide duk yanda za'ayi ayi don wlh inason Ammar" shiru umma tayi yayinda mama tayi tsaki ta fice... Frida kam tunda taga Aneesa ta shigo ta tabe baki "a ranta tana mmkin bakin ciki irin na yan gidan su...
Abba da big dady ne suka dawo sae yaya sadiq sunyi murnar ganin Ammar kuma sun yaba da hankalin sa dan har kasa ya durkusa yana gaishe su ya kuma kasa hada idanu dasu ko su yaya Auwal ya matukar birgesu gashi dae jinin sarauta amma bashi da girman kau da raini dukda yana da miskilanci dukasu yaran sarkin sun birgesu walid kam ya saki jiki sae labari suke musamman ma da faruk da suke sa'anni...
Kafin kace me gidan ya cika da jama'a su Raliya ma duk sunxo kowa sae kallon khadija yake ganin yanda ta canxa kowanen su bakin ciki fal ransa duk cikin su saleema ce kadae ta kula ta domin kau ta kula tun auren ta da ya sadiq tadan fara sakewa da ita.. Hakan ya danyi wa khadija ciwo gainin yanda yan uwan nata sukayi iskar shegu da ita amma saeta share tunda ga su fat da nan fadila ma tazo... Khadija bata samu ganin Abban nata ba saeda Ammar ya shigo tare da su ya Auwal zae gaisar dasu umma da hajjo... Sannan ta sidade tatafi wajen Abban ta... Da Ammar ya shigo saeda kowa ya bisa da idanu domin kau ya tara duk wani abu da xa'aso a jikin da namiji classic guy ne ga kyau kallo daya zaka masa kasan yana da ilimi kuma hutu da naira sun ratsa sa matshin dai ya hadu 😍.. Kuma da gansa kasan bai fiya son hayaniya ba dan ko a yanayin maganar sama tunda ya gaisar da su bai kara cewa komai ba duk surutun da hajjo ke masa saedae yy murmushi. Walid ne ma da kamal ke dan tayata sae rahma... Su abba ne suma suka shigo khadija na rike da hannun sa kallo daya Ammar ya mata yasan batada lpy dauriya kawae take dan tana cikin farin ciki.. Kallon tsana su Raliya suka bita dashi wanda duk wanda ya kalli fuskar su zai iya lura da hakan.. Su abba sundan jima kafin su fice sbd suna da wani aiki Ammar ma dakin bakin su ka kima yayinda su aunty fati suka fara shirin tafiya kausar kam har ta fita .. ..
Ammar saeda yayi su hajjo dasu mama da Abba shatara ta arziki snn suka fito Lokacin duk sauran ma sun fito su khadija ne karshe sun tsaya sae shiri ta suke ita dasu husna suna tsokanar juna.. Mistakenly farida ta kawo mata duka taxo kaucewa kenan ta turgude kafarta mai ciwo zube wa tayu a wajen tana yarfe hannu alamar zafi.. Duk cikin babu wanda ya kula da hakan sae Ammar da abun ya faru akan idan sa wanda yaji turgudewar da tayi har cikin ransa bai san sanda bakin sa ya furta "HANAN" hakan ya janyo hankalin mutanen dan basu san wata hanan ba da sauri ya nufi gurin ta suma sae lokacin suka lura da khadija... Yana karasawa gurin ta ta rumgumesa tare da fashe wa da kuka dan dama tun danxu ciwo ke cinta "wayyo kafana zafi" furzar da iska yy yana dan buga bayan ta da sauri duk akayo inda suke hankalin su aunty fati duk a tashe su faridama hankalin su duk ya tashi aunty fati taba ta da sauri ta janye hannun ta Tace "Ammar haryanxu jikin ta da zaxxabi" daukar ta ammar yy kamar wata baby a hankali yace "aunty i'll take her to the car idan munje gida kamal sae ya duba ta tunda jirgin ku nan da few minutes zae tashi.. Gyada masa kai tayi shikuma ya nufi mota da ita su ya auwal suka rufa masa baya da sauri dogari ya bude masa ya shigar da ita su ya Auwal suka leka suna mata sannu.. Su Umma kau da yaran su sakin baki sukayi dan basuyi tunanin ko kallo khadija ta ishi Ammar ba daga yanayin da suka gansa... Zuciyar su kamar ta fito dan bakin ciki ganin yanda duk su aunty fati suka shiga tashin hankali sbd wnn yar faduwar da tayi.. Su farida duk can wajen motar sukaje sukayi sallama suna jin dadin yanda kowa ya damu da khadija suna daga masu hannu har motocin suka bar unguwar,.. Kausar ma kamar ta fashe da kuka haka taji sanda taga Ammar ya dauke ta... Khadija kam har suka isa airport bata bar kuka ba Ammar duk ya damu har cikin ransa yanajin kukan nata dan baya son jin kukan mace ... Koda suka isa har su aunty fati suka fito zuwa motar su suna mata sallama har xata fito taji wani jiri da sauri tayo baya Ammar ya kamo ta "are you ok" dan fadawa jikin sa tayi tana sauke numfashi.. Aunty fati tace "kuyi xaman ku ai har an fara kiran mu" gyada mata kai Ammar yy "self journey sis my regards to mummy we're coming in the next two weeks" murmushi tayi snn tace "Allah ya kawo mana ku lpy" daga haka sukayi sallama shima ya daga masu hannu khadija dae na lafe a jikin sa kausar kam cikin fushi ta koma mota ko sallama basu dasu aunty fati ba suka bita da kallo tare da tabw baki...
Suna nan har jirgin su ya tashi snn motocin su suka bar airport din... Taba goshin ta Ammar yy kafin yace "sannu" ta dan gyada masa kai tare da tashi daga jikinsa... Suna isa kausar ta fice ta nufi part din Dada Ammar na kallon ta tacikin mota.. Dan Kallon ta yy snn yace "among the two house wife which one is your mom" saeda gabanta ya fadi da kyar tace "none" dan kallon ta yy ita kuma ta bude ta fita duk da yanda take jin juwa..ganin yanda take tafiya ne kamar zata fadi yasa shima ya fita tare da kama ta suka shiga...
Ajiyar zuciya Dada ta sauke bayan sun shige dan tana kallon su daga windown ta ita da kausar.. Fashewa da kuka kausar tayi "umma dan Allah kiyi wani abu baxan iya rayuwa ba Ammar ba" dariya Dada tayi "kwantar da hankalin ki lokaci yayi dama wann shigiyar yarinyar fatima nake so ta tafi sae su walid dasuke nanuke masa wanda duk abinda zanyi zae iya shafar su ynx kam babu su ko ta hanyar wann bnzar matar tasa nasan yanda zanyi na kawar dashi" da sauri kausar tace "dan Allah umma kar ki kawar dashi ina son sa kide kawar da matar sa" umma tace "ina nufin zan karkato hankalin sa gare ki" dan bata son tayi furucin gaban kausar ba.. A zuciyar ta kam ji take gara yabar duniya dan bata son ta bude idanu taga Ammar a doron duniya....
More comments more typing... ✍️
*#VOTE*
*#SHARE*
*#COMMENTS*✨✨✨
*NAFEESA A GUGA*
😍😍😍😍😍😍😍😍
YOU ARE READING
SABODA DUNIYA
RomanceLabarin yana dauke da abubuwan bn mmki.. Labarine akan wadanda duniya ta rufe masu ido sun manta Allah ne mai komai snn yana dauke da salon soyayya mai bn sha'awa.. Zai fadakar kuma ya nishadantar daku